← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 112

Sashe 94

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

A gidan Baffa aka sauki bakin da suka zo daga Maiduguri, aka bude musu part din Baffa inda Inna ta zauna da, Mama tazo da yammatan ta suka hadu suka shirya musu abinci mai rai da lafiya wanda duk da kasancewar su masu hannu da shuni amma sun tabbatar cewa an karrama su. Sannan Alhaji Babba yazo, Kawu Isa ma yazo sannan abban su Rumaisa shima yazo suka zauna suna ta hira ta wasan fulani da barebari suna ta dariya kamar sun saba. Sai a lokacin ne su Alhaji Babba suka san asalin waye mahaifin Sadauki, jin hakan ba karamin girgiza su yayi ba, ba kuma karamin nadama ya saka musu ba. Lallai rashin sani yafi dare duhu, wanne irin gorin arziki ne basu yi wa Sadauki ba? Wanne irin wulakanci ne basu yi masa ba shida mahaifiyar sa?

Sai da suka nutsa sannan Alhaji Bukar ya gabatar musu da dalilin zuwan su cewa suna nemawa dansu Aliyu Umar Abatcha auren yarsu Halima Usman Kollere, sai Kawu Isa ya gyara masa yace "dan mu dai. Sadauki ai dan mu ne kamar yadda Halima take yar mu. Ku kawai zuwa kuka yi dan ku tunatar damu akan abinda ya kamata muyi tuntuni amma kuma son zuciya da kuma rabo ya hanamu aikatawa sai yanzu da Allah ya sake dawo mana da damar" Alhaji Babba yace "mun bawa Aliyu auren Halima. Duk sanda kuka shirya sai ku dawo a saka rana" Alhaji Babagana ya jawo yar jakar daya shigo da ita ya ajiye a gaban Alhaji Babba yace "a shirye muka zo. Kuma munzo da ranar mu amincewar ku kawai muke nema" sai ya fadi ranar da Sadauki ya gaya masa, yace "lokacin yarinyar tana hutu" babu musu kowa ya amince da hakan, sannan suka sake gaisawa yanzu kuma a matsayin surukai. Sai kuma Alhaji Babba ya roki gafarar su a bisa abinda yayi musu wancan zuwan. Su kuma suka yafe cikin sigar tsokana dan mayar da abin wasa.

Bayan tafiyar bakin ne aka kirawo Inna da Mama da suke cikin gida suka zo akayi musu bayanin abinda ya faru da kuma ranar da aka tsayar. Alhaji Babba ya mikawa Mama jakar da aka bashi yace "ga abinda suka kawo" Mama ta bude sai ta dago kai tana girgiza wa tace "wannan kudin sunyi yawa, albarkar aure ake bukata ai bawai yawan kudi ba" Kawu Isa yace "nima dai naso ince haka, amma sai naga tunda bani suka mikawa ba gwara inyi shiru" Inna tace "ai duk daya ne babu bambanci, suma kuma nasan sun mika masa ne saboda shine Babba" Abban Rumaisa ya kalli Alhaji Babba yaga yadda yayi da fuskar abin tausayi kamar wanda yayi laifi sai yace "tunda an riga an karba ai ina ganin shikenan. Albarka kuma sai muyi ta saka musu ita mu kuma tayi musu addu'a shikenan". Sai Kawu Isa ya tashi yayi musu sallama tare da fatan alkhairi sannan ya tafi.

Ana isar da sako gurin Sadauki ya turawa Diyam message
Chapter 94 · 0% Book details