Sashe 78
Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dan rashin ta ido sai ganin kiran sa nayi a waya ta. Na kalli wayar a raina nace "lallai ma Sadaukin nan" ina kallon wayar wannan kiran ya shigo ya katse wani ma ya shigo har ya gaji ya daina. Sai na dauki wayar ina kallon number din. Finally dai anyi unblocking dina kenan. Ya kamata dai inyi saving number din nan, amma wanne suna zan saka masa? Sadauki? Ko hamma kamar yadda naga Asma'u ta saka?
Sai kawai na bude keyboard dina nayi typing "Aliyu" nayi saving. Asma'u ta budo kofa ta shigo tun kafin tayi magana nasan me zata ce "ki zo inji Inna" na dauki hijab dina na saka na fita. Yana zaune can carpet a gefen kujerar da Inna take zaune, an cika masa gabansa da kayan ciye ciye, yayi kwalliyarsa cikin normal kananan kayansa. Nayi saurin dauke kaina daga kansa saboda zuciyata da naji tana kokarin barin kirjina. Na zagaya naje na zauna can nesa dasu nace "Inna gani" tace "baki ji Sadauki yazo ba? Ai dai kya fito ki gaishe shi ko?" Na kalleshi muka hada ido, har da wani langwabar da kai kamar wani abin tausayi. Na dauke kaina nace "sannu da zuwa" yace "yauwa. Ya gida ya makarantar?" Asma'u ta fara bashi labarin school dinsu, yana ta tsokanar ta wai jambite ni dai sai na mike zan bar musu gurin sai yayi sauri ya tashi yace "Inna zan wuce, Allah ya bamu alkhairi" tace "ameen, Allah yayi albarka" sai da ya je bakin kofa sai ya juyo yana shafa kai "ammm, Diyam. Akwai sakon Subay'a a mota ko zaki zo ki karba" nace "Asma'u, bi shi ki karbo mata" sai ta mike tayi hanyar daki tana waka "you know I love it when you call me senorita" ta shige daki ta rufo kofa. Na cigaba da zama na shi kuma yana tsaye a bakin kofa yana kallona sai kawai gani nayi Inna da dauko mafici tayo kaina dashi sai na tashi da sauri na fita.
A garage na same shi a tsaye yana dariya. Na hade rai nace "ina sakon?" Yace "yanzu ke baiwar Allah sai Inna ta biyo ki da mafici sannan zaki zo gurina?" Nace "akwai sakon da zan karba ko babu?" Ya jingina a bango ya rungume hannayensa yace "babu, just want to see you, that's all" nayi shiru, trying so hard not to look at him, yace "ba kya son gani na yanzu ko?"
[3/7, 9:06 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: â¤ï¸ DIYAM â¤ï¸
By
Maman Maama
Episode Fifty Eight : Murjanatu
Na dauke kaina gefe nace "tunda babu sakon da zaka bani, Allah ya bamu alkhairi" na juya zan tafi sai ya zagayo ta gabana ya tsaya yace "look into my eyes and tell me ba kya son ganina and I promise you I will leave you alone" na daga ido na kalle shi amma muna hada ido sai nayi saurin sunkuyar da nawa idon kasa saboda wani zazzafan sako daya iso gare ni daga cikin idanunsa, sai na jawo fuskar hijab dina na rufe fuskata dashi, amma ina ganin duhunsa, sai naga ya sunkuyo dai dai fuskata yace murya can kasa "open your eyes and look into my eyes kice 'sadauki bana son in sake ganin ka" sai na juya fuskata daya side din nace "ka bani hanya in wuce, ko ka manta na baro Æ´ata a daki ita kadai? And she needs me saboda babanta bayanan yana prison" sai ya gyara tsayuwar sa yace "hmmm. Gori zaki yi min kenan ko? Wai 'Æ´ata'" ya fada yana kwaikwayon magana ta. Bance komai ba sai kuma yace "Subay'a will be fine, nayi miki wannan alkawarin. Na san ba zan taba replacing mahaifinta ba, amma zanyi duk iya kacin kokari na inga na bata duk abinda ya kamata uba ya bawa yarsa. Kar ki manta ina da training din rikon É—an wani. Ban tashi da ubana ba duk kuwa da cewa yana raye, and still I have gotten the best fatherly care and love"
Na fahimci zancen Baffa yake, sai na bude fuskata ina kallonsa nace "hakane, amma banbancin ka da Subay'a shine shi Baffa bai rufe mahaifinka a prison ba sannan bai yi gidan gona a cikin gidan grandfather dinka ba. No child will ever forget that". Ba tare dana kalleshi ba na wuce shi na koma ciki.
Ina shiga na wuce Inna a palo na shiga daki ina jin zuciyata tana yi min zafi, haushin Sadauki nake ji kuma haushin kaina nake ji. Ji nake kamar wani dan karamin yaki akeyi tsakanin zuciyata da ƙwaƙwalwa ta ko wanne yana gaya min abinda zanyi. Sai na sake jawo jakata na kuma hada kayana kamar rannan na fita na samu Inna a dakinta tana sallah sai na zauna na jira ta sai data idar sannan ta juyo tana kallona, daga yanayin zaman da nayi tasan magana ce a bakina dan haka tace "ya akayi?" Nace "Inna, alfarma nake nema a gurin ki. Dan Allah Inna ina so ki fita daga maganar Sadauki" ta kalle ni da mamaki tace "ban gane ba? In fita daga maganar sa kamar yaya? Wacce maganar kenan?" Sai nayi shiru na kasa bata amsa sai tace "ba kya sonsa ne yanzu kuma?" Na girgiza kaina nace "kawai dai Inna ina son ajiye maganar sa a gefe sai zuwa lokacin da muka sake fahimtar juna tukunna. Kinga shekaru da yawa, abubuwa da yawa sun chanja. Ba lallai ne halayyar sa ta da ita ce a yanzu ba. Ni so nake ki bar mu ni da shi kiyi ta mana addu'a in Allah yasa muka fahimci juna sai mu sanar muku ku saka mana albarka" a juya kanta gefe tace "fushi kike dashi akan maganar Saghir ko?" Nayi shiru, sai ta cigaba "ruwansa ne in yaga dama ya yafe masa, ruwansa ne kuma in bai ga dama ba kuma yaki. Ni ba wai ina matsa miki ki kula shi ko ki aure shiba, ina kokarin gyara abinda na bata ne a baya, ina kokarin bashi abinda na hana shine a baya tare da fatan ko hakan zai rage min laifuffuka na a gurinsa da kuma a gurin ubangiji. Dan haka ni dai shi nake so ki aura, amma zabi yana gurinki in kince a'a bazan ji dadi ba amma ba zan matsa miki ba".
Nace "Nagode Inna" sai kuma na gabatar mata da bukata ta tason zuwa gidan Mama. "Kwana biyu" ta ce min, naso ta barni inyi sati ko ma sati biyu amma taki, haka na hakura na dauki kaya set biyu da safe na tafi tunda ina son zuwan saboda ina so muyi shawara.
Ina zuwa na tarar Rumaisa tazo, na saka ta a gaba da tsokana mai ciki mai ciki ita kuma tana ta jin kunyar Mama, sai da muka kebe tace "wai dama haka ake ji in ana da ciki?" Hmmm kawai nace mata a raina ina cewa wannan kukan dadi take yi, na tuna cikin twins ina 14 years, babu abinda na sani, ga babu miji babu iyaye. Na tuna cikin Subay'a yadda na sha wahalar laulayi, da gorin da Saghir yayi min wai daga an taba ni sai ciki.
Sai da muka samu zama sannan na bawa Mama labarin cewa Sadauki fa ya dawo, bai dai furta direct ba amma ya nuna. Ta daga kafada tace "so? Ji nake murna zakiyi kuma naga kin bata rai" sai na gaya mata kuduri na akansa.
"Ba wai bana son aurensa bane ba Mama, so nake ya kunce kullin da yayi da kansa, saboda jin dadin kansa kuma Subay'a" tace "so kike ya yafewa Saghir kudin da yake binsa?" Na girgiza kai nace "ba wannan kadai ba, so nake ya taimaka masa yayi solving drug case dinsa. Sadauki yana da power, zai iya jan wasu strings ayi closing case din Saghir na drugs, ko kuma ayi tracking Kabir a kama shi asaka shi ya amsa laifinsa. Bayan ya fito dashi kuma ina so ya bashi aikin yi, saboda nasan with that reputation babu ma'aikatar da zasu dauki Saghir aiki ballantana ya samu abinda zai rike yayansa". Mama tace "anya kuwa Diyam wadannan sharadan naki basuyi tsauri ba? Wane ne zai je neman auren mace kuma tace masa sai ya fito da tsohon mijinta daga prison kuma ya bashi aiki? Anya kuwa kina ganin zai amsa?" Na girgiza kaina nace "ban sani ba Mama, shine kuma shawarar da nake so ki bani yadda zan saka Sadauki ya karbi wannan maganar. Ni dai abinda na sani shine zuciyar Sadauki tayi tauri da yawa, ya kasa yafewa wadanda yake ganin sun cutar dani da shi. Kuma nasan gurin Sadauki Saghir yafi kowa baƙi, shi yasa nake so ya yafe masa kuma ya taimaka masa. Nasan in dai har ya iya yafewa Saghir to babu wanda ba zai yafewa ba, in dai har ya taimaka wa Saghir to babu wanda ba zai taimaka wa ba".
Mama tayi shiru tana kallona sannan tace "zuciyarsa tana da tauri tabbas, ke ai kinsan haka tun kuna yara haka yake kuma sai rayuwa ta kara taurara shi. To ni a shawara ta ba juya masa baya zaki yi ba jawo shi kijinki zakiyi. Ki nuna masa irin son da kike masa ki bashi dama ya nuna miki nasa, to shi kansa ba zai san sanda zuciyar tasa zata rissina ba, abinda zaiyi ke kanki sai ya baki mamaki".
Kwana na biyu gidan Mama na shirya zan koma gida Inna ta kirani. "Sadauki yazo dazu, na gaya masa kina nan gidan yau zaki dawo sai yace zai zo ya dauko ki" nace "to" a raina ina jin haushin mai yasa ba zai kira ni ya gaya min ba.