← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 112

Sashe 108

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Food for thought: Mun tuna da hadisin da Annabi (SAW) yake mana bayani akan healing power da take cikin habbatus sauda? Sannan da hadisin da yake gaya mana cewa nemon tsami yana maganin cututtukan annoba? Zam zam fa? Mun tuna cewa yana maganin duk wata cuta da aka sha shi da niyyar neman waraka daga gareta? Add that to bin ka'idodin kare ka kai daga wannan cutar, kar ki/ka fita daga gida indai bada wani kwakwkwaran dalili ba, in za'a fita din kuma a saka face mask da hand gloves. A guji taba mutane, doorknobs, railers etc a lokacin da ake waje, kar kuma aci ko a sha wani abu, a kuma guji taba fuska, in an dawo gida kuma a cire kayan da aka fita dasu a shanya su a rana sannan ayi wanka kafin a taba komai na gidan.

Don't forget your morning and afternoon azkar. Insha Allah we will get through this together.
#Don't panic
#Stay safe
#Stay at home

A ranar da yamma su Diyam suka dawo Kano. Tun a jirgi Diyam take ramuwar baccin ta, sai Sadauki ya daga armrest din tsakanin kujerun su ta kwanta ta dora kanta a cinyarsa shi gyara mata hijab dinta ya rufe mata har kafafunta. Sai da zasu sauka sannan ya tashe ta, suna fitowa already daya daga cikin office drivers dinsa yana jiransu ya dauke su ya kaisu gida. A gidan ma Diyam baccin ta ta cigaba, dan sai yau take huce gajiyar biki, Sadauki bai dame ta ba ya batta tayi baccin ta shi kuma yayi musu order ta abinci aka kawo musu har gida saboda ya tabbatar wa kansa cewa bai iya girki ba.

Sati daya bayan tariyar Diyam Asma'u tazo ita da Subay'a, ranar Subay'a kamar zata zuba ruwa a kasa ta sha dan dadi musamman saboda ganin dakin da aka ware a gidan saboda ita. Diyam kuma sai ta dauko gift din data samu a Maiduguri ta ware wadanda take so sannan sauran ta hada da wasu daga cikin kayan lefen ta ta bawa Asma'u tace ta kaiwa Inna a raba wa yan'uwa, cousins dinta duk kowa sai daya samu wani abu. Asma'u kam sai data debi rabonta dama tun kafin a fara tabon. A lokacin ne Diyam ta fahimci cewa Asma'u suna waya da Bassam, she did not comment, idan hakan suke so to ita kam sai dai ta taya su da fatan alkhairi.

Sati biyu bayan bikinsu hutun su Diyam ya kare, ta dauka zasu yi drama da Sadauki akan komawarta amma sai taga shine ma mai taya ta lissafi. Da lokaci ya matso sai taga ya fara hada nasa kayan shima. Tace "aikin fa? In ka bini wa zai kular maka da companyn ka?" Yace "my dear Halima. Kin manta I managed my company for the five years din da nake karatu? Ko kin dauka zan barki tafi ki barni ne?" Tayi dariyar yadda ya fadi maganar kamar wani yaro. Amma kuma tana jin dadi a ranta dan ba karamin faduwar gaba take yi ba a duk lokacin da ta tuna cewa zata koma England school ta bar Sadauki a Nigeria.

Ta zo ta zauna akan cinyarsa ta zagaye wuyansa da hannayenta ta saka fuskarta a wuyansa tana dan bubbaga bayansa tace "kar kayi kuka, bazan tafi in barka ba kaji habibi" ya shafa mararta yace "habibi yana cikin nan gurin a kwance" ta zaro ido tace "ba wani nan" yace "to ni dai banga kinyi period ba" tace "sati biyu ne fa kadai" yace "koma kwana biyu ne, ni ai nasan irin shukar da nayi kuma nake yi so nake inga na fara girbi" ta boye fuskarta a wuyansa tace "kai dan Allah, sai kace wata gona? Ni bani da komai Allah. Kuma ma ai kaga karatu nake yi yanzu ko? Ko so kake in ke faduwa exams dina?" ya dago fuskarta yace "tare zamuyi karatun ai, muna yi kuma muna cigaba da planting seeds din mu, kafin mu gama in Allah ya taimake mu sai mu girbi ko da biyar ne" ta zaro ido "biyar fa kace? Sai kace kaza?" Sukayi dariya tare. Yace "biyar din ma rage miki nayi ai dan kar ki sha wahala da yawa, in za'a bani zabi twins nake so duk shekara. In akayi twin boys sai ayi girls, sai a sake boys a sake girls, kinga a shekara hudu anyi takwas kenan" ta mike da sauri tana cewa "in yaso a shekara ta biyar sai inga an shigo min da amarya ko" ya jawo ta ta fado jikinsa, ya gyara mata zama tana facing dinsa yana tracing jawline dinta da finger dinsa yace "kina so ta mutu ne amaryar saboda bakin ciki? Ko kuma kina so ranar lahira in tashi da shanyayyen barin jiki saboda na kasa adalci? Kina ganin zan iya jera wata dake a zuciyata Halima?" Ta turo baki tace "daÉ—in baki" yace "au baki na yana da dadi dama? Ai ban sani ba nasan dai naki yana da mugun dadi. Let's taste and find out na waye yafi dadi".

Tafiyar su tazo dai dai da hutun su Subay'a. Dan haka Sadauki yace zasu tafi da ita da Asma'u suyi musu hutu a can kuma su taimaka musu gurin settling a sabon gidan su. Murna gurin Asma'u kamar zata tashi sama dan dadi, Diyam tana kallonta tace "kina murnar zaki je England ne ko kuma kina murnar zaki je gurinsa?" Asma'u tayi saurin yi mata signing akan tayi shiru kar Sadauki yaji. Diyam ta daga murya tace "eh, Bassam da kuke waya dashi Asma'u nace kinga kuwa a can yake karatu, nasan zaku ke haduwa in kinje" Sadauki yayi saurin juyowa daga kallon news yana kallon su yace "Bassam, menene hadin Yar asama da Bassam?" Diyam ta nuna ta tace "gata nan, tayi maka bayani". Asma'u ta fara kame kame tana rarraba ido, ya kalle ta strictly yace "bana son shashanci, idan yana sonki da gaske yazo ya same ni first kafin ya cigaba da neman ki. I know his family, amma shi din zan saka a bincika min halayensa in kuma basu yi min ba kin gama ganin sa kenan. Kinji abinda nace?" da sauri Asma'u ta gyada kai.

Ranar dasu Diyam suka sauka a ranar ne suma su Murjanatu suka zo. Sun taho gabaki dayansu tare da sisters dinta dan su taya su Diyam tarewa a sabon gidan su. Gidan da Diyam taga kamar yayi musu girma dan haka ta saka aka rufe part din matar gida suka zuba kayansu a part din maigida ita da Sadauki. Sai bangaren yara kuma anan Murjanatu zata zauna tare da Judith din da Diyam ta kuma gayyatowa. Daga nan kuma sai gurin ma'aikatan gidan wadanda dama suna nan already, masu kula da tsaftar gidan, masu abinci da masu gadi. A cikin kwana biyu aka gama settling komai, a ranar suna zaune gabaki dayansu matan a palo suna hira sai Sa'adatu take basu labarin abinda Papa ya gaya musu kafin su taho daga Canada, cikin kwaikwayon muryarsa tace "ke Sa'adatu dake Falmata, ku fito da miji ayi muku aure hakanan, tunda naga karatun nan naku ba karewa zaiyi ba" duk suka kwashe da dariyar yadda tayi maganar, Diyam ta harare ta tace "yanzu haka baban nawa yake magana?" Falmata ta bude hannu tace "yanzu fi sabilillahi ni ina naga mijin da zan fitar? Ni ina naga saurayin ma? Samari fa basa kula yayan masu kudi" Murjanatu ta gyara zama tace "basa kula ku dai, ku da kuke musu girman kai, ki zo in koya miki yadda ake jawo hankalin maza" anan Sadauki ya bude kofar bedroom ya fito ya tsaya yana kallon su, duk sunyi tsuru tsuru saboda basu san yana cikin daki ba sai Diyam ce kawai ta sani. Bai ce musu komai ba sai ya dauko wayarsa yayi dialing sannan yace "hello Papa" ya gaishe shi yace "maganar nan da ka yiwa su Sa'adatu, ina ganin a hada harda fanna saboda duk tafi su samari. Okay. Insha Allah. Thank you Papa. Love you too" ya juyo yana kallon fanna yace "ke ma ki fito da naki. Gaba daya guri na zasu fara zuwa First, sai nayi approving sannan zasu je gida" bai sake cewa komai ba ya saka hannayensa a aljihu yayi tafiyar sa.

Murjanatu ta zamo daga kan kujera ta fado kasa tana birgima dramatically, tace "wallahi yau na kuma tabbatar wa yaya Aliyu baya so na" su kuma duk suna tayi mata dariya. Diyam tace "alhamdulillah. Zuciyata fess yau. Karyar tara samari ta kare.
Chapter 108 · 0% Book details