← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 49

Sashe 12

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni da ba ki guje ni ba duk da ina da 'ya'ya, kika kuma amince za ki kula da su, mai zai hana ni ma na kula da naki? Idan dai har kin amince da aure na, ni mai iya haɗa 'ya'yana da naki ne na kula da su In Sha Allah." Wani irin sanyi ta ji yana ratsa zuciyarta. Farin cikin da ta daɗe ba ta tsinci kanta a ciki ba yau ta ji shi. Har ba ta san lokacin da wani irin sassanyan murmushi ya suɓuce a kan fuskarta ba. A kan laɓɓanta ta furta

"Alhamdulillah." Ta buÉ—e idanunta a nutse ta kalli Alhaji Abubakar ta ce muryarta na bayyanar da farin cikin da take ciki

"Na amince. Allah Ya tabbatar da abin da yake alkhairi a gare mu." Ta ƙare maganar tana lumshe idanunta, a ranta tana fata hakan ya zame mata alkhairi, kamar yadda take fata. Ko ma wane irin hali ne da Alhaji Abubakar ɗin, idan dai har tana tare da 'ya'yanta za ta ji sauƙi. Ta kuma san In Sha Allah Allah zai taimake ta, ya taimaka mata wajen kula da rayuwar 'ya'yanta.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 08

Kusan a tare suka sauko daga cikin motar. Dukkansu fuskarsu ɗauke da annurin da ke bayyana farin cikin da suke ciki. Hidaya ce, sanye cikin doguwar rigar da ta matuƙar amsar jikinta, ta kuma haska kyakkyawar farar fuskarta mai kama da Tareeq. Gefen ta wata budurwar ce, wadda a kallan farko za ka iya kiran su da sa'anni. Ko ma kai tsaye ka kira Hidaya da babba saboda yadda ta fi Sultanah cika ido. Sai dai a zahiri Sultanah ta ba wa Hidaya kusan shekaru biyu ne, wanda a ido ba za ka taɓa faɗa ba idan dai har ba faɗa maka aka yi ba. Uwa uwa kuma yadda suke abubuwan su tare, suke komai tare, kai tsaye idan ba ka kira su da tagwaye ba, za ka kira su da sa'annin da suka fito daga gida ɗaya.

"Na yi matuƙar kewar gida." Sultanah ta faɗa tana murmushi. Ita ma Hidaya murmushin ta yi kafin ta ce

"Ki bari kawai Sisi, shi kansa gidan ya yi kewar ki." Ta ƙare dimple ɗin da ke gefen kumatunta na lotsawa. Daidai lokacin da wata babbar mace sanye cikin wata hamshaƙiyar atamfa ɗinkin bubu ta fito daga cikin motar da su Hidaya suka fito daga cikin ta. Kunnen ta kare da waya tana amsa wa. Idanunta saye cikin glass, hannunta kuma ɗauke da jakar da ke ɗore a tsintsiyar hannunta. Ba tare da ta dubi inda 'yan matan ke tsaye ba, kai tsaye ta wuce sashenta tana cigaba da amsa wayar.

"Sultanah bari na je, ki fara zuwa ki huta yanzun dai." Hidaya ta faÉ—a tana kallan Sultanah. Girgiza kai ta yi kafin ta ce

"A'ah ni kam.. Sai na fara zuwa na gaishe da Dadaji, tun da dai yanzu haka Abeey ba ya cikin gidan nan." Dariya Hidaya ta yi kana ta ce

"Toh shi kenan mu je." Daga haka suka maida akalarsu zuwa sashen kakar tasu. Daidai lokacin da Tareeq da Abokinsa Abdoul suke dab da ƙaraso wa wajen. Ƙirjin Sultanah ya buga, ta runtse idanunta tana ambaton sunan Allah. Daidai lokacin da suka ƙaraso.

"Yah Tareeq." Hidaya ta faɗa kyakkyawan murmushin nan da ke ƙara wa fuskarta kyau kamar koyaushe yana kan fuskarta.

"Da alama shi kaÉ—ai kika gani?" Abdoul ya faÉ—a yana kallan Hidaya, lokaci É—aya yana É—age girarsa. Dariya kawai ta yi tana gaishe da Abdoul É—in.

"Yah Tareeq barka da wannan lokacin." Sultanah ta faÉ—a tana jin kewar yayan nata.

"Barka sweetsis.. Kin dawo lafiya?" Jinjina kai ta yi kafin ta ce

"Eh, na yi kewar ka sosai." Ta faÉ—a kawai, dan ta so ba a gaban abokinsa ba ne, da hugging nasa za ta yi. Sassanyan murmushi ne ya tashi a kan fuskarsa kana ya amsa da

"Missed you more Sulty." Sai a lokacin sannan ta maida duban ta kan Abdoul ta gaida shi. Tun da ta masa kallo ɗaya ba ta sake bari ta kalle shi ba. Don kwata-kwata ba ta iya jure kallan nasa. Daga haka ba su ƙara mintuna masu yawa ba, Sultanah da Hidaya suka yi sashen Dadaji, ya yin da Tareeq da Abdoul suka wuce.

Tun kafin su ƙarasa shiga ta tafi a guje tana faɗin

"Dadaji tawa." Ta faÉ—a tana rungume tsohuwar da ke zaune a kan lallausan carpet É—in da ke malale a tsakiyar É—akin.

"Oh ni ɗiyar babana, yau ga Sultanah na neman karya ni." Ta ƙare tana yamutsa fuska.

"Kai Dada tsananin kewar ki da na yi ne fa." Sultanah ta ƙare tana turo baki.

"Eh dole ai ki yi kewa ta mana.. Ke ni ba wannan ba, tun da dai yanzu Allah Ya dawo mini da ke lafiya, maza tashi ki shiga kitchen."

"Kai Dadaji daga dawowa ta?" Ta ƙare tana waro ido. Taɓe baki Dadaji ta yi ba tare da ta ce komai ba. Sultanah ta sake faɗin

"Ga Hidaya nan da babu gajiyar komai a tare da ita."

"Ni! Raba ni da wannan malalaciyar." Dadaji ta ƙare tana auna wa Hidaya harara. Dariya Hidaya ta yi tana faɗin

"Toh shi kenan ki bari Sulty ta shiga tsakaninmu. Ni dai babu ruwa na." Ta ƙare tana gyara zamanta. Dariya Sultanah har ma da Dadajin suka yi jin abin da Hidaya ta faɗa.

... A ɗaya ɓangaren kuwa cikin ƙanƙanin lokaci aka tsaida ranar auren Inna-wuro da Alhaji Abubakar. Babu daɗewa Inna-wuro ta sanar da su Daneen canjin da suke ƙoƙarin samu, na barin ƙauyen gaba ɗaya zuwa can wani waje su rayu. Farin ciki kamar su taka rawa haka suka ji. Ko babu komai za su rabu da Dada. Matar da zuwa yanzun suka sake fahimtar kwata-kwata ba ta ƙaunar su, ba ta son duk wani abu da ya shafe su. Musamman ma dai Ameer da tun da abin nan ya faru ya ɗauki gaba da Dadan. Sai da Inna-wuro ta fahimci abin da ke faruwa sannan ta tsawatar masa. Shi ne ya sassauta saboda gudun ɓacin ran Innar tasu.

A ƙofar gidan ya yi parking na matarsa, kamar kodayaushe sanye cikin shadda ɗinkin babbar riga. Bai kai minti 3 da tsayuwa ba, Baffa ya fito daga cikin gidan.

"Ƙaraso ciki mana, ai yanzu ka tashi daga ɓako ka zama ɗan gida. Kwana nawa ne ya rage?" Baffa ya ƙare maganar yana murmushi. Shi ma murmushin Alhaji Abubakar ya yi kafin ya gaishe da Baffan cikin girmamawa. Ya amsa yana yin gaba don ba wa Alhaji Abubakar damar shiga gidan. Babu musu ya bi bayansa, cikin ransa yana saƙa lallai ko ma mene ne dalilin kiran nan nasa yana da matuƙar muhimmanci, tun da har aka umarce shi da shiga cikin gidan. A soro suka dakata, Baffa ya nuna masa wata tabarma ya ce

"Bismillah." Babu musu Alhaji Abubakar ya tuɓe takalmansa, ya nemi waje ya zauna bayan ya tattare babbar rigarsa. Baffa da takaimaimai bai san dalilin kiransa ba ya shiga gidan don kiran Dada. Tun kafin ya ƙaraso ta ce

"Mu je, ai na shirya ma." Ta faÉ—a tana gyara zaman gyalen da ta yafa a kanta, sai dai gaba É—aya ta kwashe shi zuwa kan kafaÉ—arta, har rigar jikinta ana gani. Babu musu ya juya, ya bi bayanta, don har ta riga shi fita.

Da mamaki shimfiɗe a kan fuskar Alhaji Abubakar yake kallan Dada, ƙwarai da gaske ya yi mamakin ganin ita ke son magana da shi. Duk da tun bayan da ya ya soma zuwa wajen Inna-wuro ya soma fahimtar halayenta. Amma duk da haka bai yi ƙasa a gwuiwa ba wajen gaishe ta cikin girmamawa.

"A'ah lafiya ƙalau Alhamdulillahi. Wallahi mun gode Allah." Ta faɗa tana gyara zama. Kafin ya ce komai ta cigaba da faɗin

"Dama abin da ya sa na kira ka.. Ba wata doguwar magana ba ce. Magana ce a kan 'ya'yan Inna-wuro da na ji ka ce za ka riƙe. Toh ka san yanzu yadda rayuwar nan ta sauya, 'yan gulma sun yi yawa. Sai a dinga gulmar ko ma dai mata biyu ka aura ne ba ɗaya ba. Toh saboda gudun hakan ya sa na ce bari na faɗa maka.. Idan har niyyar kula da su ka yi, ni ɗin nan kakarsu ce, zan iya kula da su fiye da yadda kake tunani. Idan ya so duk wata sai ka dinga yo aiken abin da za a kula da su. Ai hakan ba wani abu ba ne." Ta ƙare tana dariya gami da gyara zama. Shiru Alhaji Abubakar ya yi na tsawon wasu sakanni yana nazarin maganganun Dadar. Kafin can ya ce, bayan ya sauke ajiyar zuciya

"Babu komai Baba. Ni ma ina da 'yan matan har guda biyu, shi ya sa ma nake so na haÉ—a su waje É—aya. Hakan ba abin damuwa ba ne. Zan kula da su idan babu damuwa."

"Toh! Ikon Allah!" Dada ta faɗa a wani sheƙe tana kallan Alhaji Abubakar. Ji take kamar ta tashi ta rufe shi ta tsinannan duka ko ta ji daɗi. Sai dai kafin ta ida tsara abin da ke cikin ranta ta jiyo muryarsa yana faɗin

"Ga wannan.. Na gode sosai Allah Ya saka da alkhairi." Ya yi maganar bayan ya ajje kuɗi a gaban Dadan. Don ba tun yanzu ba ya fuskance ta, ya kuma fahimci me ye damuwarta. Sai kuwa ta fashe da murmushi tana riƙo kuɗin lokaci ɗaya tana furta

"Duka dai? Kai dai ba ka gajiya." Ta ƙare tana murmushi. Shi dai be sake cewa komai ba ya miƙe ya saka takalmansa. Ya yi sallama da Baffa ya fice daga gidan, a ransa yana cigaba da bitar kalaman Dada.
Chapter 12 · 0% Book details