← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 49

Sashe 14

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"A kula, Allah Ya tsare mini ku, sai na dawo." Inna ta faÉ—a tana kallan su.

"Allah Ya tsare Inna." Suka haɗa baki wajen faɗar hakan. Ta lumshe idanunta tana juya wa a hankali ta soma tafiya zuwa wajen motar. Dab da za ta ƙarasa, ta sake juya wa ta kalli 'ya'yan nata. Sai ta juya da sauri ta shige cikin motar, saboda yadda ta ji a yanzun ba za ta iya jurewa ba, zuciyarta ta gama karyewa. Ƙarasawa Alhaji Abubakar ya yi ya shiga motar, bayan wasu sakanni ya tashi motar. Ƙasa da kanta Inna-wuro ta yi don tabbas idan ta cigaba da kallan 'ya'yanta za ta iya bijire wa umarnin mijinta ta ƙi binsa ta cigaba da zama da su. Don haka har ya soma tafiya ba ta ɗaga kanta ba. Daneen da Ameer, suka cigaba da bin motar da kallo, har zuwa lokacin da ta ɓace wa ganin su. Hannun Ameer Daneen ta kama ta riƙe sosai tana runtse idanunta. Wani irin bugu zuciyarta take yi. A hankali kuma sai ta soma takawa zuwa cikin gidan, ya yin da Ameer ya rufa mata baya.

Bin su da kallo Dada ta yi lokacin da ta ga shigowar su cikin gidan. Ta taɓe baki tana jinjina kanta. Ita dama burinta bai wuce a bar mata 'ya'yan Inna-wuro a wajenta ba, ko babu komai ta san za su dinga zuwa a kai a kai ana ajiye mata kuɗi da sauran su. Amma idan suka tafi da 'ya'yan suka manta da ita da wa ta ɓare kenan? Bar mata su da aka yi yana nufin samun wata mafitar kafin su dawo, wadda za ta hana su tafiya da su duk da sun yi niyya.

Kai tsaye ɗakinsu suka nufa suka yi shiru kowa da abin da yake saƙa wa. Ranar haka suka wuni kamar masu zaman makoki, babu wanda ke cewa da ɗan'uwansa ko uffan ne.

Washegari jiki a sanyaye duk suka farka, sai suke jin su wasu daban, ba su taɓa farkawa ba su ga Innarsu ba sai a yau ɗin. Ba su taɓa rabuwa da Innarsu ba sai a wannan karon. Suna ta farin ciki abin farin ciki ya same su, ashe ba su sani ba kafin samuwar farin cikin sai sun soma rayuwar kaɗaici. Da yake ranar babu makaranta ya sanya suna gida, tun safe bayan sun fito daga ɗaki ba su koma ba. Shi Ameer yana can aiken da Dada ke ta masa, da kuma wasu ayyukan. Ya yin da Daneen ke yi wa Dada girki da sauran ayyukan cikin gida.

.. "Me kake yi haka ne Ameer?" Daneen ta faɗa tana kallan Ameer da ke cusa kayan sakawarsa cikin jakar islamiyya. Sai da ya ƙarasa cusa wadda ya ɗakko sannan ya ɗaga ido ya kalle ta ya ce

"Inna zan bi." Da mamaki matuƙa Daneen ke kallansa idanunta a waje. Cike da mamakin dai ta ce

"Inna kuma Ameer? Ka san inda ta je ne?" Jinjina kai ya yi kana ya ce

"Ehh, jiya na ji Dada tana faɗa wa ƙawarta wai sunan garin Kano. Ko ban san gidan ba, na san muna zuwa muka tambayi Mai gari gidan Alhaji Abubakar ya sani. Tunda kin ga mu ma a garin nan gidan waye Mai gari bai sani ba?"

"Ni yi mini shiru dallah.. Tashi ka tafi toh." Daneen ta faɗa tana shirin miƙe wa. Maida ta ya yi ta zauna ta hanyar riƙo hannunta. Ya shiga girgiza kai yana faɗin

"Kar ki mini haka Addata. Idan har ke ba ki amince mini ba waye zai amince mini? Don Allah ki duba abin da na faÉ—a ki bari mu tafi. Ni ba zan iya cigaba da zama da Dada ba wallahi. Ko ba ki amince na bar garin nan ba, toh zan bar cikin gidan nan in tafi ko ma ina ne."

"Wai Ameer ba ka da hankali?" Daneen ta faÉ—a tana kallan sa a tsorace.

"Toh ki yarda da abin da na faÉ—a."

"Ba zan yarda ba." Ta faÉ—a tana jefa masa harara.

"Don Allah Addaneen tawa ni kaɗai. Don Allah.." Ya ƙare a marairaice. Sai a lokacin sannan ta sake juyawa ta kalle shi sosai ta ce a hankali kamar me raɗa.

"Ameer wai da gaske kake?" Jinjina kai ya shiga yi lokaci É—aya yana furta

"Wallahi da gaske Adda. Ji nake kamar ana azalzalata da in bar gidan nan, ki taimaka ki amince mu bi Inna garin da ta je." Shiru Daneen ta yi na tsawon wasu mintuna. Rashin yawan tazarar shekarun da ke tsakaninta da Ameer ya sanya wayonsu kusan É—aya ne. Wani lokacin ma har ya fita wayo. Don idan ya yi wani abun sai ka É—auka shi ne babba, sai kuma wani lokacin ko ba a faÉ—a maka ba za ka fahimci Daneen ce babba.

"Amma idan Inna ta yi faÉ—a fa? Tun da ka ga ta ce nan da sati É—aya za ta zo ta É—auke mu."

"Ba za ta yi ba Adda, ba za ta yi ba. Shi ma kuma sabon Abban ai yana da mutunci. Sai mu ce zuwa muka yi mu gaishe su." Shiru Daneen ta yi na tsawon wasu mintuna kafin ta shiga jinjina kai ta ce

"Toh." Ta ƙare tana ajje numfashi.

"Yawwah Addata." Ameer ya faɗa yana murmushi. Cikin zuciyarsa yana jin wani shahararren farin ciki na kama shi. Da gaske har cikin ransa ji yake tamkar ana azalzalarsa da barin gidan. Kuma da gaske yadda ya faɗa ɗin tabbas da Addar tasa ba ta amince da bin Innarsu ba, yau ba zai kwana cikin gida ɗaya da Dada ba. Shi da kansa ya tashi ya ɗauki jakar islamiyyar Daneen ya shiga saka mata kayan sakawarta ciki. Ya samu dama da yawa kuwa sun shiga saboda yadda yake cusa su don ma kar a gane meye a ciki. Sai da suka gama tsaff, kafin ya miƙe ya ce

"Adda riƙe jakarki mu tafi." Babu musu ta karɓa ta rataya ta cikin hijabin makarantar islamiyya da ta saka. Shi ma ya rataya tasa jakar saman uniform ɗin islamiyyar. Ba tare da tunanin komai ba suka fito daga cikin ɗakin. Dada na zaune tana jin Radio a kan tabarma, ya yin da Baffa ke mata fifita yana daga gefen ta.

"Dada, Baffa mun tafi." Daneen ta faÉ—a, don tana da tabbacin idan ba ta faÉ—a ba Ameer ba zai faÉ—a ba. ÆŠaga idanunta Dada ta yi ta kalle su, Radion da take ji ya sa ba ta iya tantance iya Daneen ce kaÉ—ai ta mata magana ba. Tsaki ta ja kafin ta soma faÉ—in

"Ni fa makarantar ma na gaji da ganin ku kuna zuwan ta wallahi. Haba." Ta ƙare yanzu kuma tana sakin ƙwafa.

"Kin ga ƙyale su su tafi, kar shirin nan ya wuce ki. Idan kin gama ji in ya so duk hukuncin da za ki yanke sai ki yanke kafin su dawo." Baffa da ke cigaba da firfitarsa ya faɗa yana kallan ta. Shiru ta yi na tsawon wasu sakanni kafin cikin na'am da zancen nasa ta ce

"Haka ne kuma.. Ku tashi ku tafi." Tun kafin ta ida faɗa har Ameer ya miƙe, kafin ka ce mene wannan ya fice daga cikin gidan. Ta ja ƙwafa tana cije gefen leɓenta, a ranta tana saƙa yadda za ta yi maganin yaron cikin ƙanƙanin lokaci.

"Kin gani ko Adda? Kin ga abin da nake faɗa miki koh? Kin ji fa wai makarantar ma hana mu zuwa za ta yi, toh me ya sa?" Ya ƙare tambayar yana kallan Daneen da ta sauke ajiyar zuciya saboda ganin da ta yi Dada ba ta gane kaya ne a cikin jakunkunansu ba. Jinjina kai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Cigaba da tafiya suka yi, sai da suka yi tafiya mai nisa kafin suka isa wani titi. A nan suka samu motar da za ta fitar da su inda za su samu motar da za ta kai su Kano. Da kuɗin da Inna ta ba su suka yi amfani wajen biyan mai motar kuɗinsa lokacin da ya sauke su. Sai suka sake tarar wata motar wadda ita ma dai ba Kanon direct za ta wuce ba. Don haka bayan ta sauke su a nan suka yi tambaya suka samu motar da za ta wuce Kano. Cikin matuƙar farin ciki suka hau motar. Motar da ba ta kai ga cika ba, don haka aka tsaya ana jiran wasu passengers ɗin kafin motar ta tashi.

"Adda yunwa nake ji." Ameer ya faɗa yana ɓata rai. Hannu ta saka ta karɓi jakar hannunsa, ta ce tana kallan waje

"Ka ga wata mai siyar da awara can, je ka siya ka ci." Ta faɗa tana zaro kuɗi a jakar Inna ta miƙa masa. Hannu ya saka ya karɓa yana sauka daga motar, kai tsaye wajen mai awarar ya wuce. Ta bi shi da kallo tana lumshe idanunta, daidai lokacin da bugun da numfashinta ke yi ya cigaba da fita a gurguje kamar wadda ta yi tsere. Bayan wasu mintuna sai ga shi ya dawo. Yana dawowa kuma, motar na gama cika. Don haka bai daɗe da zama ba, motar ta tashi aka soma tafiya.
Chapter 14 · 0% Book details