← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 49

Sashe 7

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Waye ya ce maka ba ta son ku?" Ta tambaya a sanyaye. Ɗan ƙaramin bakinsa ya buɗe ze yi magana, sai kuma ya juya ya kalli Daneen da ke zaune suna kallan juna. Dara-daran idanunta farare ƙall ta ɗaga ta zuba wa Ameer ɗin su tana jira ta ji me ze ce. Ganin yana shirin buɗe baki ya yi magana ya sanya ta soma girgiza masa kanta, ƙasa-ƙasa da siririyar muryarta mai daɗin saurara take faɗin

"Inna ba ni ce ba."

"Adda Neen." Ya faɗa yana nuna ta, lokacin da ya turo bakinsa. Don babu yadda ze yi, ba ya so Innar ta kama shi da laifi kwata-kwata musamman da ya ga ranta ya ɓaci. Sai dai in da a waje ne, ko ma wane irin laifi Adda Neen ɗin tasa za ta yi ya gwammace ya ɗauki laifin. Shi ya sa sau da dama ko a makaranta sai dai a yi faɗa da shi ba dai da Daneen ba. Don kuwa zama yake tamkar shi ne yayan ita kuma ƙanwar. Maida duban ta Inna-wuro ta yi kan Daneen da ta yi rau-rau da idanunta kamar me shirin saka kuka, ta buɗe baki za ta yi magana Daneen ta ɗaga yatsanta guda ɗaya ta kai saitin bakinta tana faɗin

"Inna na rantse ba haka ba ne." Dariya ta ba ta, don haka ta sanya hannu ta janye hannun tana faÉ—in

"Ya isa haka, kar na sake jin wani a cikin ku ya ce haka. Dada tana son ku sosai Uhmm?" Jinjina kai kawai suka yi suna murmushi.

"Ya yi kyau. Abin da nake so da ku kawai ku dage ku yi karatu, ina so ku zama wasu, ku zama waÉ—anda kullum zan din ga alfahari da su."

"Inna da ma muna ƙoƙari ai ko?" Ameer ya faɗa yana murmushi.

"Kuma dai na fi Ameer ƙoƙari." Daneen ta faɗa tana rausayar da kai, sassanyan murmushi na fita daga kyakykyawar fuskarta.

Haka suke yini cikin farin ciki idan suna tare, sai dai daga zarar sun koma gida sai farin cikin ya gushe, musamman idan halin Dadan ya motsa. Haka za su yi gum a É—aki ta yi ta jarabarta ita kaÉ—ai. Idan Inna-wuro ta tanka ta ce za ta mata rashin kunya. Idan kuma ta yi shiru ta ce ta maida ta mahaukaciya tana magana ta mata shiru. Wannan dalilin ne yake sanya Inna-wuro kasa sanin takamaimai abin da za ta yi. Sai kawai ta haÉ—a kan 'ya'yanta ta rungume cikin rashin sanin abin yi.

Wannan kenan.

*** *** ***

__ Ƙaton palour ne da ya amsa sunansa palour. Haɗaɗɗe, me ɗauke da zafafan kujeru masu ɗaukar hankali, kyau da nutsuwa. Ƙatuwar T.V ɗin da ke gefe, inda take zaune a tsare babu hayaniya ce ke ta aiki. Sai dai ga dukkan alamu babu wanda ya damu da abin da ake haska wa a ciki. Wata dattijuwar mata ce zaune a kan ɗaya daga cikin lausasan kujerun da ke zagaye da ɗakin, ƙafarta ajje a kan wani tattausan pillow, wata matashiyar budurwa na matsa mata ƙafar. Can gefe kuma wata kyakykyawar mata ce zaune, sanye cikin atamfa doguwar riga ɗinkin kaftan, ta yi ɗauri wanda ya dace da shekarunta. Har bayan wajen mintuna biyar babu wanda ya ce ko uffan. Zuwa can wata matashiyar budurwa ta shigo cikin ɗakin da sallama ɗauke a bakinta. Hannunta ɗauke da tsadaddiyar wayarta, tana sanye cikin wata doguwar riga da ta matuƙar karɓar jikinta. Neman waje ta yi ta zauna gefen wannan dattijuwar fuska a narke tana kallanta. Girgiza kai dattijuwar ta yi kafin ta ce

"Toh.. za a yaudare ni ne?" Ta ƙare tana taɓe baki. Turo baki matashiyar ta yi kafin ta ce

"Babu wata yaudara fa Dadaji. Allah kuwa magana na zo mu yi da ke mai muhimmanci." Jin hakan ya sanya wadda ke yi wa dattijuwar tausa miƙewa, don ba hurumin su ba ne jin wata maganar da ta shafi 'yan gidan. Don haka ta ce cikin girmamawa.

"RankiyadaÉ—e bari na je." Amsa mata Dadaji ta yi tana maida dubanta kan Hidaya ta ce

"Me kuma ya faru?"

"Dadaji har zuwa yanzu fa Yah Tareeq bai fito ba. Na yi wa Maama magana ta ce na bar shi zuwa an jima, na kikkira wayarsa ya ƙi daga wa kuma Aminu ya tabbatar mini da ya ga shigowarsa cikin gidan nan, ni kuma na kasa haƙuri."

"Oh ni 'yar nan. Toh ni kuma meye nawa a ciki Hidaya? Ke É—in da kuke É—asawa ma da shi bai É—aga kiranki ba me zan yi masa? Da ma ya aka cika ballantana kuma wani abu ya faru? Ni kam ban san me zan masa ba kuma." Dadaji ta faÉ—a.

"Kai don Allah.. Wallahi dai ya kamata a tausaya wa Yaya.. Ni fa ina tsoro wallahi, kin dai san shi da saka abu a rai. Maama don Allah ki saka baki kin ji?" Ta ƙare maganar tana juyawa ta kalli ɗayar matar da ke cikin ɗakin.

"Hidaya na faɗa miki ki bar shi yana buƙatar kaɗaici koh?" Maama ta faɗa tana kallan Hidayar.

"Ah toh." Dadaji ta faÉ—a tana jinjina kai. Jiki a sanyaye Hidaya ta ce

"Tohm." Daga haka ta miƙe ta wuce ɗakinta, har lokacin tana sake kiran number Yayan nata amma be ɗaga ba.

... Bayan tsawon mintuna masu yawa da ya kwashe a toilet ɗin, inda ya sakar wa kansa ruwa me sanyi. Ɗaure da towel a ƙugunsa ya fito daga toilet ɗin. Nannaɗaɗɗen gashin kansa jiƙe sharkaf da ruwan da ya daɗe a cikinsa. Farar fatarsa ita ce ta tona asirin baƙar gargasar da ke jikin gaɓɓai da yawa na jikinsa. Musamman ma dai ƙirjinsa zuwa kan hannunsa, wadda duk da yadda take a jiƙe hakan be hana ta miƙewa ba. Be yi tunanin duk daɗewar da ya yi cikin ruwan nan zai cigaba da jin ɓacin rai ba. Sai dai yadda zuciyarsa ke tafasa, tana sake yin zafi ya sa hatta numfashinsa yake fita da sauri. Tsigar jikinsa har lokacin ta ƙi dena tashi, wadda ita ta taimaka wa gargasar jikinsa wajen ƙin lafe wa a kan faffaɗan ƙirjinsa. Cikin takun nutsuwa ya ƙarasa bakin mirror ya tsaya, daidai lokacin da kyakykyawar fuskarsa ma'abociyar wani sassanyan kyau ta bayyana. Kyakykyawa ne na gani na faɗa, irin kyan nan me ruɗar da duk wanda ya yi tozali da shi. Fari irin farin nan me mugun kyau, wanda ƙasumbar da ke zaune ras a kan fuskarsa ta ƙara ƙawata kyawunsa da kuma farin nasa. Wasu idanu ne da shi na musamman, farare masu ɗauke da baƙa wuluk ɗin ƙwayar ido. Ɗan ƙaramin baki ne da shi tamkar wata mace, ja kamar wanda ke shafa wani abun. Yadda kwantacciyar ƙasumbar fuskarsa ta zagaye fuskarsa har tana ƙoƙarin rufe mitsitsin kyakykyawan laɓɓansa. Hannunsa ya kai ya ɗan shafa saman girarsa idanunsa a lumshe yana ɗan fidda numfashi a hankali ko zai samu ɓacin ran da yake ji ya tafi, ya manta da abin da ya faru, ya ɗauka ya jefa shi cikin kwandon sharan abubuwa mara sa amfani, amma ya kasa, ya kasa kwata-kwata. Daidai lokacin wayarsa da ke yashe a kan gado ta ɗauki ƙara. Be ko motsa ba, ballanta ya yi yunƙurin ɗaukar wayar. Wani kiran ne ya sake shigo wa bayan wancan ya tsinke. Duk da ba a ɗaga ba, hakan be sa an dena kira ba, ya lumshe idanunsa yana jan ƙaramin tsaki, sabon ɓacin rai na taso masa. A nutse ya juya ya ƙarasa kan gadon ya ɗauki wayar, yana shirin kashe ta gaba ɗaya sabon kira ya sake shigo wa. Ya dafe kansa da yatsu biyu kafin ya kalli me kiran nasa. Sauke ajiyar zuciya ya yi har lokacin kyawawan idanunsa ɗore a kan wayar. Dab da za ta tsinke ya ɗauka. Daga can ɓangaren aka ce

"Tareeq.. Me ya sa za ka yi haka ne?" Ya faɗa a gajiye. Maida wayar ya yi ya riƙe da ɗayan hannunsa kafin ya gyara tsayuwarsa, kafin ya kai ga cewa komai aka sake faɗin

"Don Allah ka fito. Wallahi ka ɗaga mini hankali." Ya faɗa dan ya san halin abokin nasa da saka abu a zuciya, ƙaramin abu ma idan ya saka a zuciyarsa an banu, ballantana wannan lamari da dukkanin su babu wanda ya taɓa tunanin hakan za ta iya faruwa.

"Abdoul don Allah ka ƙyale ni, zuciyata na buƙatar hutu, idan har ba so kuke ta tarwatse ba." Ya ƙarasa maganar a gajiye, yana fesar da wani huci da ya fito tun daga ƙasan zuciyarsa.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 05

__ "Tareeq!" Abdoul ya faÉ—a bayan ya sauke ajiyar zuciya. Bai ce komai ba sai ajiye wayar da ya yi, ya koma ya zauna a gefen gadon hannunsa É—aya cikin sumar kansa, idanunsa a lumshe, zuciyarsa na sake cunkushe wa waje É—aya.

A ɗaya ɓangaren kuwa kallan Abdoul Maama ta yi ta ce

"Ya katse ne?" Ta tambaya tana kallan sa. Gyara zaman wayar ya yi a hannunsa kafin ya jinjina kai, a nutse ya buÉ—e baki ya ce

"Ehh, amma dai sauƙin ta ɗaya yana cikin gidan nan." Ajiyar zuciya Maama ta sauke kana ta ce

"Ku bar shi, kar wanda ya sake kiran sa don Allah, ni da kaina zan je na same shi zuwa gobe, na san kafin nan In Sha Allah zuciyarsa ta yi sanyi."

"Toh shi kenan." Abdoul ya amsa da hakan. Daga haka ya yi sallama da su ya fice daga É—akin.
Chapter 7 · 0% Book details