Sashe 15
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.. "Maza maza mun zo tasha. Ina na Kano su sauko." Abin da kwandastan motar ke ta faɗa kenan lokacin da yake a waje, hannunsa ɗore a kan motar yana ɗan bubbugawa. Kallan juna Daneen da Ameer suka yi, kafin a sukwane suka sakko daga cikin motar. Dama tuni sun ba wa kwandastan kuɗinsa, don haka sai suka soma taka wa suna rarraba idanunsu a inda suke. Daneen ta haɗiye wani busshashshen yawu da ya haɗu cikin bakinta da ƙyar zuwa maƙogwaronta. Ta kalli dogon titin da suke kai, wanda kwata-kwata bai yi mata kama da titin ƙauyen su ba. Ita kwata-kwata ma ba ta ganin ƙarshensa, kai ba ma ƙarshensa ba, wajaje take gani duk inda ta juya, maimakon ta gan su a haɗe kamar yadda nasu gidajen suke. Sai dai kwata-kwata ma ita ba ta hangi wani gida ba, kenan ina ne gidan mai gari? Shi dai Ameer ban da sake rungume jakarsa babu abin da yake yi, lokaci ɗaya kuma yana bin garin da duhu ke sake mamaye shi da kallo. A karo na barkatai suka sake kallan juna, idanun kowannensu ya yi tsilli-tsilli, ya raina fata, gaba ɗayansu kuma da abin da suke saƙa wa a cikin ransu. Sai dai abin da ya fi yawo a zuciyar kowannen su shi ne 'Shin ina ne nan ɗin suka kawo kansu?'
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 10
Idanunta da suka yi rau-rau ta ɗaga ta kalli Ameer ta ce jikinta a matuƙar sanyaye
"Na shiga uku Ameer, ina ne nan?" Cikin rashin sanin abin yi Ameer ya girgiza kai kafin ya ce
"Ni ma ban sani ba Adda." Ya faÉ—a yana sake maida kansa inda suke. Duk da yadda take jin tsoro na sake shigar ta, hakan bai hana ta kallan wani mutum da ke gefen su ba. Cikin sanyin murya ta gaida shi, ya amsa yana kallan yanayin shigarta.
"Don Allah gidan Mai gari muke nema." Ta yi ƙundunbalar faɗin hakan, cike da fatan su samu abin da suke so.
"Toh ikon Allah! Mai gari ko Mai Unguwa?" Ya tambaya yana kallan ta. Shiru Daneen ta yi tana tunanin abin da ya kamata ta ce, sai dai kafin ta ida tunanin ta tsinto muryar Ameer ya ce
"Eh shi." Ya yi maganar yana jinjina kai kamar ƙadangare, lokaci ɗaya kuma yana sake rungume jakarsa a hammata.
"Toh da yake dai babu nisa daga nan, ku biyo ni na nuna muku, idan ya so sai na wuce inda zan je." Cikin matuƙar farin ciki suka shiga yi masa godiya, a ransu duka ji suke tamkar su taka rawa. Bin bayan nasa kuwa suka yi kamar yadda ya faɗa, suka soma tafiya. Duk inda suka gifta sai sun bi wajen da kallo.
"Ai dama na faÉ—a miki Adda, yanzu ba ga shi ba har mun samu gidan." Ameer ya faÉ—a farin cikin da yake ji na bayyana a kan fuskarsa da kuma muryarsa. Ita ma murmushin ta yi kana ta ce
"Ai kuwa dai. Allah har na ƙagu na yi ido biyu da Innarmu." Ta yi maganar daidai lokacin da mutumin ya juyo ya kalle su, sai da ya soma nuna musu wani gida da ke ɗan nesa kaɗan da inda suke kafin ya ce
"Kun ga wancan gidan, shi ne gidan Mai Unguwar nan Unguwar." Ba tare da damuwa da bayanin da ya musu ba suka sake masa godiya cikin matuƙar farin ciki. Daga haka ya yi musu sallama ya ƙara gaba, ya yin da suka nufi inda ya nuna musu.
Lokacin da suka isa, sun samu wani yaro tsaye a ƙofar gidan. Suka sanar da shi abin da ke tafe da su na son ganin Mai gari.
"Ai kuwa dai Mai Unguwa ba ya nan, ya yi tafiya an yi masa mutuwa. Amma idan wani abun ne ku faÉ—a sai na taimaka muku." Kallan juna Daneen da Ameer suka yi, kafin suka maida duban su kan yaron.
"Dama zuwa muka yi mu tambayi gidan wani Alhaji Abubakar, wanda ya yi aure kwanan nan, ya auri wata Fatima." Tsayawa yaron ya yi yana kallan su irin kallan rainin hankalin nan. Sai dai abin da ma ba su sani ba, cikin ransa tunani yake anya kansu É—aya? Ya duk girman unguwar nan amma su zo suna tambayar gidan Alhaji Abubakar wai wanda ya auri Fatima. Anya kuwa?
"Ba a nan garin kuke ba ne?" Girgiza kai suka yi. A wannan karon ma dai Ameer ne ya ce
"Daga ƙauyenmu muke. Muna neman su ne shi ya sa muka taho kai tsaye gidan Mai gari. Tun da yadda muka sani duk wani gida da ke a ƙarƙashin ƙauyen Mai gari ya san masu gidan,lll shi ya sa muka zo." Sai a lokacin yaron ya kaɗa kai, shi dama ya san a rina, ashe daga ƙauye suke.
"Kun ga, nan fa ba ƙauye ba ne. Ba a ƙauyenku kuke ba. Kun ga ku rufa wa kanku asiri ku koma inda kuka fito, tun da ba ku san inda waɗanda kuka fito nema suke ba. Wannan garin yana da faɗi, ba kamar yadda ƙauyenku yake ba. Mu nan ba iya garin nan ba, duk wata unguwa da ke cikin garin nan tana da Mai Unguwa, kuma Mai Unguwa ba shi da hurumin sanin mutanen da ke cikin unguwarsa. Ka ga kenan ba za ku taɓa samun abin da kuke nema ba." Tun da ya soma maganar suke kallan sa, har ya ƙare. Jiki a matuƙar sanyaye suka yi masa godiya. Bayan ya yi musu sallama ya wuce cikin gida. Ba su taɓa tunanin haka abin yake ba. Sun ɗauka tamkar yadda ƙauyensu yake nan ɗin ma haka yake. Shi ne dalilin da ya sa suka taho ba tare da wani tunani ba.
***
"Sister ban san ta ina zan fara ba." Sultanah ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye. Gyara zama Hidaya ta yi kafin ta ce
"Kin ga ki fara ko ta ina ne. Na ƙagu na ji me ke damun ki, tun da kuka dawo gida dama na fahimci tabbas akwai abin da ke damun ki." Shiru Sultanah ta yi tana kallan Hidaya ba tare da ta tanka ba. Hidaya ta kamo hannunta ta jinjina mata kai don ba ta ƙwarin gwuiwa.
"Ki sanar da ni." Ta faÉ—a har lokacin tana kallan ta. Ajiyar zuciya ta sauke, ta lumshe idanunta kana ta buÉ—e bakinta ta ce a hankali
"Er'uwa ban san yadda za ki ɗauki zancen ba ke kanki, ballantana kuma har in yi wa Yah Tareeq maganar. Amma tabbas na tsinci kaina dumu-dumu cikin ƙaunar Yah Abdoul." Ta ƙare maganar tana jin yadda mikin da ke cikin zuciyarta ke famuwa. Hannunta Hidaya ta zare daga cikin na Sultanah tana kallan ta sosai cike da matuƙar mamaki.
"Yah Abdoul kuma Sultanah?" Jinjina kai Sultanah ta yi a sanyaye, tana jin duk wani ƙwarin gwuiwarta na zagwanyewa, ganin tilon er'uwarta da take saka rai a kanta tana neman watsa mata ƙasa a ido.
"Kar ki zama mutum ta farko da za ki fara ganin laifi na Hidaya don Allah." Sultanah ta faɗa tana kamo hannun Hidaya. Murmushi Hidaya ta yi don saboda kar ta zubar wa da er'uwar tata ɗan ƙwarin gwuiwar da take da shi ta ce
"Ba watsa miki ƙasa a ido zan yi ba Sultanah. Kawai dai abin ne na ji shi tamkar a mafarki, na kuma yi matuƙar mamaki. Amma In Sha Allah zan taya ki da addu'a idan rabon ki ne shi ɗin Ubangiji Ya juyo miki da hankalinsa tun kafin ki sanar da shi. Don ban san ta yadda za mu sanar wa da Yah Tareeq kina ƙaunar Abokinsa ba." Ajiyar zuciya Sultanah ta sauke kafin ta ce
"Ni ma abin da nake tunani kenan Hidaya. Ina tsoron Yah Tareeq ya ji zancen nan, amma ban san yadda zan yi ba. Abin yana damu na matuƙa a cikin zuciyata."
"Ki yi haƙuri Sisi, In Sha Allah komai zai zo da sauƙi."
"Ke! Maganar wa na ji kuna yi?" Maami da ta fito daga cikin É—aki yanzun ta faÉ—a tana kallan su, tana sanye cikin doguwar rigar atamfa. Tsananin kamar da suke da Sultanah shi ne zai bayyana maka mahaifiyarta ce. Gaba É—aya É—aga kai suka yi suka kalle ta a tsarge. Da sauri Sultanah ta shiga girgiza kai
"Babu komai Maami."
"Anya kuwa?" Ta sake faÉ—a tana kafe Sultanah da ido, kamar mai son gano gaskiyar abin da take faÉ—a a kan fuskarta.
"Ehh Maami." Hidaya ta faÉ—a. Jinjina kai kawai Maamin ta yi, tana wuce wa kitchen É—in da dama abin da ya fito da ita kenan. Wata gauruwar ajiyar zuciya Sultanah ta sauke kafin ta ce
"Na gode wa Allah." Ta faɗa tana dafe ƙirjinta. Bin ta da kallo Hidaya ta yi, tana mamakin yadda ruɗewar Sultanahn ta yi yawa. Sai dai sanin halin Maamin ya sanya ta girgiza kai kawai.
***
Ɗaga kansa ya yi ya kalli wanda ya shigo office ɗin, ya amsa sallamar yana maida dubansa kan takardun, ba tare da ya kalli abin da ke rubuce a cikin su ba ya haɗa su waje guda. Ƙarasawa Abdoul ya yi ya nemi waje ya zauna shi ma hannunsa ɗauke da wasu takardun.
"Ga waɗannan takardun, duk dai cikin na Diyana ne." Abdoul ya faɗa yana miƙa masa takardun. Ba tare da ya ce komai ba, ya karɓa ya haɗa su waje ɗaya. Ba dan ba dan ba, yanzun nan zai saka wani ya ƙoma masa takardun, sai dai ko ma mene ne, ba ya so komai da ya shafe shi ya fita waje. Don haka bayan ya gama haɗa su waje ɗaya, sai ya nemi waje ya killace su. Sai a lokacin ya mayar da duban sa kan Abdoul ya ce
"Ya ake ciki?"
"Na tura maka komai ta E-mail naka, ka bincika bayanin komai na ciki." Jinjina kai Tareeq ya yi kafin ya ja laptop ɗin da ke gabansa ya shiga dannawa cike da ƙware wa. Kyawawan idanunsa na bin duk wani rubutu da ke bayyana a kan fuskar laptop ɗin, kai ka ce haddace kowacce kalma yake yi, saboda yadda yake bin su cike da takatsantsan da son tabbatar da duk abin da ya gani gaskiya ne.