Sashe 81
Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murjanatu tace "yau dai finally zanga wannan precious Abatcha Motors din da yake rike yayana a Nigeria. Ko da yake ban sani ba ko ba shi kadai bane yake rike shi ba" ta fada tana mintsini na ta baya. Na juya na harare ta shi kuma yana mana dariya muka shiga building din.
Da yake weekend ne duk babu ma'aikata sai security kamar zasu ci mutum. Muna zuwa suka taso kamar zasu durkusa mana ni dai duk sai naji inajin nauyin su. Ya saka su bude ko'ina a gurin sannan yace dasu Murjanatu su zagaya duk inda suke so mu kuma sai ya saka aka kawo mana kujeru gaban wani fountain muka zauna.
Sannan ya dauko waya yayi kira, da alama abinci yayi mana order. Sai kuma yace min "ranar nan, you asked me some questions. Are you ready for the answers?" Na tuno tambayoyin da nayi masa farkon zuwa na office dinsa. Sai nace "eh. Ina son sani please". Yace "okay. Let's start from the beginning".
"Tun farko na san cewa Alhaji Bukar ne ya hada auren Ummah da mahaifina, amma bamu taba maganar dashi ba saboda ganin kamar umman bata so".
"Sunan mahaifina Alhaji Umar Mustapha Abatcha" nayi saurin cewa "Alhaji Umar Mustapha dai wanda muke jin labarin sa?" Ya gyada kai yace "shifa. Family din Mustapha Abatcha family ne da yayi suna ba'a Maiduguri ba kadai har ma da sauran Nigeriya. Suna da kudi tun asalinsu but kudin Umar Mustapha daban ne dana sauran. Tun yana saurayi ya mallaki kudin da shi kansa mahaifinsa a lokacin bashi da su. Harkar man fetur yakeyi yi, tun yana yin gidajen man fetur a gari gari har ta kai shi ga fara siyan rijiyoyin man fetur din gabaki É—aya. Bashi da lokacin aure, dan haka ya jima baiyi ba, wannan yasa yan'uwansa, musamman da yake duk yan uba yake dasu dan shi kadai ne a gurin mahaifiyarsa, suka sako shi a gaba, suna saka ran in ya mutu suci kudi. A lokacin ne Alhaji Bukar, tsohon amininsa da sukayi secondary school tare yayi masa tayin auren bafulatanar yarinya Zainab. Shi kuma sai ya karba yana ganin tunda ba auren soyayya bane ba ba zata ke demanding time dinsa ba. Ta gaya masa labarin wanda take so aka raba su and he was sympathetic, yana nuna mata kulawa sosai ita kuma ta kwantar da hankalin ta sukayi zamansu lafiya a nan family house dinsu dake Maiduguri. A haka har ta samu ciki. A lokacin ne kuna ya fara business da Canada yana exporting crude oil daga Nigeria zuwa Canada wanda har yanzu shine sana'arsa, a yanzu yana daya daga cikin manyan dealers na crude oil a kasar Canada.
Tunda zainabu ta samu ciki shikenan kuma sai al'amurra suka cabe mata, gashi lokacin baya zama a kasar ita kuma taji duk duniya babu inda ta tsana irin gidan aurenta, babu wanda bata son gani kamar mijinta, babu kuma abinda take son rabuwa dashi irin cikin jikinta. Ta zama kamar mahaukaciya, sai ta fita da gudu sai an bita ana kamota ana dawo da ita gida, wani lokacin kuma sai ta zauna tayi ta dukan cikin wai sai ta kashe abinda yake ciki. Alhaji Umar yana zuwa ya ganta a wannan halin yasan asiri ne dan haka ya hada malamai aka zauna addu'a da magungunan karya sihiri akayi tayi mata, in abun ya lafa kwana biyu sai ya dawo. Ta sha wahala sosai. Ranar nan cikin dare suna bacci ta tashi tafita ko dan kwali babu ta kama doguwar katangar gidan da aka zagaye da waya da kwalabe amma a haka ta haura ta var gidan cikin jinin ciwuwwukan da taji, Alhaji Umar yana tashi yaga bata nan ya fito yayi ta nema babu wanda ya ganta sai ya dauki mota ya fita hankali a tashe. Cikin ikon Allah sai ya samo ta tana ta tafiya kamar zautacciya a kamata da kyar ya saka a mota daga nan sai airport. A can ya samu yayi mata adduoin ta dawo hankalinta ya sako ta a jirgi ta taho Kano ya kira Alhaji Bukar ya gaya masa, shi kuma sai ya koma ya nuna cewa bai same ta ba. Akayi ta nema har da cigiya a gidajen radio daga baya aka hakura.
Ita kuma ta dawo gurin yaya ladi ta zauna a kano. Har ta samu lafiya sosai aka tabbatar duk sihirin dake jikinta ya fita. Anan ta haife ni, Alhaji Umar yazo da kansa yayi min huduba da suna Aliyu "saboda ka zama jarumi ya sa na saka maka Aliyu" daga nan sai ya datse igiyar aurensa da zainabu, ya kuma roki Alhaji Bukar cewa ya nemo wannan wanda take so din yayi kokarin hada su aure, bayan an samo Baffa kuma Alhaji Umar da kansa ya bashi amana ta. "Dan Allah ka rike shi tamkar kai ka haife shi. ÆŠa na kowa ne ai, wata kila ma kai zaiyiwa rana bani ba. Ni dai kawai ina son shi da mahaifiyarsa su kasance safe". Through all those years da nake gurin Baffa ashe duk Alhaji Umar yana biye da rayuwata, kuma yace ko da sau daya Baffa bai taba neman wani taimako daga gare shi ba.
To bayan rasuwar Umma da Baffa, bayan na koma gidan Alhaji Bukar, sai yake gaya min cewa ya gaya wa mahaifina zancen rasuwar, amma baya kasar a lokacin yasan da zaizo gaisuwa ma amma yace a gayamin in saka rana da kaina sanda na ke ganin am ready in gaya masa zaizo Nigeria sai mu hadu a Maiduguri. I fixed the date, sai muka tafi. But cikin rashin sa'a sai ya zamanto shi din wani abu yarike shi a can kasar da yake zaune, Canada, dan haka bai samu tahowa da wuri ba. Ban sami kowa a Maiduguri ba sai step grandmother dina a uncles dina. A lokacin ne kuma kika kirani da maganar za'a hada aurenki da Saghir. Nan take naso in yi musu dan karamin hauka a gidan na dage akan lallai sai an taho anzo Kano an nema min auren ki. Duk kallona suke kamar tababbe, irin suna ganin ban isa aure ba ai. Aka kira Papa aka gaya masa yace a rabu dani, wanne irin aure kuma? Sai na karbi wayar na gaya masa ko dai ya ajiye koma me takeyi yazo ya nema min aurenki ko kuma in kama gabana kuma babu wanda zai kuma jin labari na. Sai na gaya masa ko wa cece ke da dangantakar mu. Wannan ne ya ja hankalinsa. Sai ya bani hakuri akan cewa ba zai iya zuwa ba sai dai mu taho tare da Alhaji Babagana, daya daga cikin uncles dina. Muka taho din kuwa and you know what happened a gidan Alhaji Babba. Sanda muka fita I was beyond broken. Sai nace bazan koma Maiduguri ba, a gidan Alhaji Bukar zan zauna. Na zauna gidan Alhaji Bukar trying to find a solution amma na rasa ko daya, babu irin tunanin da banyi ba ciki kuwa har da in shirya mana visa tare zuwa Canada sai in dauke ki mu tafi can mu cigaba da rayuwar mu. But sai na tuno da kalaman Baffa da yake cewa ba yaso ya bani aurenki in dai babu amincewar Inna a ciki, nasan kuma yadda Inna bata sona in na dauke ki zata hada daga ni har ke ne ta tsine mana kuma ba zamu taba ganin dai dai ba a rayuwa. And I didn't want to put you through that. Sai na fara bincike ta karkashin kasa, Alhaji Babagana ya bani kudi sosai kafin ya koma Maiduguri dan haka bani da matsalar kudi, I followed Alhaji Babba, I watched him a lokacin da ya siyar da garejin Baffa, I also watched him lokacin da ya siyar da filina, I watched him lokacin daya siya wa dansa gida na bishi har gidan na gani. But bayan ya tafi sai na tsaya ina studying gidan, bai yi min ba kwata kwata. Unguwar was deserted dan haka babu security kenan, ko menene zai samu mutum a gidan babu wanda zai sani. Na haura na shiga har cikin gidan sai naga locks din kofofin ba masu kyau bane sosai sai naje na siyo wasu na dawo na cire wadancan na saka sababbin da kaina. But still ban gamsu ba dan nasan wannan mijin naki ba lallai yake zama a gida bake kadai zai ke bari so I hired a gate man for you. Malam Iliyasu" na kalle shi da sauri nace "Malam Iliyasu dai maigadin gidan Saghir?" Yace "yes. Tsohon soja ne yana gadi anan kusa da gidan Alhaji Bukar to sai wanda yake yi wa gadin ya rasu. So I took him zuwa unguwar na nuna masa gidan, mukayi sa'a Saghir din yazo sai na nuna masa shi nace yaje ya nuna masa cewa gurin zama yake nema, yana son zaiyi masa gadi free of charge abinda yake so kawai a bashi dakin mai gadi ya zauna anan. And he took the bait. Nace yace masa free ne dan na fahimci babu yaren da Saghir yake ganewa sosai irin na kudi. So, Malam iliyasu yayi muku gadi, ni nake biyansa duk wata, in return shi kuma yana supplying dina with information musamman abinda ya shafi lafiyar ki"
Ban bar kano ba sai da nayi attending daurin aurenku da Saghir. Daga nan airport na wuce straight na tafi Maiduguri ina zuwa kuma na tarar takarduna sun gama haduwa zuwa Canada dan haka kwana na daya a Maiduguri na tafi Ottawa, capital din Canada inda anan ne mahaifina yake zaune da iyalinsa.