← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 112

Sashe 26

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da dare sai ga kwanukan abinci nan daga duk matan gidan kowa ta zubo ta aiko mana dashi, Inna ta karba tayi godiya amma daga ni har ita ba wani cin kirki mukayi ba Asma'u ce ta danci da yawa. A lokacin da muke cin abinci ne naga chance dina na magana da ita dan haka na zayyane mata duk tunani na da plans dina na kara da cewa "inna in mukayi hakan kamar mun dogara da kan mu kenan, ba ruwan mu da abinda za'a bamu da abinda ba za'a bamu ba. Duk wanda ya ke ganin zai taimaka mana saboda zumunci sai yaje har gidan mu ya taimaka mana in ma ba'ayi mana ba bamu da damuwa tunda muna da abin hannun mu. Inna dan Allah ki duba maganar nan".

Tunda na fara ta ajiye spoon dinta tana kallona har na gama sannan ta fara girgiza kai tana kallona tace "yayi daidai Diyam, ya kamata a jinjina wa wannan tsarin naki. Amma bara in tambayeki, sanda kike yin wannan tsarin mune a ranki ni da Asma'u ko kuma bakin yaron can? Iye? Wato bakin cikin ki shine mun taho nan gidan an raba ki da shi shine kike so mu koma saboda ku cigaba daga inda kuka tsaya ko? Kuma ke yanzu a tunanin ki duk duniya in rasa wanda zan dauki ragamar rayuwata ni da yayana in bawa sai wannan yaron? Bani da yan uwane? Ko shi mahaifinku bashi da yan uwan da zasu kular masa da sana'arsa su kuma kular masa da iyalinsa? Ai ina sane na karbi shawarar Alhaji Babba ta cewa mu dawo gidan sa mu zauna saboda in raba ki da wannan yaron. Ina so ki saka a ranki cewa Alhaji Babba yayi mana mutunci yayi mana karamci daya dauko mu ya kawo gidan sa cikin iyalinsa saboda baya son mu zauna mu kadai cikin kunci da kewar mahaifinku dan haka daga ni har ku kamata yayi mu gode masa mu kuma yi iyakacin kokarin mu gurin faranta masa. Maganar gareji kuma shi Alhaji Babba da yake da mutum ne mai budadden ido kuma wanda ya san mutane na tabbatar zai san abinda ya dace ayi dashi. Magana ta karshe Diyam, daga yau sai yau, kar ki sake yi min maganar yaron nan".

Bayan na kwanta na jawo bargo na lulluba sai na tambayi kaina ko a ina Sadauki zai kwana? Ko a wanne hali yake ciki? Sai kawai naji baccin ya dauke daga idona baki daya. Babu abinda ba zan iya bayarwa ba a lokacin dan in samu in san halin da yake ciki.

Kwanan mu biyu gidan Alhaji Babba kuma so far bamu da matsala. Muna samun kulawa da sympathy sosai daga jama'ar gidan amma ni a gurina na gaji da "Allah sarki" da "kuyi hakuri kunji" da kullum akeyi mana wanda babu abinda yake rage min a zuciya ta sai ma kara karyar min da ita da yake yi. Sannan kuma ga tunanin Sadauki daya addabi zuciya ya kullum sai karuwa yaje yi har cikin baccina wanda da kyarnake samu nake yi amma mafarkin Sadauki ne, ko inyi mafarkin rayuwar mu a baya ko kuma inyi mafarkinsa wai shi kadai a titi, har ganinsa nake yi a kwance abskin hanya ruwan sama yana dukansa duk kuwa da cewa nasan yaya ladi ba zata rabu dashi a titi ba, akwai makotan mu da akayi zaman mutunci dasu nasan ba zasu barshi a titi ba, akwai kuma marikin Ummah nasan shima ba zai bar Sadauki a titi ba, wannan sai yasa nayi tunanin to in duk wadannan ba zasu barshi a titiba why Inna? Ita me yasa ta barshi a titin ba tare da ko kayan sawa ba, wacce irin zuciyace da ita? Me yayi mata mai zafi haka?

Bayan mun kwana hudu Mama tazo dan ganin yadda mukayi settling down, ta kuma taho mana da yan abubuwan da take ganin zamu bukata. Bayan sun kebe da inna ne take cewa "ni kuwa Adda ina so muyi magana dake a kan yaron nan dan wajen zainabu. Wallahi ranar nan ba karamin tausayi ya bani ba ke kuwa dan Allah ki sauko da zuciyarki akan sa, ji nakeda zainabu kukayi kishin ku kuma zainabu yanzu kasa ta rufe fuskarta haka zalika shima wanda akayi kishin a kansa, shi kuma yaron ina ruwansa?".

Inna ta kuta tace "ni yanzu wani abu kika ga nayi masa, ko kallon banza banyi masa ba ballantana tsawa ko hantara. Abinda nace shine babu ruwa na dashi yayi gabas inyi yamma tunda wanda ya haÉ—a din ya raba yanzu. Ba shikenan ba." Mama tace "amma at least magana mai dadi ma ai sadaka ce musamman ga maraya, yaron nan bashi da wani gata fa yanzu sai Allah" Inna tace "wai ni Hafsa kin manta da irin wahalar da nasha ne a dalilin uwar yaron nan, kin manta da irin kiyayyar da aka nuna min saboda ba'a aure ta ba? Saboda ita ake so bani ba? Kin manta? Kin manta har sakina akayi a kanta aka kuma dauki yata aka bata. Babu irin kokarin da banyi ba dan in jawo hankalin mijina zuwa gareni amma har ya bar duniya idanunsa ita suke kallo, zuciyarsa baki daya tana gunta duk kuwa da cewa nice uwargidan sa, nice uwar yayansa, ni ce yar uwarsa kuma ni ce wadda ya aura a budurwa ita kuma bazawara. To yanzu sai kiga laifina dan nace bana bukatar duk abinda ya shafe ta? Dan nace bana son ganin abinda zai tuno min da ita?"

Mama tayi ajjiyar zuciya tace "shikenan. Allah ya kara sanyaya miki zuciyarki amma zan sake tuna miki da cewa yaron nan yana da gado a dukiyar da hamma Usuman ya bari, dai dai abinda zaki samu shima haka zai samu shida yaya ladi. Dan Allah Adda a fitar musu da abinsu a basu kinsan shi gado wuta ce, annabi ya fada cewa da mutum yaci gadon maraya gwara ya cika cikinsa da wuta." Inna tace "wannan kuma masu rabon gadon ai sunsan wannan karatun, kuma nasan zasu basu abinsu duk samda aka zo rabawa" Mama tace "yaushe za'a zo rabawar? Ai yanzu ne yake bukatar su, tunda kin ki daukarsa ai kamata yayi a raba gidan a bashi kason uwarsa sai ya fitar da kofa ya zauna a ciki" Inna tace "wai ni Hafsa ki gayamin kina baya na ne ko kina bayan yaron nan ne?" Mama tace "ina bayanki Adda, wannan kuma shi yasa nake gaya miki gaskiya".

A haka mukayi sati biyu a gidan, kallo daya zaka yi min kasan gabaki daya hankali na baya tare dani duk na kara ramewa dama ni ba jiki ba, kullum ina cikin tunanin halin maraicin da muka shiga ciki da kuma tunanin halin da Sadauki yake ciki. Ko wajen gate bani da damar fita saboda kullum ina tare da Inna ko aike na waje ba'ayi saboda akwai yan aiki da masu gadi. Rannan naji Hajiya Yalwati da tazo dakin mu tana cewa "wannan yarinyar kuwa anya ba sai anyi mata rubutu ba? Ita kadai sai inga kamar tana zabura" Inna tace "haka take yi wallahi, ina lura da ita ko baccin kirki bata yi" nan Hajiya Yalwati ta saka ni a gaba da nasiha akan yarda da kaddara mai kyau da marar kyau sannan tace inzo muje dakinta ta bani littafin wasu adduoi da zasu taimaka min. Naje na karba kenan na taho ina hanyar dawowa sai ga Murja da sauri tazo gurina tace "Diyam wai kizo wani yana kiranki a waje" nayi sauri na toshe mata baki muka matsa can gefe na tambayeta waye "to ni ina zan sani, mai gadi ne dai yazo ya a kiranki sai ya ganni ya fada min, wai wannan wanda yake zuwa gurinki sanda kika zo hutu" naji wani adrenaline rush yazo min, nayi kamar zan tafi dakin Inna sai kuma na dawo da baya na zare hijab din jikin Murja na saka nace "Please kar ki gaya wa kowa yanzu zan dawo" sai na wuce da sauri ita kuma ta bini da ido.
Chapter 26 · 0% Book details