Sashe 11
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na san zuwa yanzu kun fahimci abin da ya faru. Yaron nan ya yi mini satar zogale. Ni kuma wallahi ba zan haƙura ba, don haka zuwa na yi a biya ni kuɗin abin da ya tsinkar mini." Habule ya faɗa yana gyara tsayuwarsa. Tun da suka zo wajen kwata-kwata Ameer ya kasa ko da ɗaga idanunsa ne ballantana ya kalli mutanen da ke tsaye a wajen. Shi kaɗai ya san yadda kalaman da ake faɗa suke sukar zuciyarsa. Ya rasa abin da ze yi, ya rasa ya ze yi. Be san cewa mutane da dama ƙiris suke jira a kansu ba sai yanzu, sai da abin nan ya faru.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Ameer! Yanzu nan sai da ka nuna halinka a waje? Sata da farar ranar nan? Oh jama'a.. Jinin Hadeeza sun shiga 3." Dada ta yi maganar tana tafa hannu. Babu shiri Ameer ya É—aga idanunsa ya kalli Dada, cike da mamakin maganganun da suke fito wa a bakinta. Cikin sauri kuma sai ya mayar da idanunsa kan Inna-wuro da ta runtse idanunta cikin rashin sanin abin yi. Girgiza kai ya shiga yi tamkar tana kallansa
"A'ah Inna, kar ki yarda da abin da suke faɗa, wallahi ban yi masa sata ba. Ɗansa ne ya ce mini in je in tsinka tun da ban samu na siyarwa ba. Inna kar ki yarda, wallahi ban yi masa sata ba Inna." Ya ƙare maganar gwanin ban tausayi. Shi gaba ɗaya abin da mutanen ke masa be dugunzuma masa hankali ba kamar tsoron ka da Innarsa ta yarda da abin da suke faɗa.
"Dallah rufe mana baki ɓarawon banza ɓarawon wofi." Wani da ke gefen Habule ya faɗa yana tunkuɗa masa ƙeya. Ya tafi kamar ze kifa kafin ya dawo a kan ƙafafunsa. I zuwa lokacin zuciyarsa ta yi taurin da yake ganin ba ze iya jure wannan cin mutuncin ba. Wani irin zafi zuciyarsa take masa, ji yake kamar ya fasa ihu ko ze ji sauƙin abin da yake ji. Don haka a fusace ya juya ya cakumi wuyan wanda ya tura shi yanzun. Cikin ƙanƙanin lokaci maganar mutane ta soma tashi a wajen, kowa da abin da yake faɗa. Tuni ya ƙwace jikinsa daga hannun Habule. Kamar yadda ya cakumi wuyansa, haka shi ma wancan ɗin ya cakuma, suna shirin soma faɗan ya ji an riƙo hannunsa. Cakk ya dakata, ya ɗaga idanunsa ya sauke a kan fuskar Inna da ta riƙe hannunsa. Ta girgiza masa kai a sanyaye, muryarta ma a sanyaye ta furta
"Rabu da shi.. Allah zai saka maka." Ta ƙare maganar tana jan hannunsa. Babu musu ya sake shi, har lokacin yana jin yadda zuciyarsa ke cigaba da wani irin zafi, gefe guda kuma wani rauni ne a cikinta. Ganin da Habule ya yi Inna-wuro ta ja hannun ɗanta ya sanya shi saurin faɗin
"Ina za ku je ba tare da kun.."
"Daneen ɗakko kuɗi ki ba shi." Maganar Inna-wuron ta katse masa maganar da ya soma. Ya ja ƙwafa yana faɗin
"Ah toh." Kusan a tare suka shige gidan su ukun, har lokacin Inna-wuro na riƙe da hannun Ameer.
"Don Allah ka yi haƙuri, ka san halin 'ya'yan yanzu.. Ka yi haƙuri amma tabbas zan tsawatar masa, ta yadda ba zai sake marmarin ɗaukar abin wani ba." Maganar Dada kenan, wadda ta sauka a kunnen Daneen lokacin da ta fito daga cikin gida, hannunta ɗauke da kuɗi ta miƙa wa Habule, ba ta jira ya ce komai ba ta koma cikin gidan tana cigaba da tariyar kalaman Dadan.
"Babu komai." Habule ya faɗa lokacin da yake ƙirga kuɗin hannunsa.
"Ka yi haƙuri." Baffa da tun ɗazun be ce komai ba ya faɗa yana kallan Habulen. Jinjina kai Habule ya yi yana kallan mutanen da suka biyo shi ya ce
"Ku wuce mu je." Duk sai suka ɗunguna suka bi bayansa. Dada da Baffa suka bi bayansu da kallo har sai da suka ɓace musu da gani. Ƙwafa Dada ta ja ba tare da ta ce komai ba ta shige cikin gida, babu daɗe wa Baffa ma ya bi bayanta zuwa ciki.
A ɗaya ɓangaren kuwa, a sukwane Daneen ta nemi gefen Ameer ta zauna, yana zaune kansa ɗore a kan gwuiwarsa. A hankali ta kai hannunta ta dafa kafaɗarsa, cikin sanyi ta ce
"ÆŠan'uwa." Runtse idanunsa ya yi kafin ya buÉ—e, ya É—ago a hankali ya kalli Daneen. Girgiza mata kai ya shiga yi yana jin yadda zuciyarsa ke karyewa.
"Adda wallahi ba sata na yi masa ba." Ya ƙare yana riƙo hannunta. Idanunta da suka cika taff da hawaye ta lumshe tana buɗe wa a lokaci guda. Sai ta shiga jinjina kai tana riƙe hannunsa sosai.
"Na sani Ameer.. Inna ma ta sani, ka dena damun kanka."
"Amma kin ji abin da Dada ta faɗa koh? Tun da nake na taɓa sata a rayuwata ne? Me ya sa ne muke rayuwa a cikin gidan nan Adda? Babu wanda ke sonmu fa sai mu kanmu. Ni ba ɓarawo ba ne Adda. Wallahi ba ɓarawo ba ne ni." Ya ƙare yana fashe wa da kuka. Sai a lokacin kukan da ita kanta Daneen ɗin ke riƙe wa ya fito fili, ta ja Ameer jikinta ta rungume ita ma tana fashe wa da kukan.
"Ya isa haka Ameer.. Ya isa haka.." Ta yi ƙarfin halin faɗa. Cigaba da girgiza kai ya yi, don tabbas abin da ya faru ya masa zafi, kukan da yake shi ne kaɗai zai sanyaya masa zuciya. Ita ma Daneen ɗin ba ta hana shi ba, ta bar shi ya yi kukan, dan ta san hakan zai taimaka wajen rage raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa.
"Ku dena kuka In Sha Allah, Allah zai kawo mana mafita nan ba da daɗewa ba." Inna ta faɗa tana haɗa su su duka ta rungume. Ba ta so ta bar wata alama da zai sa su fahimci ita ma tana cikin damuwar. Sai dai za ta iya cewa abin da take ji cikin zuciyarta ya fi wanda suke ji. Ita kaɗai ta san abin da take ji a duk lokacin da kalmar 'ɓarawo' ta faɗo mata cikin rai. Mummunar kalmar da aka jefi ɗanta da shi. Mummunar kalmar da mutane da dama suka kira ɗanta da shi. Kawai sai ta runtse idanunta tana jin yadda Ameer yake sauke ajiyar zuciya cikin ƙunar rai. Lallai yau ɗin tabbas abin ya taɓa zuciyar Ameer, tun da har yake kuka, duk kuwa da ƙarfin zuciya irin nasa duk da ƙananun shekarunsa.
Ranar dai haka suka wuni babu walwala. Cikin sa'a kuma ita ma Dada sai ba ta kula su ba. Ta cigaba da harkokinta daga tsakar gida zuwa cikin É—aki.
Washegari da ta kasance babu makaranta bin Innar suka yi kasuwa. Ba su suka dawo gidan ba sai da yamma. Har kuma zuwa lokacin Ameer be koma daidai ba. Daneen da Inna-wuro ke ta ƙoƙari wajen ganin sun kwashe damuwar da ya ɗora wa kansa.
... "Kin sanar da shi kin amince?" Tambayar da Dada ta jefa mata kenan tun kafin ta ida shigo wa soron gidan. Gaba É—aya sai ta ji jikinta ya yi sanyi, ta girgiza kai kafin ta ce
"Na sanar da shi zan yi shawara, sannan kuma na nemi zaɓin Ubangiji." Inna-wuro ta faɗa a sanyaye, cike da fatan Dadan ta amince da hakan, ko dan kasancewar yanzu ba kamar da ba ne. Tun da yanzu da hankalinta ba kamar da ba.
"Toh ki koma ki sanar da shi kin amince.. don wallahi ba shawararki muke nema ba, umarni ne muke ba ki. Ki koma ki sanar da shi kin amince, ko kuma yau É—in nan wallahi ki ga abin da zan muku cikin gidan nan, babu ruwa na da wasu 'ya'ya da kika tara wallahi ci miki mutunci zan yi." Dada da ke dab da soro ta faÉ—a tana maka mata harara. Girgiza kai Inna-wuro ta yi ta ce a sanyaye
"Dada.."
"Ka saka baki Malam.. Wallahi ba kirki ne da ni ba, ka da ki ɓarar mana da wannan damar." Dada ta faɗa tana kallan Baffa da ke zaune a tsakar gidan. Ɗaga idanunsa ya yi ya kalli Inna-wuro ya ce
"Kin ga maza koma ki sanar da shi kin amince. Mun riga mun zaɓa miki shi, babu buƙatar wani tunani kuma." Duk da yadda zuciyarta ke bugawa hakan be hana ta juya wa ba, ƙafarta har wani rawa take lokacin da ta bi umarnin mahaifinta wajen koma wa wajen mutumin. Har ya shiga cikin motar ya tayar da ita, ya hangi Inna-wuro da ta fito. Sai ya kashe motar cike da mamakin abin da ya fito da ita bayan sun yi sallama. Kai tsaye inda take tsaye ya nufa yana kallan ta.
"Ina so mu yi wata magana." Inna-wuro ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye. Ita kam ta rasa wannan wace kalar rayuwa ce. Ta rasa mafita a rayuwarta. Tana so ta inganta rayuwar 'ya'yanta, sai dai da alama Dada tana so ta yi mata cikas. Maimakon a ce yanzu haka maganar auren 'yarta ake, amma wai nata ake. Ba ta san dalilin Dada na saka mata ido ba. Ba ta san me ye ƙudurin Dada a kanta na son sai ta yi aure ba.
"Ikon Allah! Ina sauraron ki." Alhaji Abubakar ya faɗa yana gyara tsayuwarsa. Sauke numfashi Inna-wuro ta yi tana tunanin ta inda za ta fara. Sai dai kawai ta yi ƙundunbala wajen soma faɗin
"Ina da 'ya'ya guda biyu.. Ina neman alfarmar idan dai har za ka aure ni ka bar ni na taho da su. Ni ba zan ɗora maka komai ba. Ni zan din ga musu komai da ake buƙata, ni dai buri na kawai ka amince na zo da su gidanka." Cikin matuƙar farin ciki ya ce
"Kina nufin idan dai har na amince da hakan kin amince za ki aure ni?" Runtse idanunta Inna-wuro ta yi, kafin ta shiga jinjina kanta a sanyaye. Murmushi ya yi, har cikin ransa yana jin daÉ—i. Ya buÉ—e baki a nutse ya soma faÉ—in