← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 49

Sashe 13

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu jimawa lokacin da aka saka na biki ya zo. Ranar wata juma'a aka ɗaura auren Inna-wuro da Alhaji Abubakar. Tuni dama Inna-wuro ta ajiye sana'ar nan tata. Musamman da ya kasance a lokacin tana da kuɗin da za su yi amfani da shi wajen harkokin yau da kullum. Ga kuma Alhaji Abubakar da shi ma ba ya barin ta haka, duk da yadda take nuna ba ta so. Amma sai ya nuna mata tamkar yadda ya yi alƙawarin kula da 'ya'yanta to zai fara ne tun yanzu. Ita dai Inna-wuro sai dai ta runtse idanunta tana gode wa Sarki Allah buwaya gagara misali, wanda ya ba ta Alhaji Abubakar. Mutumin da tun kafin a yi nisa duk wasu kyawawan halayensa suka bayyana, mutumin da ya nuna ƙaunar 'ya'yanta, ya nuna zai kula da su duk da kasancewar ba shi ya haife su ba. Ita kuwa me za ta yi idan ba ta cigaba da gode wa Allah ba?.

Tana sanye cikin atamfa riga da zani, da mayafi sabbi gall. Ta yi kyau matuƙa, idan dai har ba sani ka yi ba, ba za ka ce ita ce ta ajje Daneen da Ameer ba. Sabuwar wayarta da Alhaji Abubakar ya ba ta ita ce ta shiga ƙara. Ameer da ya fi kusa da wayar ya ɗauka ya miƙa mata yana faɗin

"Inna ana kiran ki." Miƙa hannu ta yi tana faɗin

"Miƙo mini." Babu musu Ameer ya miƙa mata, ta karɓa idanunta a kan fuskar wayar don ganin mai kiran.

"Inna in haÉ—a har da wannan?" Daneen da ke haÉ—a kayanta da na Ameer ta faÉ—a tana kallan Innar. ÆŠaga kai Innar ta yi ta kalli kayan kafin ta ce

"Eh ki haɗa da shi, haɗa da wancan ma." Ta ƙarasa maganar tana mai nuni da wasu kaya cikin kayan da Daneen ɗin ke duba wa. Sai ta ɗauka kuwa ta haɗa cikin waɗanda take haɗa wa. Ya yin da ita kuma Inna-wuro ta ɗaga kiran da ake mata.

"Amarya ba kya laifi." Daga can ɓangaren Alhaji Abubakar ya faɗa yana murmushi. Duk sai ta ji kunya ta kama ta. Ta yi murmushi tana gaida shi. Amsa wa ya yi, kafin ya ɗora da

"Na san dai kina cikin gida yanzu haka. Toh idan babu damuwa ki leƙo akwai wata muhimmiyar magana da za mu yi." Haka nan kawai ta ji faɗuwar gaba ta ziyarce ta, sai dai ta basar kafin ta ce

"Toh ga ni nan." Daga haka ta katse wayar. Ta É—an yi shiru na wasu sakanni kana ta maida duban ta kan Ameer ta ce

"Ameer ka tashi ka taya Addarka shirya kayan nan, ka bar ta tun ɗazun tana yi ita ɗaya." Miƙe wa ya yi yana faɗin

"Toh Inna."

"Kafin na dawo kun gama uhmm?"

"Toh Inna sai kin dawo." Daneen ta faÉ—a har lokacin idanunta na kan kayan da take shirya wa.

Kamar yadda ya faɗa ɗin kuwa, yana ƙofar gidan, ganin ta da ya yi ya sanya shi faɗaɗa murmushin kan fuskarsa. Ya ƙaraso yana sake zolayarta. Ita dai sai babbasarwa take yi dan har ga Allah kunya yake ba ta.

"Amm.." ya faÉ—a bayan ya yi gyaran murya. Nan ma sai da ta ji gabanta ya tsinke ya faÉ—i. Ta yi saurin runtse idanunta tana ambatar sunan Allah.

"Wato Fatima tafiya ce ta taso mini bagatatan, yau yau ɗin nan zuwa Abuja ya taso mini. Yanzu ma haka ni ake jira mu wuce. Ban san da wane ido zan kalle ki in sanar da ke yau ɗin za mu wuce Abuja ne tare da ke kawai ba. Idan ya so da mun tashi dawo wa, kai tsaye nan za mu dawo mu ɗauki 'ya'yanmu mu wuce da su gida." Cikin lokaci ƙanƙani zuciyarta ta cigaba da bugawa fiye da zato. Jin da ya yi ba ta ce komai ba ne ya sanya shi faɗin

"Kar ki damu, kwata-kwata ba za mu wuce sati ɗaya a can ɗin ba. Na kuma yi miki alƙawarin daga can ɗin nan za mu wuto babu wani tsaye-tsaye." Ya ƙare a tausashe duk dan ta fahimce shi. Duk da yadda ya yi maganar tabbas ta ji ta yadda da abin da yake faɗa, sai dai ba ta san dalilin da ya sa zuciyarta ta ƙi na'am da hakan ba. Sam hankalinta ya ƙi kwanciya, ji take kamar ba za ta iya barin 'ya'yanta na tsawon sati guda cikin gidan nan bayan ba ta cikinsa ba. Sam ta kasa gane dalilin hakan. Ga kuma faɗuwar gaban da ta ƙi barin ta har zuwa yanzun.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 09

Jin da ya yi ta yi shiru na fiye da tsawon minti É—aya, ya sanya shi gyara tsayuwarsa ya ce a tausashe

"Ki yi haƙuri, kar ki ce ban yi miki adalci ba. Ban san wannan tafiyar za ta taso ba, ina mai sake ba ki haƙuri." Kalmar haƙurin da yake ta maimaitawa tabbas ta yi matuƙar tasiri a zuciyarta, sai dai duk da haka, ba ta dena jin bugun zuciyar ba. Ta yi ƙarfin halin buɗe baki da ƙyar ta ce

"Babu komai, Allah Ya sa haka ne mafi alkhairi." Sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce

"Ameen, na gode."

Shiru ne ya wanzu a wajen na tsawon mintuna, zuwa can Alhaji Abubakar ya ce

"Bari na jira ki sai ki shirya koh? Kafin nan mun yi magana da Baffa." Da kai ta amsa masa maganar, ba ta sake cewa komai ba ta faɗa cikin gidan tana tunanin ta inda za ta fara sanar wa da 'ya'yanta tafiyar sati da za ta yi ta bar su cikin gidan. Kamar yadda ta umarci Ameer kuwa, yanzu haka tare da Daneen ta same su suna shirya kayansu cikin jaka. Ya yin da ragowar da ba za su ɗauka ba suna ninkewa suna mayar da su wajen kayansu. Ƙarasawa cikin ɗakin ta yi jikinta a matuƙar sanyaye ta nemi waje ta zauna tana cigaba da kallan su.

"Inna mun gana haɗawa fa." Ameer ya faɗa yana murmushi. Ji yake tamkar ya yi ta tsalle saboda farin ciki, don zai iya cewa kaff cikin su ya fi su farin ciki da barin ƙauyen nan da za su yi. Murmushin yaƙe Inna-wuro ta yi kafin ta ce

"Ku zo ku zauna ku ji." Kusan a tare Ameer da Daneen suka ɗaga ido suka kalli Innar tasu jin yadda maganarta ta sauya cikin ƙanƙanin lokaci. Wannan ɗin ba sabon abu ba ne a wajen su, fahimtar halin da ɗaya daga cikin su ke ciki ko da ta magana ne kuwa, ba tare da ya sanar da su ba. Ajiye Hijab ɗin da ke hannunta Daneen ta yi, ta ƙarasa gaban Innar tasu da sauri ta zauna, ya yin da Ameer ma ya zauna a gefen ta, gaba ɗayan su jiki a sanyaye.

"Ku buɗe kunne da kyau ku saurare ni, ba don na so ba sai don haka Allah Ya tsara, zan bar ku cikin gidan nan na tsawon sati guda. Kai tsaye nan za mu dawo mu ɗauke ku mu wuce da ku inda za mu zauna. Kar ku damu, kar ku ɗaga hankalinku." Ta ƙare maganar a nutse, duk da ita ma ba ta da nutsuwar zuciya, sai don kawai ta ba wa 'ya'yan nata ƙwarin gwuiwa.

"Inna.." Shi ne abin da Ameer ya yi ƙarfin halin faɗi yana cigaba da kallan Innar. Wata ƙwalla da ta ji ta taho mata ita ce ta sanya ta saurin saukar da kanta ƙasa, wajen sakanni 30 kafin ta ɗago tana kallan su su duka. Ta kamo hannayensu ta sanya cikin nata.

"Ba mu taɓa rabuwa ba tun da muke, sai ga shi yau ɗin za mu rabu na tsahon kwana bakwai. Ina so na yi amfani da wannan damar wajen neman alfarmar yin haƙuri da zama da Dada cikin gidan nan bayan ba na cikinsa. Akwai kuɗi a cikin jakata, duk abin da kuke buƙata ku yi amfani da shi. Daneen ga Ameer nan, ki kula mini da shi har na dawo. Ameer ga Daneen nan ka kula mini da ita har na dawo. Allah Ya yi muku albarka, Ya albarkaci rayuwarku, Ya raya mini ku." I zuwa lokacin gaba ɗaya jikinsu ya yi sanyin da suka kasa amsa addu'ar Innar. Kowanne da abin da yake saƙa wa a cikin ransa.

"Kar ku mini kuka." Inna ta faɗa tana girgiza kai lokaci ɗaya tana kallan su duk da ita ma nata idanun cike suke da ƙwalla.

"Toh maza ki fito Hajjaju ta ɗaka, mijinki na jiran ki. Ko kuwa ƙaramar yarinya ce ke da sai an zo an rarrashe ki kafin ki fito." Ta jiyo muryar Dada na faɗin hakan. Hannu ta kai ta goge fuskarta da zuwa lokacin hawaye sun fara sauka, ta yi saurin ɗauke su don kar ta sake karyar wa da 'ya'yanta zuciya.

"Toh gani nan." Ta ɗaga murya wajen faɗar hakan, don Dadar ta ji. A hankali ta miƙe har lokacin hannunta na cikin na 'ya'yanta da suka kasa furta komai.

"Ku yi haƙuri kar da ku karya mini zuciya. Ba na tafi kenan ba, nan da sati ɗaya zan dawo in ɗauke ku da yardar Allah."

"Inna don Allah kar ki tafi." Daneen ta faÉ—a da muryarta da ke rawa, lokaci É—aya tana rungume Innar. Kukan da Inna ta ji ta fashe da shi shi ne ya sanya ta runtse idanunta, ta saka hannu ta ja Ameer jikinta, ta haÉ—a su ta rungume waje É—aya. Sun kai wajen minti biyu a haka kafin suka saki juna. Inna-wuro ta saka hannu ta É—auki jakar kayanta. Bin bayanta suka yi har zuwa tsakar gidan. Kafin su kai ga fita daga cikin gidan wata da take kusa da Dada ta ce

"Wai dama ba a nan za ta zauna ba."

"A'ah nan cikin Kano ne fa za ta zauna." In ji Dada tana gyara zama lokacin da Inna-wuro ta nemi waje ta zauna. Ba wata addu'a daga Dadar har Baffan suka yi mata ba, haka dai ta ja ƙafafunta suka fice daga gidan. A sanyaye su Daneen suka gaishe da Alhaji Abubakar, ya amsa cikin sakin fuska kafin ya karɓi jakar hannun Inna-wuro ya saka cikin mota.
Chapter 13 · 0% Book details