← Book details Diyam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 112

Sashe 61

Diyam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rayuwa ta cigaba da tafiya, har Fauziyya tayi sati a gidan. A ranar ne kuma Saghir ya tubure. "Babu wata shekara, ban yarda na. Eh an baku dama kuyi kyautar kwana amma sai da amincewar mijin ni kuma nace ban amince ba" na daga gira ina kallonsa a raina ina cewa 'zakayi saki reshe kama ganye kuwa' a dole na na hakura na karbi kwana na. Dokin da yake sai daya sa naji tausayin Fauziyya. Ni kuma kamar an saukar min da bacin rai haka naji nayi zamana a dakina amma sai gashi ya taho. Ina game a waya ya karba ya ajiye yace "me kike so inyi miki ne Diyam? Kuka zanyi ne ko tsallen kwado?" Na juya masa baya nace "duk wanda ranka yafi so" sai ya hawo gadon ya fara yi min tausa. Yace "da gaske fa nake. Say it, anything, yanzu zaki ga anyi miki" na tashi na zauna yace "kudi kike so?" Sai ya dauko bandir din 500 notes ya ajiye min akan cinyata yace "ki shirya gobe in kaiki shopping ki sayi kayayyakin ku na mata, kayan kwalliya, jaka, takalmi anything" na mayar masa da kudin sa nace "ka sayi kayan abinci ka kai gidan Alhaji" ya dawo min da kudin yace "angama. Can we please go to my room? Kinga Subay'a tana nan".

Washegari kuwa ya fita dani, yayi ta lodo min kaya komai ya gani na mata sai ya dauka, "wannan zaiyi miki kyau, wannan ma yana da kyau, wannan zai dace dake" haka dai yayi ta fama. Muna dawowa gida muka tarar babu abinci, bata yi ba tunda girkina ne dan haka na shiga kitchen na dora da yake weekend ne Subay'a tana sama tare da Saghir suna kallo. Riga da wando ne a jikina kaina babu dankwali na daga gashina sama ina ta aiki na ina jin kida a waya ta sai naji kawai wani strange kamshi da ban sani ba, ina juyo wa sai naga wani mutum a tsaye a palo yana kallona muna hada ido sai cewa yayi "Fauziyya tana nan?" Ni kuwa na zunduma ihu ina kiran Saghir, sai kuwa gashi nan a guje ya sauko kafin mutumin ya fita. Ya damko shi yana tambayarsa lfy sai cewa yayi wai shi gurin Fauziyya yazo shi dan uwanta ne kuma ita tace mishi ya shigo. Ranar naga bala'i a gurin Saghir, daga Fauziyyan har bakon nata ya haÉ—a ya balbale su da fada daga baya ma ya haÉ—a har da maigadi wanda yayi ta faman rantsuwa a kan cewa shi bai san mutumin ya shigo ba. Ni dai na dauki yata muka koma sama nace ku kare kalau.

Sai da daddare kuma Saghir yayi ta bani hakuri. Nace "duk wanda ya sayi rariya dama ai yasan zata zubar da ruwa. Tun da har ka auri yarinyar daka gama nema a waje ai kasan dole zata kawo maka maxa gida kaima. Duk abinda kayi ai kaima dole za'ayi maka. Haka rayuwa take" ya fahimci magana nake fada masa sai yace "kin san ai dalilin da yasa nayi auren nan ko? So nake kike kula dani yadda ya kamata sai nayi tunanin idan nayi aure kika ga wata tana kula dani kema zaki koya. Wannan shi yasa na auri Fauziyya saboda bana son in auri wata wadda itama bata iya din ba" a raina nace "oh, ita wannan ta iya din kenan"

Rayuwa ta cigaba da tafiya. Saghir har mamaki yake bani yadda yake yi min, gabadayansa ya chanja kuma duk abinda nace to kuwa zaiyi shi sai dai in bance din ba. Na saka shi ya ke kai kayan abinci gidan su, sannan kuma na daina jin warin giya a tare dashi duk da ban tabbatar ko ya daina sha ba. Fauziyya bata da problem, tana dai da daga kai da nuna irin ta fini dinnan amma tunda ta fahimci yadda Saghir yake ji dani sai ta ja baya. Bamu fiya zama muyi hira ba kowa harkar gabansa yake yi. In ranar girkin tane tayi ta iyayi da rawar kai ni kuma in ranar girkina ne Saghir yayi ta rawar kafa, duk da dai ba koda yaushe yake samun abinda yake so din ba dan wani lokacin rufe kofa ta nake in kashe waya, watarana kuma in naje in bata rai har sai ya hakura ya rabu dani. A lokacin ne kuma bikin Rumaisa ya tashi, za'a hada ayi tare dana yaya Mukhtar. Lokacin muna 22 years, tana kuma final year dinta a jami'a.

Bikin yana matsowa na tambayi Saghir sati biyu. Ya rike baki "sati biyu kuma Diyam? Kwana nawa za'ayi ana bikin da har zakiyi sati biyu?" Nace "nice fa babbar kawar amarya. In ina nan ta yaya zanyi shirye shirye?" Babu yadda zaiyi yace "shikenan" amma ina kira Mama na gaya mata zan taho tace "baki da hankali dama? Babu wani sati biyu da zaki zo kiyi, sati daya zakiyi shima kuma dan kina da abokiyar zama ne da ba zan barki ki taho ki barshi shi kadai ba" ranar har kuka nayi, I just needed a break from the house and from Saghir.

Sai satin bikin sannan Saghir ya kaini gidan Mama. Ya kuma buga min warning "saura kuma ki shiga cikin yammata kuyi ta shiririta. Kinsan dai ke mai aure ce ko?" Nace "uhm" a raina ina mamakin wai yau Saghir ne yake kishi na. Ko yaushe zan fara nasa ni?

Munsha bikin mu lafiya mun gama lafiya. Da muka je dinner naga yadda Rumaisa take nishadi da mijinta sai naji wani longing a zuciyata. I missed all this, ni banyi yammatanci ba kuma babu abinda zan adar na bikina. Ranar Lahadi muka kai amarya dakin ta. Litinin kuma na biyo su Inna muka dawo gida tunda satin da aka bani bai kare ba sai nan da kwana biyu. Muna zuwa naji Maman Iman tana soya wainar fulawa sai na aika Asma'u ta karbo min na zauna ina ci.

Ina tsaka da ci sai kawai jin sallamar Sadauki mukayi wai ashe duk mondays yake zuwa ya gaishe da Inna. Na sunkuyar da kaina ina jin wainar ta fita daga raina har ya shigo ya gaishe da Inna da Mama sannan na dago na gaishe shi. Ya amsa yace "ya family?" Sai na kasa reply. Ya mike zai tafi Mama tace "oh Sadauki kaki aure har yanzu? Ko so kake ayi maka kidan tuzuru ne?" Ta tsaya yana shafa kansa, muka hada ido yace "an kusa ai mama insha Allah" Inna tace "alhamdulillah, ai gwara ayi din, aure ai shine cikar kamala da kimar mutum. An sami matar kenan" yace "eh, a can gida ne. A Maiduguri ne" sai naji wainar dana ci duk ta tattaro ta dawo makogwaro na, da sauri na mike na shiga toilet sai da na amayo duk wainar da naci.
[2/19, 5:19 PM] +234 818 247 0922: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Seven : The Messages

Sai dana gama sannan na zauna akan toilet seat na dafe kaina, ina jin jiri yana juyani duk da cewa a zaune nake. Nayi iyakacin kokari na gurin ganin cewa ban yi tunanin maganar da Sadauki ya fada a palo ba sannan na mike na wanke bakina da fuskata na fita, ina tunanin ya riga ya tafi amma ina fita sai na ganshi a tsaye yana kallona yace "ba kya jin dadi ashe? Allah ya sawake" na sunkuyar da kaina ciki ciki nace "ameen" sannan na wuce shi zan shiga cikin daki Inna tace "ba kiji Sadauki yana miki sannu ba? Shine kika wuce ba zaki amsa shi ba?" Na juyo nace "Inna nace masa ameen, ameen, ameen summa ameen,me kuma yake so ince masa" sai kawai yayi murmushi ya juya ya fita, inna kuma ta rufe ni da fada Mama tana taya ta, na zauna kawai nayi tagumi da hannu bibbiyu ina jinsu har suka gama sannan na zame na kwanta a gurin ina jin jikina kamar mai zazzaɓi har Mama tayi mana sallama ta tafi.

Kwana biyun haka na kare su babu lafiya sosai, na so inki komawa saboda bana jin dadi amma Inna ta matsa Saghir ma kuma yace in ma zan zauna sai dai ya dauki Subay'a saboda makaranta ni kuma bana jin zan iya barin ta tare da Fauziyya dan nasan ba kunya ce ta ishe ta ba. Dan haka dole na shirya Saghir yazo muka tafi. A hanya ya kalleni yace "kin kara kiba, baki da lafiya amma kinyi kiba kin kara fari. What's the secret?" Na bata rai nace "what secret kuma?" Yayi murmushi "wai cewa nayi ko Subay'a ce zata yi kani? It is about time, tayi girma da yawa" na juya kai ina kallon titi" I missed my period wannan watan, a lokacin bikin nan ya kamata inyi kuma banyi ba but that doesn't mean anything tunda dama ina missing sometimes. Ina ganinsa yayi packing a bakery suka shiga shida Subay'a suka lodo kayan ciye ciye sannan muka tafi.

A toilet da zan shiga wanka na tsaya ina kallon kaina a mirror, da gaske nayi girma na ciko ta koina musamman hips, abinda da bani dasu sai yanzu suke zuwa kuma. A raina nace "sai yanzu makerin budurci ya tuna dani" after I lost mine long time ago.
Chapter 61 · 0% Book details