← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 49

Sashe 49

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Kuma idan kika sake kika fita daga cikin ɗakin nan za mu haɗu da ke. A nan za ki kwana daga nan har zuwa lokacin da za ki amince da ƙudirina." Daga haka ta bar wajen cike da sassarfa ta shige ɗakinta. Runtse idanunta Sultanah ta yi tana jinginar da kanta a kan kujera, yau kam wace irin baƙar rana ce a gare ta? Me Maami take faɗa haka? Shin da gaske abin da yake faruwa gaskiya ne, ko kuwa wani mummunan mafarki ne take yi, wanda ke neman datse mata farin ciki? Sai a lokacin sannan ta iya fashe wa da wani marayan kuka, ta cure waje ɗaya tana kifa kanta a tsakiyar gwuiwoyinta, ta shiga raira shi, cikin rashin sanin abin yi.

... Jinjina kai Dada ji take yi cike da mamakin wannan al'amari na Ubangiji, wato ba ta taɓa kawo wa har cikin ranta Tareeq ɗin zai yi wannan tunanin mai matuƙar amfani ba. Sai ga shi da kansa ya samar wa kansa mafita.

"Wato ina ga na fi kowa farin ciki da wannan abu ya faru, Ubangiji Allah Ya tabbatar da alkhairi, Ya yi muku albarka. Alhassan." Ta ƙare maganar tana kallon Abeey. Cikin girmamawa Abeey ya ce

"Na'am Dada ji."

"Ina ganin a gobe goben nan, ba sai wata rana ba, a É—aura auren nan kowa ma ya huta." Cikin na'am da zancen Dada ji Abeey ya ce

"In Sha Allah Dada, duk yadda kika faɗa haka za a yi." Ya faɗa har cikin muryarsa za ka iya fahimtar yana cikin farin ciki. Don kuwa tabbas ya yi farin cikin matuƙa.

"Amma ina so da kaina na ji daga bakin yarinyar, kafin nan sai na san abin yi." Jinjina kai Dada ji ta yi kafin ta ce

"Gaskiya ne wannan, hakan na da kyau."

Wayarsa Abeey ya É—auka ya kira number Hidaya.

"Turo mini Daneen yanzu." Kasancewar ta san inda suke ya sanya ta amsa wa da "Toh Abeey." Daga haka ta miƙe ta je ta kira Daneen ɗin, a ranta tana fatan Allah Ya sa abin da take tunani ne yake shirin kasancewa. Har ƙofar ɗakin Abeey ta raka ta, tana shirin juyawa Daneen ta yi saurin riƙo hannunta tana faɗin

"Hidaya."

"Na'am." Hidaya ta amsa bayan ta kalle ta. Narkar da fuska ta yi, kamar wadda ke shirin yin kuka ta ce

"Tsoro nake ji, ba zan iya shiga ni kaÉ—ai ba." Hannunta Hidaya ta kama tana murmushi

"Toh mu je in raka ki." Ajiyar zuciya Daneen ta sauke, kana ta bi bayanta suka shige É—akin Abeeyn.

Sai da suka gaisar da kowa, sannan wajen ya É—auki shiru na tsawon mintuna. Zuwa can Abeey ya soma faÉ—in

"ÆŠiyata Daneen, shin kin amince da auren Tareeq kamar yadda ya sanar da ni?" Runtse idanunta Daneen ta yi na tsawon sakanni, kafin tun kafin ta kwafsa, kawai sai ta É—aga kanta a sanyaye.

"Ma Sha Allah! Alhamdulillah." Dada ji ta faɗa cikin wani irin farin ciki. Shi ma ajiyar zuciya Tareeq ya sauke, yana ji bayan wani lokaci yau ga wata mace ta amince da aurensa, ba don dukiyarsa ba, ba da niyyar mallake masa dukiya ba, ba kuma don ƙirar jikinsa ba, ba kuma don tana son shi ba. Sai kawai don kimarsa da darajarsa a wajenta. Lallai kuwa Daneen ɗin za ta ci gaba da kasancewa mai daraja da kuma ƙima a wajensa. Bayan wajen shuɗewar mintuna goma Abeey ya ce

"Zan ɗauke ki mu je ƙauyenku saboda sanar da mariƙiyarki batun aurenki da za a gabatar a gobe." Tun kafin ya ƙarasa maganar ta ji zuciyarta ta buga. Don haka yana ida wa ta fara faɗin bayan ta ɗaga kanta karo na farko ta kalli Abeeyn. Sai a lokacin ne ma sannan ta fahimci Hidaya ba ta cikin ɗakin.

"A'ah kar ka je don Allah. Za ta iya yin duk wani abu don kar a yi auren nan. Ka yi haƙuri kar ka je." Ta faɗa har lokacin tana girgiza kai ƙirjinta na ci gaba da bugawa. Cike da tausayawa Tareeq ke kallon Daneen, lallai tabbas rayuwar yarinyar nan akwai tarin ƙalubale a cikinta. Gaba ɗaya 'yan ɗakin ma da kallon tausayin suke bin ta da shi. Abeey ya sauke ajiyar zuciya tausayin yarinyar na sake kashe masa jiki.

"Kar ki damu, kar kuma ki yi kuka. A yanzu É—in nan mu ne iyayenki In Sha Allah. Ba ma za ta ji labarin ba ballantana ta hana."

"Alhassan kamar yadda ta faɗa ɗin a bari idan babu damuwa. Idan komai ya lafa shi Tareeq da kansa sai ya ɗauke ta ya kai ta can ƙauyen nasu wajen kishiyar kakar tasu." Dada ji ta faɗa. Jinjina kai Abeey ya yi kana ya ce

"Abin da nake nufi ke nan ni ma Dada." Ya dakata a nan kafin ya maida duban sa kan Maama ya ci gaba da faÉ—in

"Saboda haka ku fara shirye-shiryen duk wasu abubuwa da suka dace, In Sha Allah gobe ne ɗaurin auren. Duk wasu abu da ake buƙata a yi su daga baya."

... Tsaki ya ja a karon farko yana kallon mai kiran nasa. Kamar kar ya ɗaga, sai kuma ya tamke fuskarsa, yana shirin ɗagawa kiran 4ps ya shigo wayar. Sai ya sauke ajiyar zuciya, duk da ya san shi ma ɗin ba lallai ne su kwashe ta da daɗi ba. Kara wayar ya yi a kunnensa bayan ya ɗaga, daga can ɓangaren Pops ya ce

"Yohana."

"Yes, Pops."

"Kana ina?" Pops É—in ya faÉ—a, cikin muryarsa babu alamun wasa.

"Me ya faru?" Ya katse shi da tambayar hakan.

"Ka zo ka É—auke ajiyar ka."

"Amma Pops.."

"Na dai faɗa maka, barin garin ma za mu yi gaba ɗaya. Idan kuma ba ka yi hakan ba za ka ga ba daidai ba." Numfashi ya sauke yana jin ransa na ɓaci, be ce komai ba ya datse kiran yana jan tsaki. Har wani huci yake fitarwa saboda tsabar ɓacin rai. Wato Babansa na son ya kwaɓa masa aiki. Ya dafe goshinsa yana tunanin ta ina zai fara?

... Tun ɗazu yake ganin wayar tana kawo haske babu ƙaƙƙautawa. Alamar kira ne ke ta shigowa. Don haka ya ɗan ja gajeren tsaki, kafin ya janyo wayar. Ganin sabuwar number ce ya sanya shi jefar da wayar ya kwantar da kansa kan bangon gadon idanunsa a lumshe. Zuwa can sai ya ji alamar shigowar saƙo, ya ɗan gyara zamansa kana ya janyo wayar ya buɗe saƙon, cikin zuciyarsa yana mamakin yadda ya ji ya zaƙu da son karanta labarin tun da ya ji alamar shigowar saƙo.

"Shege, wai har ni za ka nuna wa ba ka gane waye ni ba? Duk iya shegen nan fa mu ma mun iya shi, ka fi kowa sanin hakan. Shi ya sa na yi yadda zan yi na nemo number ɗinka, na kikkira kuma ka ƙi ɗagawa. Dalili kawai nake so na ji na abin da ka aikata. Amma dai kar ka manta duk iya shegen nan ni ma na iya fa, musamman ma kuma yanzu da na ƙaro wani."

Ya karanta message ɗin ya kai sau biyar, kamar wanda ke shirin haddace duk wani rubutu, da kuma wasalin da aka yi amfani da su wajen rubuto saƙon. Ya yi shiru yana jin yadda zuciyarsa ke ɗan bugawa, wanda hakan ya tilasta masa lumshe idanunsa. A hankali ya sake kwantar da kansa jikin bangon gadon, yana jin yadda saƙon ke ci gaba da yi masa amsa-kuwwa cikin kunnuwansa, tamkar wanda ake sake karantowa. Ba ya fatan abin da yake tunani ya tabbata. Ya fi awa ɗaya a hakan, yana ci gaba da saƙawa da warwarewa, zuciyarsa tamkar za ta yi bindiga. 'Ko kuwa dai batun aurensa ne ya zagaya har inda ba su yi tunani ba, wanda hakan ka iya janyo tabbatuwar tunaninsa?' Ya tambayi kansa, duk da ya san babu mai ba shi wannan amsar.

... Washe-gari ta kasance ranar Juma'a, wato ranar da za a ɗaura aure. Bayan an yi Sallahr Azahar, a babban masallacin Dikko da ke cikin unguwarsu, Abeey da ya zama waliyyin amarya, ya karɓi sadakinta a hannun Alhaji Abubakar (Mahaifin Abdoul) wanda shi kuma ya zamo waliyyin ango. Cikin ƙanƙanin lokaci dubban mutane suka shaida ɗaurin auren DANEEN da kuma angonta TAREEQ ALHASSAN DIKKO. Ɗaurin auren da duk da ba a wani shirya masa ba, amma manyan mutane da dama sun samu halartar ɗaurin auren. Kafin ka ce mene ne wannan, tuni maroƙa sun fara shela, ta hanyar faɗin

"Allah Ya nufa. Tabbas Allah Ya nufa. Aure ne irin na girma, an ɗaura auren Shalele, ɗa ga Alhaji Dikko, Tareeq, tare da amayarsa Daneen. Alƙawarin Allah Ya cika." Maganganun da suka tilasta shi runtse idanunsa ke nan, wani babban al'amari da bai yi tsammani ba, shi ne bugun zuciyar da ya ji ya ziyarce shi. A nutse ya buɗe bakinsa, a kan laɓɓansa ya shiga furta.

"Ya Hayyu Ya Qayyum."

Alhamdulillah! A nan na kawo ƙarshen littafin DANEEN Book 1. Mai son ci gaba da karanta DANEEN Book 2 har zuwa Book 3, zai tura ₦500 ne ta..

8124818273
Zahra'u Yusuf Ishaq
Opay

Shaidar biya ta wannan number 08124818273

Ko kuma kai tsaye a tuntuɓe ni ta 08124818273.
Chapter 49 · 0% Book details