← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 49

Sashe 38

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya yi kyau." Ya faɗa daga can ɓangaren, daidai lokacin da ta sauke wayar daga kunnenta. Ta yi shiru kamar mai tunani, sai kuma ta sake sauke ajiyar zuciya, kai tsaye ta wuce banɗakin. Sakin baki ta yi tana kallon banɗakin da ya gaji da haɗuwa tamkar ba banɗaki ba. Kai idan ba don ta fara wayewa ba, da yau ne farkon zuwanta garin nan cewa za ta yi ba banɗaki ba ne. Don kuwa tsaff za ta samu wajen kwanciya, tsaff za ta iya yin shimfiɗa ta kwanta abin ta ba tare da ta san cikin banɗaki take ba. Haka dai tana ta kalle-kallenta da mamakin yadda masu ginin gidan 'yan birnin nan ke zama su tsara ko'ina, ciki kuma har da toilet. Ita dai ruwa ta tara a bokiti ta yi wankanta kamar yadda ta saba a gida. Zuwa can ta fito bayan ta mayar da hijab ɗin jikinta. Doguwar rigar abaya ta tarar a kan gadon, ta ɗauka tana kallon ta. Sai kawai ta zumbula ta, ba ta bi ta kan mayafin ba, ta mayar da hijab ɗin. Sai ta cusa wayar cikin kayan da ta cire, ta ninke su waje guda. A ɗakin ta ci gaba da zama, wani sashe na zuciyarta na faɗa mata ta fita, saboda ta din ga ganin motsin Tareeq, ya yin da wani sashen ke raya mata da kar ta yi gaggawa. Yau ne ranar ta farko cikin gidan, don haka ta bari zuwa gobe sai ta fara aiwatar da abin da ya kawo ta.

... Washegari da safe tun da suka fita ba ta sake jin motsin su ba. Saboda sun san da baƙunta, nan suka ajje mata abin karyawa, suka kuma bar ta ta sake sakewa ita ɗaya kafin baƙuntar ta sake ta. Ba ta san me za ta faɗa wa Yohana ba idan ya kira ya tambaye ta yadda ake ciki ba. Don haka kawai ta miƙe, gwara a yi komai da wurwuri, ko zuciyarta ita ma za ta samu sassaucin abin da take ji. Cike da takatsantsan take takawa, tana yi tana duba gefen ta don kar ta haɗu da wata. Cikin sa'a kuwa har ta fito palourn Maama ba ta ga kowa ba. Don haka a gaggauce ta fice daga palourn. Daidai lokacin da shi kuma yake ƙoƙarin wucewa. Da sauri ya yi baya, saboda yadda ya lura sam ba ta san da tahowar wani ba. Cike da mamaki yake bin ta da kallo. Rashin tsammanin ganinsa ya sanya ta ji ƙirjinta ya wani irin bugawa. Sai ta runtse idanunta da sauri ko za ta samu ta ji nutsuwa ta zuwar mata.

"Ina so.. ne na je na.. gaisar da Kaka." Ta faÉ—a cikin inda inda. Shiru Tareeq ya yi yana kallon Daneen na tsawon sakanni, kafin ya É—auke kyawawan idanunsa daga kanta. Ba tare da ya nuna ya ji abin da ta faÉ—a ba ya ce

"Kin tashi lafiya? Ya jikin naki?" Runtse idanunta Daneen ta sake yi a karo na biyu, ta tsani ta ji ya yi mata wannan tambayar, kai gaba É—aya ma ba ta son wata magana ta haÉ—a ta da shi. Ji take kamar kar ta amsa, ji take kamar ta yi wucewarta ba tare da ta tanka masa ba. Sai dai kuma ta san hakan ka iya zama abu na farko da zai kawo cikas na zamanta cikin gidan. Ta san hakan ka iya janyo zargi a wajen kowa ma ba shi kaÉ—ai ba. Don haka cikin dakiya ta furta

"Alhamdulillah."

"Ma Sha Allah, Allah Ya ƙara afuwa. Hope dai kin ji daɗin gidan namu?" Ya faɗa ba tare da shi kansa ya yi tsammanin hakan ne zai fito daga bakinsa ba. Don tabbas da wani ɗan gidan nasu na wajen shi kansa sai ya yi mamaki. Ko da yake magana fa ake a kan wanda ta ba shi ƙoda. Shi ma kansa hakan ya ɗauka a matsayin dalilin da ya sa yake son jin lafiyarta a ko da yaushe. A yanzu kam har cikin zuciyarta shiru ta yi niyyar yi, ta damƙe hannunta ɗaya da ke cikin ɗayan. Da ƙyar, kamar wadda aka yi wa dole ta ce

"Ehh."

"Madallah." Ya faɗa, daga haka bai sake cewa komai ba ya wuce parking space a gaggauce. Ɗaga idanunta da har kalarsu ta sauya ta yi ta bi shi da kallo, zuciyarta ban da harbawa babu abin da take yi. Tana kallon yadda yake ɗan waige-waige lokaci zuwa lokaci. 'Duk wasu alamomi sun nuna ba ya son kowa ya lura da fitar tasa, wata ƙila ma wajen fasiƙancin zai nufa, shi ya sa ba ya so a sani.' Ta raya hakan a ranta, daidai lokacin da Ameer ya faɗo mata cikin rai. Ta yi yaƙe tana fesar da iska daga bakinta, don hana kukan da ta ji ya taho mata fitowa. Kawai sai ta juya da sauri ta koma cikin ɗakin da aka sauke ta.

... "Huh Hidaya Yah Abdoul ne, wallahi Yah Abdoul ne Hidaya. Ina zan saka kaina don daɗi, karanta ki gani fa, neman amincewa ta yake a kan soyayyarsa. Ina zan saka kaina don daɗi Sisi?" Sultanah ta faɗa lokacin da Hidaya ke a jikinta ta ruƙunƙume ta kamar za ta ɓalla ta. Dariya mai suna dariya Hidaya take yi, don babu ƙarya ta taya 'yar'uwarta murna ainun.

"Na gani Sisi, Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah." Hidaya ta faɗa tana murmushi. Sai a lokacin sannan suka koma suka zauna. Daneen da ke gefe kwance kamar mai bacci tana jin duk abin da suke cewa. Sai dai ba za ka taɓa zata ba, duk da kwanciyar da ta yi ba irin ta bacci ba ce, amma za ka yi tsammanin baccin ne ya kwashe ta ba tare da ta sani ba.

"Mu tashi Daneen ta ci abinci tun kafin Maama ta shigo ta ci mana mutunci." Hidaya ta faÉ—a tana kallan Daneen. Girgiza kai Sultanah ta yi kafin ta ce

"A'ah, bar ta ta yi baccin, idan ta tashi sai ta ci. Yanzu dai mu yi magana a kan abin farin cikin da ya same mu. Ya kike gani? In faɗa wa Maami?" Waro ido Hidaya ta yi ta karɓi wayar hannun Sultanah ta ce

"Hajjaju, ki ba shi amsa tukunna. Maami kuma ba yanzu ba gaskiya, mu bari sai komai ya kankama tukunna." Ta ƙare tana murmushi. Jinjina kai Sultanah ta yi kafin ta ce a sanyaye.

"Ga shi dai cikin farin ciki nake ji na Sisi, amma ban san me ya sa nake jin wata irin faÉ—uwar gaba ba. Na kasa gane dalili." Murmushi Hidaya ta yi tana kamo hannun 'yar'uwar tata ta ce

"Cikin farin ciki kike jin ki fa Sulty, ina da tabbacin hakan na da nasaba da farin cikin. So ki kwantar da hankalinki, burin ki ya kusa cika In Sha Allah. Yah Abdoul zai so ki fiye da yadda kike son shi."

"Ina fatan hakan." Sultanah ta faÉ—a a sanyaye.

"Ya kamata mu je gidan Umma, kin san dai halinta da na Jawahir É—in kanta. Biki yana ta matsowa." Ajiyar zuciya Sultanah ta sauke kafin ta ce

"Wato Hidaya mu sake gode wa Allah da Ya ba mu ɗan'uwa irin Yah Tareeq wallahi, har abada zan ci gaba da alfahari da shi, ki ga dai yadda silar sa nake ta farin ciki. Bikinsa kuma nan da sati biyu, ai dole ne mu tashi tsaye. Daɗin abin kuma Jawahir ce matar. Allah dai Ya tabbatar da alkhairinsa." Taɓe baki Hidaya ta yi kafin ta ce

"Ameen dai, duk da dai ni wallahi ban wani so haÉ—in nan ba." Duka Sultanah ta kai mata a kan yatsun hannunta ta ce

"Ke Sisi."

"Yoh Allah kuwa." Motsin da Daneen ta yi ne ya sanya Hidaya kallon ta. Ta dubi Sultanah ta ce

"Kin ga kar mu tashi baiwar Allah, zo mu fita mu ba ta waje." Ta faɗa tana jan hannun Sultanah. Babu musu Sultanah ta miƙe a nutse suka fice daga ɗakin. Wani irin gumi ke tsatstsafowa Daneen tun da ta ji abin da suke faɗa. Ta kai wajen mintina goma tana sake tauna maganganun nasu, kafin ta miƙe ta ɗauko wayar nan daga inda ta ɓoye ta. Hannunta har karkarwa yake yi, lokacin da ta ke nemo number Yohana cikin karambani. Sai kuwa ga shi ta gano ta, ta danna masa kira tana jin wani irin zafin zuciya. Idan har Tareeq ɗin ya yi aure ya bar ta cikin gidan me kenan?

"Daneen." Ya ambata tun kafin ta ce komai. Ba tare da ta amsa kiran sunanta da ya yi ba, ta soma faÉ—in

"Yanzun nan na ji ƙannensa na faɗin aurensa nan da sati biyu. Na rasa me ma zan ce ne ni kam." Cikin wani irin tashin hankali Yohana ya miƙe tsaye, idanunsa har wani ƙanƙancewa suke yi. Ya kai wajen mintina biyu bai ce komai ba, kafin daga baya ya buɗe bakinsa ya ce

"Ya zama dole mu tashi tsaye.. Kamar yadda yake, har yanzu babu abin da ya canja a ƙudirinmu, sai dai a yanzu sati biyu ne da mu ni da ke. A cikin kuma sati biyun ne za mu yi duk abin da ya kamata. Ki shiga cikin jerin abubuwan da suke kan wayar, za ki ga Whatsapp, ki shiga ciki zan tura miki wasu hotuna, ki duba ki karanta da kyau. Zan yi miki bayanin komai ta can. Abin da kawai nake so na tunasar da ke, dole sai kin dage, sai kin cije, kin saka wa kan ki jarumta. Kin ji kowacce kasada ce za ki iya don samun damar cika burina, da kuma naki. Hakan ma ya yi daidai, ko babu komai idan muka san muna da ƙayyadaddun kwanaki, za mu fi yin aikin da sauri. Ki ajje wayar yanzun nan ki shiga abin da na faɗa miki." Daga haka ya yi mata bayanin yadda za ta hau online ɗin yana jiran ta.

"Kar ki manta sati biyu ne kawai da mu." Ya sake maimaita mata kafin ta katse wayar. Tamkar yana gabanta ta jinjina kai, tana jin ko ma wacce irin kasada ce za ta yi domin cikar burinsa, daga nan kuma ya samu ya shigar mata da Tareeq ɗin ƙara, a ƙwatar wa Ameer haƙƙinsa.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..
Chapter 38 · 0% Book details