← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 49

Sashe 9

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah ka yi haƙuri Ameer ka tashi mu tafi, idan Inna ta ji Dada ta saka mu aiki ba mu yi ba ba za ta ji daɗi ba. Ka yi haƙuri ka ji?" Shiru ya yi na tsawon sakanni kafin ya miƙe ba don ya so ba. Ya haɗe fuska don ba kaɗan ba ransa ya ɓaci. Kuma sanin kanta ne ita Dadar Habule ya hana mutane shigar masa gona tsinkar wani abun, don ba shi da mutunci ko kaɗan, a kan ko da ganye ɗaya ne be ƙi ya ya ci maka mutunci ba, ya zage kaff danginku hankalinsa kwance. Ɗebo ruwa kuma da ta aiki Daneen ta yi ta san sarai an hana mata zuwa rafin, saboda gurɓatattun samari da ke zama a wajen. Ko kuma su laɓe, ba sa tashi fitowa sai 'yan mata sun zo ɗibar ruwa. A can aka kama wasu samari su huɗu sun yi wa wata yarinya fyaɗe, kafin a kai ta asibiti ta rasu. Wannan dalilin ne ya sa aka hana mata zuwa ɗibar ruwan, aka kuma samar da rijiyoyi don abin ya zo da sauƙi.

"Kar ka sake ka siyo mini na siyarwa ba na so, idan ma shi ka siyo zan gane. Ni ba sa'ar ka ba ce, don haka inda na aike ka can nake nufi ka je. Ke kuma sauri nake na ba ki mintuna biyar ki kawo mini ruwa in ɗora tuwo kar ya min dare. Idan kika sake kika wuce billahillazi sai na ci ubanki a cikin gidan nan." Dada ta faɗa lokacin da suka fito daga ɗakin. Ba su ce komai ba, sai ficewa da Ameer ya yi, ya yin da Daneen ta ƙarasa ta ɗauki wani tulu ta yi waje da shi. Baffa da tun da ta fara magana be ce komai ba, sai a lokacin ya bi su da kallo, har lokacin kuma be ce komai ba. Dogon tsaki Dada ta ja tana ƙarasa jefa gyaɗa guda ɗaya da ta yi ragowa a hannunta, sannan ta miƙe don iza wutar girki.

"Wai ana sallama da Baffan Inna-wuro." Wani yaro da ya shigo gidan bayan fitar su Daneen ya faÉ—a yana kallan Dada. Juyawa ta yi ta kalle shi kafin ta maida duban ta kan Baffa, ba ta ce komai ba, sai sake mayar da idanunta da ta yi kan yaron ta ce

"Je ka ce yana zuwa." Fice wa yaron ya yi daga gidan, ya yin da Dada ta É—aga murya tana faÉ—in

"Ai dai kana ji ana sallama da kai." Miƙewa Baffa ya yi yana faɗin

"Naa ji kam." Daga haka ya fice daga gidan. A bakin mota ya hango wani mutum tsaye, sanye cikin babbar rigar shadda, da hula zannabukar a kansa. Tsayawa ya yi da mamaki shimfiɗe a kan fuskarsa yana kallansa, don kwata-kwata bai shaida fuskar ba. Ganin fitowar Baffa ya saka mutumin ƙarasawa cike da girmamawa ya miƙa wa Baffa hannu yana faɗin

"Salamu Alaika.." Karɓar hannun nasa Baffa ya yi yana amsa wa a hankali kamar wanda ke jin tsoro. Cikin girmamawa mutumin ya sanar da shi shi ne wanda yake sallama da shi. Gyara tsayuwa Baffa ya yi kafin ya ce

"Sai dai ban shaida fuskar ba." Sauke numfashi mutumin ya yi kafin ya soma faÉ—in

"Da farko dai sunana Abubakar Bashir, ni ɗan kasuwa ne, wanda ke harkar siye da siyarwa a cikin garin Kano har ma da wajen ta. Matata Allah Ya Yi mata rasuwa, ina da 'ya'ya waɗanda ke tare da ni. A taƙaice dai na ga 'yarka ne, wadda aka tabbatar mini da nan ɗin nan ne gidan mahaifinta shi ya sa na zo don neman izini." Cike da mamaki Baffa ya ce

"Wace 'yar tawa kenan?"

"Fatima!" Ya faÉ—a kai tsaye.

"Ikon Allah." Baffa ya faɗa cike da mamaki, don kuwa zai iya cewa a tsayin shekaru sha biyar da suka gabata, babu wani da ya taɓa zuwa ya ce yana son Inna-wuron. A hankali Baffa ya ɗaga kansa ya dubi kamilallen mutumin, bai san me ze ce masa ba a yanzu dai kam. Domin kuwa tamkar ba shi ne uban ba, ba shi da ikon yanke hukunci sai abin da Dada ta faɗa. Don ko ya ce zai yanke ma, idan Dada ta faɗi saɓanin abin da ya yanke dole ne ya bi. Shi ya sa ma ba zai yi gaggawar yanke hukuncin ba, saboda kar mutunci ya zo ya zube daga baya. Dada da ke leƙe daga soro, ta sake leƙo da kanta don sake tabbatar da da gasken mota take gani zaune a ƙofar gidansu, kuma mallakin mutumin da ya zo neman auren Inna-wuro??

#MAFARI..

Na gode sosai da addu'oinku. WaÉ—anda suka kira ni, waÉ—anda suka mini gaisuwa ta DM, har ma da waÉ—anda suka mini cikin group. Thank yhu all for your kind words and condolences. I do appreciate, Allah Ya bar zumunci.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 06

__"Shi kenan, In Sha Allah zan neme ka zuwa gobe. Zan ɗan yi tunani sannan na yi shawara da matata, duk yadda muka yanke gobe sai ka dawo ka ji." Maganar da ta ji Baffa ya faɗa ita ce ta ta sanya ta ji tamkar ta daka tsalle don farin ciki. Da alama lokacin da ta daɗe tana jira ya zo. Ba ta sake jiran komai ba ta koma cikin gidan tana jiran dawowar sa. Kwata-kwata ta kasa tsaye ta kasa zaune, ji take kamar ta fita kawai ta sanar da mutumin cewa an ba shi auren Inna-wuro. Sai ta shiga zagaye tsakar gidan, tana ta saƙe-saƙe a cikin ranta. Babu dadewa sallamar Baffa ta ratso cikin gidan. Ta juya da sauri cikin farin ciki, abin da ya manta ma da mata tana faɗa wa mijinta, yau ɗin sai ga shi ta furta

"Sannu da zuwa." Ya kalle ta, sai ya ji daɗin hakan. Saboda haka ya saki murmushi yana ƙarasowa cikin gidan.

A ɓangaren Daneen da Amir kuwa, ko da suka fito kallan Amir Daneen ta yi ta ce

"Toh yanzu ya za mu yi?" Shiru ya É—an yi na wasu sakanni kafin ya ce

"Kawai ki je rijiyar majalisa, nan ne mata suke zuwa."

"Ba ni ba Amir.. Kai kuma ya za ka yi?"

"Adda in dai ke kin yi sauri kin dawo ai ni babu matsala." Ya faÉ—a a nutse. Girgiza kai Daneen ta yi ta ce

"Ba ka tsoron faɗan Dada koh? Idan ma ta kama ta haɗa da duka ko?" Ta ƙare a sanyaye. Shi ma girgiza kan ya yi kafin ya ce

"Amma dai Adda kowanne duka za ta mini ba za ta kashe ni ba ai dai koh?" Harara Daneen ta jefa masa, don har ta haddace wannan maganar tasa. Daga zarar ta masa maganar Dada, kullum amsar sa kenan, ai dai ba za ta kashe shi ba.

"Adda kar fa ki wuce mintunan da ta ba ki. Ki tafi ki je ki ɗebo. Ko kuma ki kawo in ɗebo kafin na je na siyo mata zogalen." Ya faɗa yana ƙoƙarin karɓar tulun hannunta. Janye wa ta yi ta ce

"A'ah, ka yi sauri ka je ka siyo. Ni kuma bari na je na É—ebo ruwan."

"Toh shi kenan." Ameer ya faɗa yana yin gaba. Ita ma hanyar da za ta sada ta da rijiyar ta yi da sauri saboda gudun kar ta ƙara lokacin da Dada ta ba ta. Duk da mawuyaci ne ma hakan ba za ta faru ba. Saboda ko daga fitowar su daga gida sun ci wajen minti nawa.

Tun daga nesa ta soma hango bokitai, robobi ajiye a gefen rijiyar. Wasu a hannun mamallakansu wasu kuma sun ajiye. Mutane da dama zagaye da rijiyar kowa na É—iba da gugan da ya zo da shi.

"Wayyo Allahna!" Ta ambata cikin sanyayyiyar muryarta tana lumshe idanunta. Sauke wani nannauyan numfashi ta yi, tana rasa yadda za ta yi. Ta yi shiru tana tunanin ta ina za ta fara jiran wannan layin har ya zo kanta? Anya kuwa ba ƙundunbala za ta yi ta nufi rafin nan ba? Kawai sai ta buɗe idanunta, ta sake kallan inda mutanen ke tsaye suna cigaba da ɗibar ruwansu, babu alamar za su ragu. Soma takawa ta yi tana barin wajen, kai tsaye ta nufi rafi, cikin zuciyarta tana karanto duk addu'ar da ta zo mata. Duk da yadda take jin tsoro, amma ba ta sare ba, ta dogara da addu'ar nan da take yi, ta san in Allah Ya yarda babu wani abu da zai faru.

"Daneen.." Ta ji an ambata lokacin da take dab da ƙarasawa rafin. Da sauri ta juyo cike da mamakin jin muryar Innarsu. Da mamaki Inna-wuro ke kallan ta. Fasa tafiya Daneen ta yi ta dawo da baya zuwa wajen Inna ta ce a mamakance

"Inna.."

"Na'am, ina za ki je?" Ta ƙare tambayar tana kallan tulun hannunta. Ita ma Daneen ɗin kallan tulun ta yi kamar wadda ta manta da wanzuwarsa a hannunta. A narke ta soma faɗin

"Inna, Dada ce ta ce na je na ɗebo mata ruwa.. Kuma ta ba ni ƙididdigaggun mintuna. Na je rijiyar majalisa mutane sun fi nawa, shi ne zan je na ɗebo a rafi. Amma ina tafiya ina addu'a." Ta ƙare maganar tana kallan fuskar Innar don ganin yanayinta.

"Ya ilahy." Inna ta faÉ—a tana dafe goshinta. Sai kuma can ta É—ago ta kalli Daneen ta ce

"Kar na sake ji Daneen.. Kar na sake ji kin ji koh? Ba ni tulun." Ta faɗa tana miƙa hannu, babu musu ta saki tulun Inna ta riƙe. Ta juya ta kalli almajirinta da ke kwasar mata kaya idan za ta tafi kasuwa ko kuma idan za ta koma gida.

"Ɗan yi maza ka je ka ɗebo mini ruwa." Babu musu ya amsa yana karɓar tulun. Bayan mintuna kaɗan sai ga shi ya dawo. Cigaba da tafiya suka yi har zuwa ƙofar gidan. Sai a lokacin Daneen ta karɓi tulun, Inna ta karɓi kayanta ta shiga da su cikin gida. Inda Daneen ta ci sa'a, zumuɗin da Dada ke ciki ya sanya ta mantawa ma kwata-kwata da aiken da ta yi. Burinta kawai Inna-wuro ta dawo ta sanar da ita sun yi mata miji.
Chapter 9 · 0% Book details