Sashe 52
Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ranar Thursday na kira Inna na roke ta ta turo min Asma'u tayi min weekend dan ta dan taya ni wasu abubuwan, na gaya mata bani da lafiya ne. Friday sai gasu sunzo har da Inna, wannan shine zuwan inna gidana na uku tunda nayi aure kuma duk duba ni take zuwa yi in bani da lafiya. A kasa muka zauna dan bata taba hawa sama in tazo, tana tayi min mitar yadda duk nabi na kara ramewa tana cewa me yasa banje asibiti ba? Ni kuma sai nayi shiru kawai dan ina ganin fada mata cewa Saghir ba zai kaini ba bashi da amfani tunda nasan ko tayi masa magana ba zai ji ba sai dai kawai ranta ya baci. Sai kuma nayi tunanin ko ingaya mata zancen Sadauki? Sai dai bani da tabbas din yanzu menene ra'ayinta akan Sadaukin bansan yadda zata dauki kasancewar sa a matsayin ogan Saghir ba. Na dai san tana nemansa akan gadon Ummah na gida dan haka dole zan gaya mata amma ba yanzu ba, sai na samu damar magana dashi tukunna first.
Asma'u ce ta tashi ta gyara min gidana tsaf, har dasu turaren wuta, sannan ta shiga kitchen tayi mana girki muka hadu muka ci tare harda Subay'a. Sai naji dadi sosai, maybe ciwon nawa harda rashin wanda zanyi wa magana da kuma yunwa. Ana yin la'asar Inna tayi sallah sai ta tashi ta fara shirin tafiya. Na fara mita "Inna daga yin la'asar? Ki bari mana sai kamar karfe biyar haka sai ki tafi" tace "uhm uhm, wannan gari na damina yanzu sai kiji ruwa ya sauko. Bana son mijinki yazo ya same ni a gidan nan" muka yi tayi mata dariya ni da Asma'u dan mu a gurin mu kamar babu komai dan sun hadu, ita kuma al kunya ce irin ta fulani.
Ai kuwa kamar ta fada da bakin mala'iku sai ga ruwan sama ya sauko, da yake muma daki babu wanda yasan ma da hadarin sai kawai zubar ruwa mukaji. Inna ta fara salati mu kuma muna dariya "yau kwana ya kama Inna a gidan Adda" inji Asma'u, Inna tace "kwana bai kama ni ba, ai komai dare ruwan nan in ya dauke sai na tafi gida, balle ma ba lallai ne ya kai daren ba". Wasa wasa ruwa har magrib, har isha yin sa ake kamar da bakin kwarya, Inna ta shiga dakin kasa inda Asma'u ta gyara dan anan take zama duk sanda tazo gidan saboda basu fiya shiri da Saghir ba, anan tayi sallolinta duk muka zauna muna hira ita dai tana ta bacin rai. Nace "Inna ki bari idan Saghir ya dawo sai ya kai ki a mota tunda ba kya son kwana" ta girgiza kai "ni da bana son ma yasan nazo? Bazan shiga motarsa ba. Allah ya tashe mu lafiya sai in tafi da safen".
Na dauki Subay'a muka tafi sama saboda naji dadin jikina sosai, na tafi da niyyar inyi mata wanka nima inyi, Asma'u kuma ta tafi kitchen tana gyara abinda muka bata. A lokacin Saghir ya dawo, yaga motsin Asma'u a kitchen sai ya leka, yana ganin ta yace "ke! Yaushe kika zo gidan nan?" Ta dan tsorata saboda bata san shigowar sa ba tunda shi dama ba sallama yake yi ba, ta gaishe shi sannan tace "dazu muka zo duba Adda, ni da Inna" yace "ita Addan taki ce tace muku bata da lafiya? ina gwoggon take?" Ta nuna masa daki a ranta tana tunanin yau Inna zata sha kunya in suka hadu da Saghir.
Ya tura kofar ya shiga, Inna tayi saurin tashi duk ta diririce saboda ganin sa haka a cikin dakin gashi tana kwance dan ma dai ba kaya ta cire ba, ya tsaya a tsaye yace "gwoggo Amina barka da zuwa, ashe waccan makaryaciyar cewa tayi bata da lafiya?" Inna tace "uhm uhm Saghir ba karya tayi ba, kowa yaga Diyam ai yasan bata da lafiya" ya daga kafada yace "to ai sai kuzo ku tafi tun kafin dare ya sake yin nisa kuma" Inna tace "mu tafi kuma?" Asma'u data shigo tace "dare ai ya riga yayi, ballantana daren damina? Anan zamu kwana da safe Inna zata tafi ni kuma zan zauna sai sunday" ya girgiza kansa "no, kuzo ku tafi yanzu. A Kano ai dare baya yi ko sha biyu kuka fita zaku samu abin hawa" ya ciri dari biyar ya ajiye a kusa da Inna "gashi ku hau adaidaita" ya juya ya fita.
Suka tsaya cirko cirko suna kallon juna, Asma'u tace "hamma Saghir bashi da mutunci Inna, bara inje in gayawa Adda tayi masa magana, yanzu ina zamu fita a wannan unguwa tasu duk kango? Ga shi har yanzu yayyafi ake yi" Inna ta girgiza kanta, "kar ki gaya mata. Dauko mayafin ki mu tafi. Allah yana nan ai shi zai kaimu gida lafiya" Asma'u bakin ciki ya ishe ta, Inna ma wani irin zafi zuciyarta take yi mata amma bata son gaya wa Diyam, shi da yayi din ai yasan ba dai dai bane kuma Diyam sai dai ta bata ranta kawai amma ba zata hana shi abinda yayi niyya ba, tasan ko bare Diyam ta aura ba zai musu wannan wulakancin ba ballantana É—an yayanta, É—an yayan mijinta. Ko Sadauki Diyam ta aura ba zai wulakanta Inna ba.
Mayafan su kawai suka dauka, lokacin karfe goma har ta gota Asma'u dan bakin ciki ko kayanta bata dauka ba suka fita ni ina can ban sani ba, ga duhu ga yayyafi anayi ga uban sanyin da yake kadawa. A bakin gate suka yiwa maigadi sallama, yace "Hajiya tafiya a cikin ruwan nan? Ku bari mana sai da safe ko kuma ayiwa mai gidan magana ya kaiku a mota" Asma'u tace "maigidan ai shi ya kore mu kuma yafi kowa sanin yana da mota".
Hanya duk ruwa ya kwanta haka suka ringa haskawa da wayoyinsu suna tafiya karnuka suna tayi musu haushi, babu alamar mutum ballantana abin hawa har suka fita bakin titi. Suka tsaya suna ta karkarwar sanyi amma babu abin hawa babu alamun sa. Asma'u ta fara kuka "Inna mu koma mu gaya masa bamu samu ba. In baya son mu kwana a gidan sa ba sai ya kaimu gida a mota ba? Ai muma muna da gidan ba'a titi muke ba" Inna dai bata ce mata komai ba. Can bayan sun gaji da tsaiwa sai suka fara tafiya a kafa suna saka ran maybe in sunzo round din yan kaba zasu samu adaidaita a can, ko babur ne ma in suka samu hawa zasuyi in dai zai kaisu gida. A lokacin sha daya na dare har ta wuce. Suna cikin tafiya ne wata mota ta tsaya a bayansu, suka juyo suna tunanin ko taimako ne tazo musu amma sai ji suka yi anyi musu fito, daganan suka gane yan iska ne dan haka suka kara sauri. Aka sake biyo su a baya aka ce "yan mata ji mana" Inna ta kankame hannun Asma'u suna sauri kamar zasu tashi sama amma sai motar ta sha gabansu, aka haske musu fuska da fitila sai wani yace "ashe ma tsohuwa ce da yarinya. Kyakykyawar yarinya" Inna ta tura Asma'u bayanta a lokacin da maza biyu suka fito daga motar. "Haba baba, Menene na boye ta? Rage mata hanya kawai zamuyi fa" dayan yace "kema in kina so sai mu rage miki hanyar amma a boot" suka kwashe da dariya sannan suka yo kan su Inna a tare. Da gudu su Inna suka diba, Asma'u tana gaba inna tana binta a baya mazan suna binsu a baya, daya yace "kunga tsohuwa ita ma ta iya gudu? Lallai itama da sauranta ashe". Basu yi wani nisa ba suka cimmasu suka kama su, Asma'u tana ta ihu, Inna tana ta rokon su su rabu dasu "me muka yi muku yaran nan? Ku sake ta dan Allah marainiya ce" daya yace "nima maraya ne, kinga mun dace kenan".
Sanda suke tisa keyar Asma'u cikin mota ne wata mota ta hawo ta bayan su a hankali, har ta gibta kuma sai tayi reverse da sauri ta tsaya. Asma'u ta fara kokawa dan ta samu karfin ganin taimako yazo mata wannan ya hana su tayar da motar har na cikin bakuwar motar ya fito da sauri ya taho gurinsu. Wanda yake rike da Asma'u ya fara zarowa daga motar yayi masa naushi biyu take sai ga jini a gaban rigarsa. Ba shiri ya sake ta ya shige motar, wanda yake seat din driver yayi saurin tayar da motar dan yana gudun karbar nasa rabon suka bar gurin a guje. Asma'u ta fadi a gurin tana mayar da numfashi cike da tsoro sannan ta juya tana kallon wanda ya taimaka mata, sai taga Inna ma shi take kallo amma maimakon tsoro mamaki ne kawai a rubuce a fuskarta. "Sadauki?" Ta fada da rawar murya "Sadauki!" Asma'u ma ta fada, tabbas, wannan fuskace da baza ta manta ba duk kuwa da cewa rabon data ganshi tun tana shekara tara a duniya yanzu kuwa shekarar ta goma sha shida. Sai ta mike da gudu ta tafi ta rungume shi. "Yar Asama" ya fada yana rabata da jikinsa, fuskarsa dauke da murmushi.