Sashe 31
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Shi kenan, Allah Ya saka maka da alkhairi. A madadin Alhaji Dikko, ina sake miƙa godiya gare ka." Ba tare da Yohana ya amsa ba ya miƙa wa Likitan hannu har lokacin fuskarsa da murmushi suka gaisa. Daga haka ya yi waje, Likitan ya bi shi da kallo yana ci gaba da mamakin kyawawan halaye irin nasa.
Cikin nasara, ikon Allah da kuma tarin addu'o'i daga bakunan iyalan Dikko aka yi wa Daneen da kuma Tareeq aiki.
.. "Sannu yaron nan." Dada ji ta faɗa tana kallan Tareeq cike da tausayawa. Jinjina kai ya yi daga inda yake kwance, yana sake lumshe idanunsa. Shafa goshinsa Maama ta yi tana jin wani irin tausayin ɗan nata, saboda sanin halinsa da ta yi, idan dai har ka ga ciwo ya kayar da shi, toh da gasken ciwon nan ya shahara. Ba ta ce komai ba, sai neman waje da ta yi ta zauna, daidai lokacin da aka turo ƙofar ɗakin. Sultanah, Abdoul da Hidaya, su ne suka shigo. Idanunsa a kan Abdoul ya sauka, cike da mamakin yadda suka shigo tare da su Sultanah. 'Ko dai har abin nasu ya ɗore haka?' Ya raya hakan a ransa, yana fatan a ce da gasken haka ne.
"Tare kuke ne?" Dada ji ta yi tambayar tana kallon Abdoul, tambayar da take ta masa yawo cikin kai. Don haka sai ya maida duban sa kan Abdoul don jin amsar da zai bayar, cike da fatan Allah Ya sa burin ƙanwarsa ya cika.
"A'ah, a cikin asibitin muka haÉ—u." Ya ba wa Dada ji amsar cikin girmamawa.
"Ayyah." Ta yi maganar a taƙaice. Daga haka ya gaishe ta, kafin ya gaisa da Maama. Sai kuma ya ƙarasa inda abokinsa yake.
"Sannu! Ya ƙarfin jiki?" Ya tambaya cikin kulawa. Sai da Tareeq ya lumshe idanunsa kafin ya ce
"Alhamdulillahi."
"Allah Ya ƙara sauƙi, sannu." Yanzu kam jinjina kai kawai ya yi yana sake lumshe idanunsa don so yake ya ɗan sake runtsawa, don jin sa yake tamkar an canja ji. Wani daban yake ji tun bayan da aka yi aikin. Sai dai shi a karan kansa ya matuƙar jin daɗin jikinsa, wanda ya yi kwana da kwanaki rabon da ya ji irin hakan. Su ma Hidaya da Sultanah gaishe da yayan nasu suka yi. Zuwa can Abdoul ya ce
"Maama zan so na ga wadda ta sadaukar da ƙodarta a kan Tareeq ɗinmu, ko don in yi mata godiya." Da sauri Dada ji ta kalle shi ta ce bayan ta soma tafa hannunta.
"Kaa ga aikin shiririta, daga zuwa ɗazu tana bacci babu wanda ya sake komawa. Ke maza ku tashi mu je wajen baiwar Allah ɗin can." Ta ƙare maganar tana miƙewa tsaye. Babu musu dukkansu suka miƙe. Maama ta kalli Tareeq, ganin da alama kamar bacci ya ɗauke shi ne ya sanya ta bin bayan su Dada ji da suka yi waje.
"Allah kuwa Yah Tareeq yana jin jiki, wallahi duk jikina a sanyaye yake." Hidaya ta faÉ—a a marairaice, tana hango fuskar yayanta da ta É—an sauya, kamar ba shi ba.
"Wallahi ke kam.." Ita ma Sultanahn ta faÉ—a a sanyaye.
Hidaya ce a gaba, don haka ita ce ta yi amfani da hannunta wajen tura ƙofar ɗakin. Sultanah, Maama da Dada ji suka bi bayanta. Sai Abdoul da ke a ƙarshe, wanda sai da Maama ta ce ya shigo sannan ya bi bayan su. Gaba ɗayansu idanunsu na kan gadon. Tana kwance har zuwa lokacin tana bacci, duk da yadda take bacci hakan bai hana bayyana yadda idanunta suka ɓurma suka yi ciki ba.
"Allah Sarki baiwar Allah." Dada ji ta faÉ—a tana kallan innocent face É—in Daneen, wadda yarintarta ta gama bayyana ko daga kallan fuskarta. Tun kafin su kai ga zama, Daneen ta wani irin zabura daga baccin da take, a firgice ta furta bayan ta tashi daga kwanciyar da take.
"Ameer!" Gaba É—aya idanunsu sai suka sake koma wa kanta. Tarr ta buÉ—e idanunta cikin É—akin, sai ta shiga rarraba manyan idanun nata, tana kallon duk mutanen da ke ciki.
"Ameer." Ta sake faɗa a kan laɓɓanta har lokacin ba ta daina kallon su ba. Hidaya ce ta tashi ta ƙarasa inda take, ta nemi waje ta zauna kafin ta kalli Daneen da ke takure waje ɗaya ta ce
"Sannu." Kamar sai da ta ce sannun sannan ta tuna abin da ya faru, saboda yadda ta kai hannunta ƙirjinta ta dafe. A hankali ta buɗe baki ta ce
"Tohm."
"Ya jikin?" Sake dafe saitin ƙirjinta ta yi tana sauke wani numfashi kamar wadda ta yi tsere, ba tare da ta ba wa tambayar Hidayan muhimmanci ba ta ce
"Ƙanina.."
"Hidaya taimaka mata ta gyara jikinta, sai ta je ta ga ƙanin nata." Maama ta faɗa. Da "Toh." Hidaya ta amsa, kafin ta miƙe tana kallon Daneen ta ce
"Mu je koh?" Babu musu Daneen ta soma ƙoƙarin saukowa daga kan gadon. Da sauri Hidaya ta riƙo ta saboda ganin yadda ta yi ta koma baya da sauri.
"Sannu." Ta sake furtawa cike da tausayin Daneen É—in. Kusan a tare duk 'yan É—akin suka sake faÉ—in "Sannu." Ya yin da Abdoul ya É—ora da faÉ—in
"Bari na je waje Maama, zuwa an jima sai na shigo." Babu musu ta amsa da "Toh." Daga haka Abdoul ya saka kai ya fice daga É—akin, Sultanah ta bi shi da kallo tana murmushi.
Hidaya ce ta taimaka wa Daneen sosai wajen yin komai, don har cikin ranta tausayi take ba ta. Sun kwashe fiye da rabin awa kafin suka dawo ɗakin. Nan ma dai ta taimaka mata ta sake kwanciya, saboda yadda ta fi jin daɗinta. Don ita kanta ji take kamar ba ita ba. Wajen da aka mata aikin kuwa babu laifi yana mata ciwo, amma dai ita wannan ɗin bai ɗaɗata da ƙasa sosai ba, duk kuwa da cewar ba zafi ne normal ba, tana jin zafin har cikin jikinta, amma kuma ba ta ɗauka hakan da muhimmanci ba. Don gani take duk wani zafi da za ta ji, toh zai biyo bayan zafin da take ji na ganin ɗan'uwanta cikin halin ciwon da sanadiyyar wasu suka jefa shi. Sai a lokacin sannan suka gaisa, dukkansu suna yi mata ya jiki.
"Alhamdulillahi." Shi ne abin da take amsawa da shi kawai, don ita dai gaba É—aya hankalinta yana kan Ameer.
"Mun gode sosai, Allah Ya saka miki da alkhairi, Allah Ya biya miki buƙatunki na alkhairi, Allah Ya ba wa ɗan'uwanki lafiya." Dada ji ta faɗa tana jin har cikin ranta abin da yarinyar ta yi musu yana ɗaya daga cikin alfarmomi masu matuƙar muhimmancin da har abada ba su taɓa mantawa da shi ba. Ba kuma za su taɓa iya biyanta abin da ta musu ba.
"Ameen, ina so na ga ƙanina." Ta faɗa a narke tana kallon Dada ji. Ajiyar zuciya Dada ji ta sauke tana kallon Maama ta ce
"Anya kuwa za su bar ta ta fita?" Kallon ta Maama ta yi kana ta ce
"Hakan ba damuwa ba ne, amma kuma ai jikinta za a duba. Ki bari idan kin ɗan ƙara jin dama-dama ko zuwa gobe ne sai ki je ki gan shi." Maama ta ƙare maganar tana kallon Daneen. Runtse idanunta Daneen ta yi tana jin yadda take bugun zuciyarta ya ƙaru. Ta yaya ma za ta iya haƙura ba tare da ta ga ɗan'uwanta ba? Ba ta san lokacin da ta miƙe ba, duk da yadda wajen ciwonta ya amsa, amma hakan bai dame ta ba. Sai dai ta runtse idanunta na tsawon sakanni kafin ta buɗe. Ta ce muryarta na karkarwa.
"Don Allah ki bar ni na je na gan shi kin ji? Zan iya tafiya, zan iya komai ma kin gani?" Ta yi maganar tana soma miƙewa tsaye. Da sauri Hidaya da Sultanah suka miƙe, suka riƙo ta.
"Maama don Allah ki bar ta ta je, tana so ta gan shi ne." Hidaya ta faÉ—a fuskarta a narke tana kallon Maama.
"Toh shi kenan, ku je ke da Sultanah ku raka ta. But u should go and ask doctor Adam, za ta iya fita?" Jinjina kai Hidaya ta yi tana sakin Daneen a hankali ta fice daga ɗakin. Daidai lokacin da wayar Maama ta yi ƙara. Ta kalli mai kiran kafin ta ɗaga. Sai da suka gaisa kafin daga can ɓangaren Umman Jawahir ta ce
"Ya mai jikin?"
"Alhamdulillah, jiki da sauƙi." In ji Maama.
"Wallahi na ƙagu mu dawo in ga jikin yarona. Kin ga musamman ma dai Jawahir duk ta bi ta ɗaga hankalinta. Tun da aka kwantar da shi a asibitin nan ta ɗauki damuwa ta ɗora wa kanta, yanzu haka ma kin ganta kuka take, don Abbanta ya ce ba gobe za mu taho ba." Murmushi Maama ta yi, a ranta tana ji idan Allah Ya yarda yaronta ya samu mace mai sonsa tsakani da Allah kenan.
"Ayyah Allah Sarki Jawahir. Ai babu komai me ye na damuwar? Jikin nasa kuma da sauƙi ai, ki ƙara rarrashinta."
"Ni ma haka nake faɗa mata. Kin ji koh Jawahir?" Umma ta ƙare maganar tana kallon Jawahir da ke gefen ta.
"Yawwah." Maama ta faÉ—a.
"Toh Allah Ya ƙara afuwa. Kuma In Sha Allah muna dawowa nan za mu taho babu ɓata lokaci."
"Allah Ya yarda." Daga haka suka yi sallama. Ba ta daɗe da ajiye wayar ba Hidaya ta dawo cikin ɗakin. Ita da Sultanah suka taimaka wa Daneen wajen kai ta ɗakin da Ameer yake. A bakin ƙofar suka bar ta.
"Bari mu jira ki a nan." Hidaya ta ƙare maganar tana sakin murmushi. Ita ma murmushin ta ƙaƙalo kafin ta jinjina kai. Daidai lokacin da Yohanah ya fito daga cikin ɗakin, yana shirin rufe ƙofar ya ga Daneen. Sai ya saki murmushi yana faɗin
"Ke ce?" Jinjina kai Daneen ta yi hannunta dafe da gefenta don ta fi jin daÉ—in tsayuwar.