Sashe 20
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"In Sha Allah Rankiyadaɗe." Ta amsa da hakan cike da girmamawa. Daga haka Aunty ta fice daga ɗakin. Babu daɗewa Daneen ta fito daga banɗakin sanye cikin kayan da suka matuƙar karɓi halittar jikinta. Sai jan rigar jikinta take tamkar wadda ta ɗage mata. Duk sai take jin ta a takure, duk da kayan ba kama ta suka yi ba. Sai dai duk da haka sai ta tsinci kanta gefe guda tana jin daɗi. A rayuwarta tana son sabon kaya, shi ya sa duk lokacin da Inna-wuro ta siya musu sabon kaya farin cikinsu na ranar daban yake. A hankali ta ɗaga idanunta ta kalli matar da ita ma ita take kalla, daidai lokacin da ta ce
"Yawwah, mu je koh?" Ta faɗa tana murmushin da ya sa Daneen sake kallan ta. Don za ta iya cewa wannan shi ne karon farko da ta ga murmushinta tun shigowar ta ɗakin. Ɗaukar mayafin da ke ajje Daneen ta yi, ta lulluɓa kamar yadda suka saba a ƙauyensu, idan sun tashi saka mayafi musamman da sallah. Ba tare da ta ce komai ba ta bi bayan matar suka soma tafiya. Tafiya mai ɗan tsayi suka yi, kafin suka isa wani ƙaton palour. Kai tsaye matar ta afka ciki, har lokacin Daneen na bayanta suka shige cikin ɗakin. Ƙaton palour ne irin sosai ɗin nan. Aunty na zaune daga gefe can kan wata kujera. Ya yin da wasu maza su huɗu ke zaune kowa a kan kujera mabambanta.
"Hajiya ga ta." Matar nan ta faɗa kanta a ƙasa. Ba kuma ta jira amsar Aunty ba ta fice daga ɗakin. Neman waje Daneen ta yi ta zauna tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa. Kafin ta kai ga cewa komai Aunty ta dubi waɗannan gabza-gabzan manyan mutanen da ke zaune gaban ta. Waɗanda a shekaru a ƙalla gaba ɗayan su za su ba wa 40 baya.
"Ga haja nan fa, kai tsaye ku faɗi farashi ba sai an ɓata lokaci ba. Kun san sabgogi sun yi mini yawa." Ta faɗa tana murmushi. Ita dai Daneen ta yi ƙwam, don kwata-kwata ba ta fahimci inda zancen Auntyn ya dosa ba. Amma haka nan kawai kamar ɗazun ta kasa sukuni. Ta ma rasa wanne irin aiki aka ɗauke su ne ita kam. Gaba ɗaya zuba wa Daneen ido suka yi na tsawon mintuna. Kowanne na kallan duk wata halitta ta jikinta da za su iya hasashe, tun da tana lulluɓe ne cikin mayafi. Wani daga cikinsu ya gyara zama, yana murmushi ya ce
"Na karɓa a 500k." Duk tunaninsa za su bar masa ita ne, su ce ta yi ƙanƙanta. Don shi ƙanƙantarta ya soma gani, ya kuma san dukkansu ma za su gan ta. Kuma idan aka yi sa'a ya same ta tabbas zai huta da kyau, don shi kaɗai ya san abin da ya hango. Sai dai tun kafin ya ajiye zancen nasa, wanda ya fi kusa da shi ya ce
"Na ƙara 200k a kai." Cike da mamaki ya kalle shi yana ji tamkar ya miƙe ya masa duka, sai dai maganar da ya ji daga ɗaya gefen nasa ita ce ta sanya shi juya wa jiki a sanyaye.
"Na karɓa a 900k."
"Na cike ya zama 1million." Ya yi ƙarfin halin faɗa don so yake ba sai an ja da nisa ba kawai su bar masa yarinyar ya tafi da ita ƙasar da zai tafi su shana a can. Haka suka dinga yi, kamar waɗanda ke siyan kaya. Idan wannan ya ji wani ya kere su, sai wannan ya ƙara kuɗi masu yawa. Har zuwa lokacin da duk suka yi shiru bayan da ɗaya daga cikinsu ya faɗi kuɗin da ya kere su matuƙa. Abin ya ba wa Aunty nishaɗi, don haka ba ta so aka tsaya a iya nan ba. Ta so sun cigaba da tayawa kuɗin da za ta samu su yi ta hauhuwa. Amma duk da haka, yau ɗin ta samu kuɗi masu yawa ta dalilin Daneen.
"Kar ku damu za a kawo wasu kayan ko zuwa gobe ne." Aunty ta faɗa tana kallan waɗanda suka miƙe. Ɗaya ne kawai ya iya amsa mata, ya yin da ragowar ficewa kawai suka yi. Wanda ya yi nasarar biyan kuɗin da suka shallake na kowa ya ce
"Sai haƙuri fa, kara wa da ni sai an shirya." Ya ƙare yana murmushi. Ita dai Daneen gaba ɗaya duk wani ruwan kanta ya tsotse, jikinta ya yi sanyi, ya yin da duk wasu abubuwa da ke faruwa cikin ɗakin ke sake ruɗa ta, suke kuma tunkuɗa kwanyarta cikin tunanuka barkatai. 'Anya kuwa?' Ta tambayi kanta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa kamar za ta faso ƙirjinta. Ita dai ta ji suna maganar kaya, haja, amma kuma ba ta ga wasu kaya a wajen ba. Hasalima idan maganar kaya za su yi, ba ta ga amfanin wanzuwarta a wajen ba.
"Za ki ji Alert yanzu, abin da ya rage kawai ki ba ni yarinya." Murmushi Aunty ta yi kana ta ce
"Ba ni da matsala da kai, ai kai nawa ne. Yarinya kuma ga ta nan. Maza tashi ki bi shi shi ne zai samar miki aikin." Aunty ta faɗa tana taɓo Daneen. Wani tsinke wa da gaban Daneen ya sake yi ya faɗi shi ne ya sanya ta saurin runtse idanunta tana faɗin
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Mutumin ya sake bin Daneen da kallo lokacin da ta É—ago idanunta ta kalli Aunty.
"Shi zan bi?" Ta tambaya kamar wadda ba ta ji abin da Auntyn ta faÉ—a ba. Don kar shakku ya shiga zuciyar Daneen É—in ya sanya Aunty faÉ—in
"Eh, shi zai kai ki gidan da za ki dinga yi wa aiki, kar ki damu."
Shiru ta yi na en wasu sakanni kafin ta sake ɗaga ido ta kalli Aunty. Abin da yake ta mata yawo a ƙwaƙwalwa shi ne ya sa ta buɗe baki ta ce a sanyaye
"Ƙanina Ameer." Ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta. Mutumin da ya yi nasarar biyan kuɗin da suka take na kowannensu ya wani lumshe ido yana jin yadda sanyayyiyar muryar Daneen ke neman kashe shi a zaune.
"Don Allah tashi ki kira mini ƙanin nata mu tafi." Ya faɗa yana miƙewa. Kallan sa Aunty ta yi ta ce da mamaki
"Da ƙanin nata za ku tafi?"
"Rabu da ita, kira mini shi, shi ma za a samar masa aikin yi. Ki yi da jiki please." Ba ta sake cewa komai ba, ta ɗauki wayarta ta bayar da umarnin fito da Ameer da ke can ɓangaren mazan gidan. Babu daɗewa kuwa sai ga shi wani ya rako shi, lokacin har sun fito waje, mutumin na ƙoƙarin shiga motarsa ya yin da Daneen da tunane-tunane ke ta shigar ta tana tsaye daga gefe. Sai a lokacin ta saki murmushi tana kallan Ameer, shi ma murmushin ya maida mata yana ƙarasawa ya kama hannunta ya ce
"Adda."
"Uhmm Ameer."
"Har na yi kewar ki Addatah, na É—an wannan lokacin." Ya faÉ—a yana murmushi. Hannunta ta kai ta ja kumatunsa tana faÉ—in
"Ni ma haka ɗan'uwa." Daga haka babu daɗewa, suka shiga motar mutumin. Daneen na gaba, ya yin da Ameer ke baya. Ya shiga motar ya tayar, babu ɓata lokaci suka fice daga gidan.
.. A parking space na gidan ya yi parking na motarsa, kai tsaye palourn Dadaji ya wuce, yana cikin shigar ƙananan kayan da suka matuƙar yi masa kyau. Kansa babu komai sai tulin sumar da Allah Ya ba shi mai matuƙar kyau da ɗaukar idanu. Cikin nutsuwa da tafiyarsa mai cike da mazantaka ya ƙarasa ɗakin Dadaji, bakinsa ɗauke da sallama. Ya yi mamakin hayaniyar da ya ji tana tashi tun kafin ya ƙarasa cikin ɗakin. Sai dai duk da haka bai fasa shiga ba, ya shige cikin ɗakin.
"Wa alaika salam. Barka da zuwan Tareeq." Dadaji ta faÉ—a tana kallan sa. Sassanyan murmushin da ya kan daÉ—e wa bai yi shi ba ya wanzu a kan fuskarsa. Wanda idan ba sanin ainahin yadda fuskarsa take ka yi ba, ba za ka É—auka murmushin ya yi ba.
"Dada ji." Ya faÉ—a lokacin da ya nemi waje ya zauna a kan kujerar É—akin.
"Hala dai koro ka aka yi da farar yammar nan." Murmushi ya yi mai sauti yana gyara zamansa ya ce
"Dada jiii." Ya faɗa yana jan ƙarshen sunan nata. Kafin ta kai ga amsawa ya ce
"Hayaniyar me nake ji ne?" Kallan inda zai sada ka da cikin gidan Dada ji ta yi kana ta ce
"Kar ka nuna kamar ba ka san abin da ke faruwa ba mana." Girgiza kai ya yi da mamaki shimfiÉ—e a kan kyakkyawar fuskarsa. Gane abin da yake nufi ne ya sanya Dada ji faÉ—in
"Ba gobe ne Alhassan zai dawo ba?" Cike da mamakin dai ya cigaba da kallan Dada ji. Bayan shuÉ—ewar wasu sakanni ya ce
"Abeey zai dawo, amma Maama ba ta sanar da ni ba? A taƙaice ma dai babu wanda ya sanar da ni. Rashin muhimmancin nawa ya kai haka?" Ya tambaya a nutse yana kallan Dada ji.
"A'ah, kar ranka ya ɓaci Tareeq. Duk na gida ne suka zo fa. Ƙannen mahaifinka ne kaɗai cikin gidan nan ba na waje ba."
"Sultanah ba ta shigo ba?" Ya kawar da waccan maganar ya kawo wannan.
"A'ah ta shigo babu daɗewa, uwarta ta aiko kiran ta za ta taya ta aiki. Ka san ita ma tana can tana shirye-shiryen dawowar Abeeyn naku." (Don en gidan gaba ɗayansu ba dai takatsantsan ba, musamman a kan abin da ya shafi cimarsu. Shi ya sa duk girman gidan nan babu mai dafa abinci, sai dai en aiki masu yin wasu ayyukan. Amma duk wani abu da ya shafi cikinsu su suke yi da kansu. Ko dai su iyayen su yi, ko kuma 'ya'yan su yi. Ko a ɓangaren Dadaji ma da take uwar masu gidan, ba ta da mai dafa mata abinci. Daga ɓangaren matan ɗan nata ake kawo mata. Ko kuma Sultanah ko Hidaya wata ta je ta girka mata idan tana free.)
Jinjina kai Tareeq ya yi kafin ya miƙe daidai lokacin da yake faɗin
"Bari na je, zan kira Abeeyn zuwa dare In Sha Allah."
"Toh Allah Ya yarda. ÆŠazun nan ma Jawahir ke tambayarka." Har ya soma tafiya sannan ya ce