← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 112

Sashe 46

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga ranar ban kuma lafiya ba, yau zazzaɓi gobe amai jibi ciwon ciki. Saghir kam fushi yake yi dani sosai ni kuwa ta kaina nakeyi, bai ma kula cewa bani da lafiya ba ballantana yayi tunanin kaini asibiti. Bayan nayi kusan sati ina jinya rannan uwani tace min "Diyam anya kuwa ba zaki yiwa Saghir magana ya kaiki asibiti a gwada ki ba? Ni fa ina ganin kamar juna biyu ne dake" sai naji wani amai ya taso min, naje nayi na gama na dawo nace "ciki fa uwani? Wanne irin ciki kuma?" Tace "ni dai na fada miki, kuma kije a gwada ki gani" sai na hau sama da sauri ina jin kamar labarin mutuwa ta uwani ta fada min, na fada kan gado na kama kuka, na shiga uku ni Diyam, sai na fara addu'a "Allah ka dube ni Allah, Allah kasa kar maganar uwani ta zama gaskiya" amma kuma nasan rabo na da period tun ina gidan mu, ga kuma abinda ya faru ranar dana dawo.

Ina nan kwance Saghir ya hawo yana kwalla min kira, na tashi na same shi a tsaye a kofar dakinsa yace "ki shiga ki gyara min dakina" na wuce shi na shiga na fara harhada uban lodin kayansa duk daya barbaza a dakin, ga zazzaɓi gashi jikina babu kwari saboda amai. Shi kuma ya tsaya a kofar dakin ya harde hannayensa yana kallona. Na daga wata riga kenan naji kamshin turarensa ya doke ni sai amai, da kyar na karasa toilet na fara karara wa sai ya biyo ni ya tsaya a bakin toilet din yana kallona har na gama sannan yace "baki da lafiya?" Bance masa komai ba yace "me yake damunki?" Nace "zazzaɓi" yace "da amai?" Na girgiza kaina da sauri nace "warin turarenka ne ya saka ni aman" yace "amma ai kullum shi naje sakawa baki taba aman ba sai yanzu. Are you pregnant?" Nayi shiru bance masa komai ba sai yayi tsaki "ke bansan wacce irin mace ba ce ke, daga an taba ki kadan sai ciki" naji wani abu ya tsaya min a kirji na wuce shi na dawo daki ina cewa "tunda dai bani na hau kan kaina nayi wa kaina cikin ba ai da sauki. If you hate me that much ka sallameni mana in tafi" ya biyo ni yana cewa "and who says I hate you?" Na tsaya ina masa kallon kar ka raina min hankali, sai yace "idan da bana sonki Diyam da tuni kina gidan ku wallahi ko dan wannan rashin kunyar taki. Kuma yanzu ko dan wannan samun cikin da ake yi ai ya kamata ki fahimci cewa we are meant to be together. Ki kwantar da hankalin ki muyi rayuwar aure kinki, kin ki cire that Sadauki of a person daga zuriyar ki kuma... " Ban karasa jin abinda zai fada ba na fito daga dakin na koma nawa.

Washegari shi ya tashe ni da safe wai in shirya muje asibiti, muna zuwa ya samu doctorn dana lura kamar sun san juna yace "PT zaka mata Please" sai doctorn yayi dariya ya kira wata nurse ya hadamu muka je tayi min. And it came back positive. A ranar nayi kuka kamar idona zai fita.

Tunda muka koma gida ya tare a dakina yana jinya ta, shine bani magani shine yi min sannu da su hada min tea, ni duk na dauka jinyar Allah da annabi ce sai daya sauke bukatunsa a kaina sannan na fahimci inda jinyar ta dosa.

Kayan lefe dai mun cinye su, babu biya babu ranar biya. Sai kuma yazo ya dauki set din kayan kallo na palon sama ya siyar, daga nan sai set din gadon extra dakin da bama amfani dashi a sama, sai deep freezer. Duk abinda aka siyar daga an dan siyo kayan abinci an dan bani kudin cefane bana kuma sanin inda sauran kudin sukayi. A haka har cikina ya tasa yayi wata biyar.

Ranar nan na shiga kitchen na rasa me zan dafa mana na hawo sama na same shi akwance a gado yana daddanna waya. Nace "babu fa abinda za'a ci a gidan nan" sai ya saka hannu a aljihu ya zaro min yadin aljihun na karkade min ya cigaba da danna wayarsa. Sai na samu kaina da tambayar kaina menene role din Saghir a auren mu? Shi aikinsa kawai shine yayi min ciki? Na shigo ciki na zauna a kan bedside nace "Saghir idan ni da kai da uwani mun zauna da yunwa wannan" na nuna cikina, "bai san babu ba" ya kalli cikin nawa sai ya ajiye wayar yace "to wai me kike so inyi? Ni fa ko kudin man da zan zuba a mota in fita bani dashi, ko so kike a ganni a daidaita sahu ake nuna ni a gari? Ko kuma so kike in ke bin gidajen masu kudi ina cewa allazi wahidi? Ko kuma dako kike so in dauka ko lebura ko kuma aikin mechanic? Na fahimci abinda yasa ya fadi mechanic din, so yaje muyi fada inyi zuciya in rabu dashi amma sai nace "eh, so nake kayi duk abinda ka fada indai zaka samu halak dinka. Wai kai ba kayi karatu bane ba? Ina takardun ka, ka karkade su ka fita kane gurin abokan Alhaji su hada ka da connections din da zama samu aiki. At least if you can't be a good husband try to be a good father".

Bansan ya akayi ba kuma ina daki sai gashi da folder din takardu yace zai je gida ya kaiwa Alhaji, sai kuma yace "in na samo kudi a hannun Hajiya sai in taho mana da wani abun a hanya". Ni dai na rabu dashi a raina ina cewa lallai gata mugun abu. Na tuno Sadauki da rashin zamansa a guri daya, tun yana dan karamin sa Baffa ya nuna masa neman kudi. Sai nayi murmushi ina lissafin irin kudin da Sadauki zai tara in dai ya samu hanya.

Ban kuma tabbatar wa cewa Alhaji Babba ya fada kwata ba sai da muka je gidan few days after that. Mota daya ce a compound din, ita ma kuma daga ganin ta nasan an dade ba'a hau ta ba, komai babu, ni sai naga gidan kamar har wani duhu yayi. Shi kansa ya rame, kayan jikinsa sun tsufa, na gaishe shi ya amsa yana ta yake baki. Muka shiga cikin gida suna ta kallon cikina, Hajiya Babba har da yar min da magana wai da Inna ta hanani komawa bayan ni ina son mijina, ni dai bance mata komai ba. Itama naga dakinta yar aiki daya ce kawai kuma itama na tabbatar yan uwanta ne suka dauko mata. Hajiya Yalwati kam Allah ya taimake ta Æ´aÆ´anta manya su uku sunyi nce sun fara teaching dan haka su suke daukan nauyinta da kannen su. Da zamu tafi su murja suka ce zasu bi mu amma Saghir ya rufe idonsa yace babu wadda zai dauka. Sai da muka dauki hanya ne yake cewa wai nauyi zasu dora masa in suka zo. Sai na tambayi kaina 'ba shine namiji ba, babban wa uba? Bashi ya kamata ya dauki nauyin kannensa ba amma shine mai gudun ciyar dasu na kwana biyu?"

Bayan munje gida yake gaya min "Alhaji ya hada ni da wani abokin sa shi kuma ya hada ni da wani mutum daya bude kamfanin siyar da motoci kwanan nan. Gobe zanje interview kiyi mana addu'a. Idan aikin nan ya fada ko? Hmmmm, ba karamin kudi suke dashi ba a gurin nan kuma kinsan accounting na karanta harkar kudin" ni dai nayi addu'a amma bansa ka rai ba saboda bansa ran zai samu aiki irin haka da wuri ba.

And to me surprise, sai gashi washegari da offer. "I nailed it. Diyam, I got it. Wato managern ne da kansa ya ganni, karamin yaro ne mai babbar harka. Kawai few personal questions yayi min shikenan yace 'you are hired' just like that fa, Diyam you are talking to the financial secretary of Abatcha Motors"
[2/8, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Thirty Eight : Subay'a

Na rike baki ina dariya, ko ba dan Saghir ba ko dan ni kaina da abinda yake cikina nayi murnar wannan aikin. Nace "Masha Allah. Alhamdulillah. Amma fa kayi sa'a, abinda mutane sai su dade suna neman aiki basu samu ba amma kai kaga lokaci daya ka samu" yayi dariya yana zama akan kujera yace "maybe mutanen da kike magana akan su basu san inda ya kamata su nemi aikin ba ko kuma basu dace da aikin ba. Kinsan appearance matters alot a gurin neman aiki, yanzu misali ni, kowa ya ganni yasan na chanchanta da post din dana samu" na zauna ina mamakin bragging irin na Saghir, nace "komai fa a rayuwa yana da lokaci, wadanda basu samu aiki ba lokacin samun su ne baiyi ba, kai kuma daka samu lokacin kane yayi, ita rayuwa....." Ya daga min hannu "don't spoil my mood please. Je ki kawo min ruwa" nayi ajjiyar zuciya na tashi.

Ranar daya fara zuwa office ne bayan ya dawo na tambaye shi "to an baka office? Da fatan sun fara baka aiki kanayi" yace "wanne irin aiki kuma?" Nace "rubuce rubuce mana, ba shine aikin secretaries ba?" Yayi tsaki yace "fin sec fa aka ce miki, ni harkar shiga da fitar kudi a companyn ne kawai part dina, besides, ina da mataimaki so shi zaike handling duk aiyuka" nace "so? Kai menene naka aikin?" Yace "who cares about aiki ne wai, what I care about is the salary kuma zasu ke bani mai kyau shikenan".

Tunda aiki ya samu kuma shikenan Saghir ya koma tsohuwar rayuwar sa, inya fita tun sassafe baya dawowa gida wani lokacin ma har sai nayi bacci. Baya zuwa gida a bige, amma hakan bawai yana nufin ya daina bane ba dan sau da yawa in ina gyaran kayansa nakan ji wannan warin a jiki, sai dai bani da wani kwakwkwaran hujja. Yana ciyar damu, duk da dai considering yadda yake kashewa jikinsa kudi baya yi mana yadda ya kamata amma dai muna cin abinci. Shi kuwa kullum cikin sababbin dinkuna yake yakance "gwara mutum yayi dressing sosai kar a raina masa hankali".
Chapter 46 · 0% Book details