Sashe 66
Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
So aim din bawai na koyawa mata yanda zasu gyara aurensu bane ba, aim din na nunawa iyaye da sauran al'umma illar auren dole ne. Allah yasa za'a fahimci manufa ta, ba wai ina nufin rayuwar da Diyam tayi a gidan Saghir itace dai dai ba, a'a, ina nuna akwai possibility na samun irin wannan rayuwar a auren da aka gina shi da tubalin kiyayya.
A kodayaushe rubutu na is open for corrections, criticism and suggestions. Duk abinda ka gani wanda kake ganin ba dai dai bane ba zaka iya tuntubata ka nuna min ko kayi dropping comment yadda zamu hadu mu tattauna har a samu fahimta. Amma kuma, ita fahimta hausawa sunce fuska ce kowa da irin tasa.
Godiya ga wata baiwar Allah data yi min wani gyara a last episode, akan maganar da nayi ta cewa "nothing gives a man the right to hit his wife" what I should have said a gurin shine "nothing gives a man the right to hit his wife the way Saghir did" saboda munsan cewa an bawa maza damar horon disobedient wife da bakin sutturar su, shima kuma sai akace kar su taba fuska. Nagode baiwar Allah duk da bansan sunan ki ba. Lol
Kar in cika ku da surutu, ga Diyam...........
Na tsaya a gurin tamkar wadda aka dasa ni, ina kallon bayan motarsa, ina nan tsaye su Alhaji Babba suka fito suka shiga motar Kawu Isa suka tafi ba tare da sun ko kalli inda nake tsaye ina kukan rabani da yata ba. Asma'u ta fito da tazo ta kamani "Adda kiyi hakuri kizomu koma gida, ki rabu dashi yayi ta tafiya da ita din, Allah zai baki wadansu kuma ita din ma da kafafuwanta zata dawo gurinki" ta kama ni muka shiga ciki. Muka tarar da Inna ta zabga ragumi idonta yayi ja, Asma'u tace "dan Allah Inna kar ki wani tayar da hankalin ki, ance musu in babu su ba zamu iya rayuwa ba ne ba? Ai mu kwallon mangwaro muka yar muka huta da kuda wallahi. Da auren Saghir ba gwara babu ba?" Inna tace "hmmm. Asma'u ke yarinya ce. Ba zaki gane ba".
Ni dai sai na wuce su na shiga daki na zauna a bakin gado. All I have ever wanted tun da aka daura aurena da Saghir shine inji sanda zai furta da bakinsa yace ya sake ni. To gashi na samu amma kuma yanayin da sakin yazo min sai yasa naji sam banji dadinsa yadda nayi tunanin zanji ba. Hakan kuma yana da dangantaka da abubuwa da dama. Na farko zargin da Saghir ya sake ni saboda shi, wanda kuma ba gaskiya bane ba, na biyu zumunci daya karasa lalacewa tsakanin mu da yan uwanmu, na uku Subay'a I can't even imagine yadda rayuwar Subay'a zata zamo a gidan Saghir ba tare dani ba. In banda mutuwa menene yake raba uwa da yar karamar yarta? Amma ni gani a raye amma an raba ni da tawa yar. And I asked myself then, shin Saghir yana da wannan damar?
Ranar haka na karasa wuni raina babu dadi. Da nazo sallah kuwa ina dora goshina a kasa sai kuka, zuciyata ta cunkushe gabaki daya, na idar na daga hannuna da niyyar yin addu'a amma sai na rasa me zan roka kuma. Sai kawai na roki Allah daya dubi zuciyata tunda ya fini ni kaina sanin abinda yake cikin ta, na roke shi ya daidaita min lamurana zuwa ga abinda yake shine dai-dai bawai abinda ita zuciyar tawa take so ba, ya saka rabuwar nan da mukayi da Saghir ta zamanto mafi alkhairi a gare mu baki daya, sannan ya bayyana gaskiya ya goge zargi ya kawo daidaito tsakanin mu da yan uwan mu. Na kuma roke shi daya kasance tare da Subay'a a duk inda take.
My life had been full of challenges so far, na fuskanci kaddarori iri iri wadansu naji dadin yadda na dauke su wasu kuma I have made a total mess of them. Amma a cikin regrets dina babu rabuwa da Saghir, na daiyi regretting irin zaman da mukayi amma banyi regretting kuma bana jin zanyi regretting zama na dashi. For more than eight years muna tare dashi amma dai dai da rana daya ban taba jin zuciyata tana sonshi ba, ko da kuwa a cikin ranakun da yake kyautata min ne sai dai inni kiyayyar sa ta dan kwanta min amma ba dai ta tafi ba ballantana sonsa ya shiga. Nayi addu'ar kuma kullum, kullum nayi sallah sai nayi addu'ar idan zamana da Saghir ne mafi alkhairi Allah ya rage min kiyayyar sa a zuciya ta. Dan haka da akayi rabuwar sai nayi taking that as shine zabin Allah kuma ma roke shi ya cigaba da zaba mini.
Na fara zaman iddah a nan gaban inna, ba inda nake zuwa sai kewayen maman iman sometimes inyi kallo musamman in Asma'u ta tafi makaranta, sometimes kuma in zauna anan dakin Inna inyi ta karatu wanda shine yake kara nitsar min da zuciyata ina jina ina zama at ease. Inna ta gayawa Mama abinda ya faru, kuma tazo har gida ta ganni ta kuma yi min nasihohi sosai akan karbar kaddara da kuma shirin facing rayuwar da zata zo min. Tace "in kin gama iddah Diyam makaranta zaki koma. Kar ma kiyi tunanin aure gwara kiyi karatu ki huta kema jini ya dawo jikinki sosai. Sannan ki samu exposure. Kuma ki koma islamiyya ki karasa saukar ki dama kin kusa ko?" Na daga mata kai, tace "sai ki karasa kuma ki fara hadda, ki cigaba da bin sauran littattafan addini suma kina kara buda kwakwalwar ki" nace "insha Allah Mama". Washegari sai ga Rumaisa amarya tazo gurina. Muka wuni tare muna ta hirarrakin mu sai naji hankalina ya kwanta sosai.
Monday Sadauki yazo kamar yadda ya saba zuwa. Last Monday bai zoba ya kira Inna yace wani issue ne ya rike shi a Maiduguri amma tayi hakuri. Wannan Monday din kuwa tun safe naga tana ta haÉ—a masa kunun aya wai taga yana so, ta dama masa fura itama ta saka a fridge ni dai ina ta kallonta. Yamma tana yi, dama nasan da yamma yake zuwa sai na saka hijab dina na tafi gurin Maman iman muka kafa hirar mu. Bana son ganinsa yanzu kuma nasan kona zauna a cikin daki in yazo sai Inna tace in fito in gaishe shi. Amma muna zaune kawai sai ga baban iman da baki sunzo, dan haka dole nayi musu sallama na fita na koma gurin Inna. Ina shiga naga takalmin namiji a kofar palo, sai na jawo farar kujera na zauna a tsakar gida amma ina zama inna ta kira ni, na bata rai kamar zanyi kuka na tashi na shiga. Yana zaune a kasa, Asma'u kusa dashi da wata takarda a hannun ta tana nuna masa wani abu suna magana a nutse. Ga kunun ayansa nan a cup a hannunsa yana sha. Na zauna a gaban Inna nace "sannu da zuwa" ya dago ya min kallo daya ya mayar da kansa yace "sannu maman Subay'a" sai ya cigaba da yiwa Asma'u bayanin wanda na fahimci kamar takardar jamb ce take kokarin cikewa. Na mike na shiga daki nayi kwanciya ta. Sai naji Inna tace masa "Diyam fa sun rabu da Saghir" naji yace "rabuwa Inna" cikin mamaki, Inna tace "rabuwa fa, ya sake ta" yayi dan shiru sannan yace "ya Salam. Subhanallah. Abu baiyi kyau ba. Allah yasa hakan shi ya fi musu alkhairi" Inna tace "ameen" Asma'u tace "ai rabuwar ma itace alkhairi hamma, wannan auren na Adda ai dashi gwara babu" Inna tace "rufe min baki sarkin magana. Waye ya tambaye ki? Tashi ki fita" ta tashi ta fita. Sadauki yace "na dauka ai ko ganin ku tazo yi" Inna tace "uhm uhm, ai satinta biyu kenan anan. Tun sanda nayi maka wayar nan ai bata koma ba dama. Nan yazo har gabana ya sake ta yasa hannu ya dauki yarsa" yace "Subay'a? Ita ta bashi ita ko kuma shine kawai ya dauke ta?" Inna tace "ina kuwa zata bashi ita? Gata nan tunda ya dauki yarinyar nan kullum sai na ganta tana kuka kuma nasan kukan yarta take yi amma ya zanyi?" Yace "a'a in dai ba ita ta bashi ita ba to zata iya karbar yarta. Ai both islamically da constitutionally bashi da right din daukar yarinyar" Inna tace "to ta yaya za'a karbo ta kenan?" Yace "ba wahala ai. Ko hisba akaje akayi reporting zasu karbo yarinyar a hannunsa su kawo mata" Inna ta jinjina kai tace "mutanen nan sunyi mana ba dai dai ba daga ni har yaran nan, amma yanuwan mune. Bana son cigaba da rigima dasu so nakeyi a samu fahimta a tsakanin mu. Amma zabin Diyam ne" sai ta saka baki ta kira ni. Na gyara hijab dina na fita, sai na ganshi a zaune yana daddanna waya kamar ba shine yanzu suke magana rai rai da Inna ba, na zauna a gabanta nace gani, tace "Sadauki yace za'a iya karbar Subay'a a hannun Saghir in aka gayawa hisba. Kina so a karbo miki ita?" Na juya na kalle shi busy with his phone, at least a matsayin da yake dashi na yayana da muka tashi tare kuma Inna ta bashi wannan labarin ai ya kamata ko magana mai dadi ce yayi min, sai na dauke kaina nace "ina son karbar Subay'a Inna, kuma zan karbo ta insha Allah amma bana bukatar taimakon sa. I can do it on my own" sai naga yayi sauri ya dago kai yana kallona. Yace "how?" Nace "ba kace hisba ba? Ai nasan hanyar hisba din kuma ina da bakin da zanyi musu bayani in naje" Na daga kafada na mike na komawa ta daki.