Sashe 8
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
... Tura ƙofar ɗakin ta yi, cikin sa'a kuwa sai gashi ta buɗe. Ta sauke ajiyar zuciya tana saka kanta cikin ɗakin da sallama ɗauke a bakinta. Yana zaune a kan haɗaɗɗiyar kujerar da ke cikin palourn, sanye cikin ƙananan kaya da suka matuƙar yi wa jikinsa kyau. Laptop ce gabansa yana dannawa cikin ƙwarewa, gaba ɗaya fararen idanunsa na kai, da alama wani aikin yake mai matuƙar muhimmanci. Duk da kusan duk hankalinsa na kan laptop ɗin, hakan be hana shi jin lokacin da aka turo ƙofar ba. Ya ɗaga manyan fararen idanunsa ya kalli ƙofar a nutse. Daidai lokacin da Hidaya ta ƙarasa shigowa cikin ɗakin, kamar koyaushe babu abin da ke tashi sai sassanyan ƙamshin jikinsa da kuma na cikin ɗakin. Wanda suka cakuɗu suke bayar da ƙamshi me daɗin gaske. Rufe laptop ɗin ya yi kafin sassanyan murmushin da ya ƙawata fuskarsa ya bayyana a kan laɓɓansa. Sai dai yadda tsagoron kyawunsa ya sake bayyana, ga duk wanda ya kalle shi zai so a ce ya zauna a hakan ne ko da yaushe. Ita ma murmushin Hidaya ta yi tana ƙarasawa ta nemi gefensa ta zauna ta ce a narke
"Kai Yah Tareeq, da ma ka gama fushin amma shi ne ba ka nemi kowa ba?" Kallan ta ya yi, kafin cikin er basarwa ya ce
"Ni na faɗa miki ina fushi?" Ya ƙare kamar da gasken ba shi ne ya yi mugun fushi jiya ba. Sanin halinsa ya sanya ta yin murmushi kafin ta ce
"Yah Tareeq.."
"Uhmmm." Ya amsa yana É—aukar wayarsa da ke ajje a gefen sa. Daidai lokacin da Hidaya ke faÉ—in
"Yaya tun jiya duka gida sun damu da ganin ka, ni ma kasa jurewa na yi shi ya sa na sake zuwa in duba ka. Please ka je ko za su ji daɗi." Jinjina kai ya yi, har lokacin idanunsa na kan waya. Miƙewa Hidaya ta yi ta ce a nutse
"Bari na je Yaya, na ga kamar aiki kake yi." Sai a lokacin ya É—aga idanunsa a nutse ya kalle ta. Ya É—an lumshe idanunsa kafin ya buÉ—e, ya buÉ—e bakinsa kamar wanda ba ya son yin maganar ya ce
"Olright, take care of ur self soulsis. Zan shigo zuwa an jima In Sha Allah." Ya ƙare da ɗan gajeren murmushin nan nasa da ya kasance na dabi'a. Yana matuƙar ƙaunar er uwar tasa, kasancewar ta mace ta farko da ta fi kowa damuwa da damuwarsa, ta fi kowa fahimtar sa idan yana cikin damuwa. Ta fi kowa shiga damuwa idan ta gan shi cikin rashin walwala. Shi ya sa duk lokacin da take kusa da shi, ya kan yi ƙoƙari wajen wanzar da murmushi ko da kuwa yana da damuwa don kar ma ta fi shi shiga damuwa.
"In Sha Allah Yaya. Amma don Allah ka cire Diyana a ranka, ka manta da rayuwarta.." Hannu ya ɗaga mata alamar ta dakata kar ta ƙarasa maganar da ta fara. Tuni annurin fuskarsa ya ɗauke. Shi haka rayuwarsa take, idan dai har ya bar abu toh ya bar shi har abada. Shi ya sa ma ba ya saurin yanke hukunci har sai ya tabbatar da abu. Ganin tana shirin ɓata masa rai ne ya sanya ta faɗin
"Don Allah Yaya ka yi haƙuri.." Ta faɗa tana kama kunnenta. Ɗan sauke gajeriyar ajiyar zuciya ya yi kamin ya ce bayan ya ƙaƙalo murmushi a kan fuskarsa
"Kar ki ƙara." Girgiza kai ta yi tana faɗin
"Ba ma zan ƙara ba har abada." Ta ƙare tana murmushi. Daga haka ta yi sallama da shi ta fice daga ɗakin. Ya ja laptop ɗin gabansa ya cigaba da abin da yake yi a ciki.
.. Sanye take cikin doguwar rigar atamfa mai matsakaicin kyau, tana sanye da hijabi dogo wanda ya wuce gwuiwarta. Tafiya suke yi tare ita da wani É—an saurayi wanda kusan tsayin su É—aya, sai dai kasancewar namiji ya sa ya fita tsayi. Jefi-jefi su kan É—an yi magana, har zuwa lokacin da Ameer da ya kalli Daneen ya ce
"Adda wai kin ma san wani abu kuwa?" Girgiza kai ta yi tana É—aga manyan fararen idanunta ta kalle shi sannan ta ce
"A'ah." Ta yi maganar tana cigaba da tafiya.
A haka idan ka kalle su za ka iya cewa Ameer ne babba, sai dai nutsuwa da yanayin yadda Daneen ke abubuwanta da suka wuce na shekarunta, ya sa ake gane ita ce babba. Kyawun nan da ta taso da shi tun yarinta, har yanzu babu abin da ya ragu. Sai ma ƙaruwa da ya yi, ta ƙara zama wata irin kyakykyawa, don kaff rigarsu tana sawun farko cikin kyawawan 'yan matan ƙauyen. Idanunta manya ne, kamar yadda tun yarinta suke, sai dai yanzu asalin kyawunsu, da kuma yadda suke a halitta sun ƙara bayyana. Tamkar idanun mage haka suke, masu kyau da kuma ɗaukar hankali. Wani irin shape na da su na musamman, wanda ko iya kyawun idanunta aka tsaya an gama tashi. Siririn hanci gare ta, wanda ta gado shi daga wajen Inna-wuro. Don ko kaɗan, daga ita har Ameer ba su ɗauko ko abu ɗaya daga wajen Alhaji Baita ba. Bakinta kuwa ƙanƙantarsa kaɗan ne ya ƙaru tun yarinta. Haka yake ɗass a bakinta, ja ne matuƙa, irin jan nan mai ɗaukar hankali. Don sau da dama idan ta je makaranta a kan ce sai ta goge jan bakin da ta shafa a bakinta kafin ta shiga aji. Idan ta ce ba ta shafa ba, wasu ba sa yarda, har sai ta saka gefen hijab ɗinta ta goge bakin nata, sai dai maimakon janbakin da suke iƙrarin ta shafa ya fita, sai bakin ya sake ɗaukar ja saboda gurje shin da ta yi. Duk wani abu da ake buƙata a jikin kyakykyawar mace Allah Ya ba wa Daneen. Ƙarancin shekarunta ba su nuna wa a jikinta saboda tarin nutsuwa da take da ita. Sai dai idan fuskarta ka kalla shi ne za ka gano zallar yarintar da ke tattare da ita. Sanyi ne da ita tamkar me, ba ta da hayaniya ko kaɗan. Ko da kuwa a cikin jama'a ne, za ka same ta shiru babu hayaniya, idan dai har ba tare da rabin jikinta Ameer take ba, toh shi ne za ka ji bakinta sosai. Shi ma Ameer kyakykyawa ne, don kamar su ɗaya ma da Daneen ɗin, sai dai duk kyawunsa ta fishi, musamman kuma don kasancewarta mace.
"Mutumin nan fa yau ma sai da ya." Tun kafin ya ƙarasa ta katse shi da faɗin
"Kaa ga Ameer na faɗa maka ka fita harkar wanda ba ka sani ba koh? Wallahi ba ka jin magana." Ta ƙare maganar tana hararar sa. Dariya ya yi, yana so ya ga Daneen ɗin na masa faɗa, sam ba ma ta iya haɗe ran ba. Kuma ma wani idan ya gan su tana masa faɗan zata zai yi rashin kunya take yi wa yayanta. Tun da dai a tsaye ya fita girma, dan ma dai ba shi da ƙiba ne, haka yake siriri sai tsayi.
"Toh Adda na dena." Ya faɗa daidai lokacin da suka iso ƙofar gida. Da sallama suka shiga cikin gidan, Dada na zaune kan kujera tana cin gyaɗa marau, ya yin da Baffa ke zaune kan tabarma yana saurarar Radio. Dukansu girma ya bayyana sosai a jikinsu, sun sake zama dattijai matuƙa. Tun da suka shigo gidan sai suka kama kan su, don sanin halin masu gidan.
"Baffa barka da wannan lokacin, Dada barka da wannan lokacin." Suka haÉ—a baki wajen faÉ—ar hakan. Ba tare da sun jira jin cewar wani daga cikin su ba suka wuce É—akinsu, É—akin da yanzu Inna-wuro ta yi masa dabara ta samu ta fitar wa da Ameer inda yake kwana. Don sun san in dai Dada ce ba amsa wa za ta yi ba, shi kuma Baffa ko ya yi niyya idanun Dada ba za su bar shi ya amsa ba.
"Sai da na ce miki mu tafi wajen Inna ba ta dawo ba, ni na ji hakan a jikina." Ameer ya faÉ—a lokacin da suka gama shiga É—akin nasu babu Inna-wuro a ciki. Ita ma Daneen É—in tura mitsitsin bakinta gaba ta yi kafin ta ce
"Allah na É—auka ta dawo fa."
"Toh mu koma mana." In ji Ameer. Girgiza kai ta yi ta ce
"Dada na tsakar gida shi ne za mu fita, chaɓɓ.. Ba inda za mu je." Ta ƙarasa maganar tana neman waje ta zauna.
"Kai Adda."
"Na gama magana." Ta faÉ—a tana jefa masa harara.
"An gama The Babbar Yaya." Ya ƙarashe maganar yana dariya. Shi ma neman waje ya yi ya zauna, sai suka shiga bitar littafan makaranta. Don ko a makarantar ma ajinsu ɗaya har islamiyya. Sai dai ko minti 10 ba su yi ba muryar Dada da ta ke magana cikin ɗaga murya ta katse su.
"Ina waje ina aiki kuna cikin É—aki koh? Toh ku fito kai ka je mini gonar Habule ka tsinko mini zogale. Ke kuma ki zo ki je ki É—ebo mini ruwa..
Za ku fito ne ko sai na ci uwarku." Ambatar sunan uwar da ta yi ya sanya duk jikinsu ya yi sanyi, ɓacin rai ya taso wa Ameer da yake ya fi Daneen zuciya. Shi idan ta shi ne in da ubansu ta ce toh da sauƙi. Tun da dai be san waye uban nasu ba, abu ɗaya ya sani kawai duk lokacin da suka yi wa Inna-wuro zancen wani abu da ya shafi mahaifinsu ranta kan ɓaci. Wannan dalili ne ya sa suka jefar da maganar tasa gefe suka dena yi. Girman mahaifiyarsu na ƙaruwa a zuciyarsu, domin su a wajen su ita ce uwa, kuma ubansu. Miƙewa Daneen ta yi, ganin Ameer be ko da motsawa ba ne ya sanya ta faɗin
"Ameer tashi mu je."
"Ni ba inda zan je." Ya faÉ—a yana É—auke kai. Hannunta ta kai ta dafa kafaÉ—arsa a sanyaye ta ce