← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 49

Sashe 37

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Toh." Sultanah da Hidaya suka amsa kusan a tare. Sai a lokacin suka kalli Daneen, wadda duk suna sane da ita, sun ƙyale ta ne ta yi kukan, don sun san dole ɗan'uwanta ta tuna shi ya sa take kuka.

"Su kai ta ɓangaren su kuma kamar ya ya?" Maami da ke ƙarasowa wajen ta faɗa tana bin Daneen da wani irin kallo, tamkar ita ce mai gidan. Da mamaki Abeey ya kalle ta ya ce

"Asma'u.." Ya ambata yana kallon ta da matuƙar mamaki shimfiɗe a kan fuskarsa. Sai da ta girgiza kai sannan ta ce

"A'ah, ai wai tambaya ce." Girgiza kai Abeey ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya ja siririn tsaki yana barin wajen.

"Toh ita ce yarinyar da ta ba wa Magaji ƙodarta." Muryar Dada ji ta katse mata saƙe-saƙen da take a zuciyarta. Ta san da biyu ta faɗi hakan, don ta san ba ta ƙaunar ta ji ta kira Tareeq ɗin da Magaji. Abin da ba ta iya ɓoyewa kenan har a kan fuskarta. Sai da ta ɗauke kai tana kai wa iska harara, ba tare da ta bari kowa ya ganta ba sannan ta ce

"Amma don kawai ta ba wa Tareeq ƙoda, hakan ba shi ke nuna za a shigo mana da ita har cikin gida ba tare da mun san wace ce ita ba."

"Aou kawai ne ma Asma'u? Ehh lallai.." Dada ji ta faÉ—a tana jinjina kai. ÆŠauke kai ta yi tana jefa wa Sultanah da ke ta narke fuska, tana yi mata alamun ta bari don Allah harara. Ita kuwa ko a jikinta, don ita dai haka nan kawai tun kallo É—aya da ta yi wa yarinyar ta ji kwata-kwata ba ta kwanta mata ba.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 24

Murmushin yaƙe Tareeq ya yi, wanda ya tsaya iya kan laɓɓansa. Ya girgiza kai, mamakin halin Maamin na kama shi. Ta yadda ita kwata-kwata ba ta iya ɓoye abu, sai ta amayar da abin da ke ranta sannan take samun nutsuwa. Har Dada ji ta buɗe baki za ta sake yin magana, sai kuma ta fasa, ta juya ta kalli su Hidaya ta ce

"Ke Hidaya ku wuce da ita sashenku. Zuwa an jima idan Allah Ya kai mu za mu haÉ—u." Babu musu Hidaya ta amsa da "Toh." Daneen da ta fahimci da ita ake, sai ta bi bayan su Hidaya.

"Ki huta lafiya Dada ji, bari na raka Tareeq sashensa." Maama ta faÉ—a ba tare da ta kalli inda Maami take ba. Murmushi Dada ji ta yi kana ta ce

"Tareeq ɗan gatan Maama. Allah Ya ƙara lafiya." Ta haɗe maganar lokaci ɗaya. Ɗan lumshe idanunsa Tareeq ya yi kafin ya yi murmushi ba tare da ya ce komai ba. Dada ji ta wuce sashenta, ya yin da Maama da Tareeq suka wuce sashen nasa. Da kanta ta buɗe ko'ina. Tamkar suna cikin gidan, babu wani abu na datti, ko kuma wanda zai nuna an daɗe ba a shiga ɗakin ba. Saboda kullum duk da ba ya cikin gidan, sai Hidaya ko Sultanah, ɗaya daga cikinsu ta zo ta gyara ɗakin. Har bedroom ta kai shi, sai da ya nemi waje ya zauna sannan ta ce

"Ka samu ka yi wanka, ka yi bacci ka huta sosai yau É—in nan." Ta faÉ—a don ta san halinsa sarai. Jinjina kai ya yi yana É—an murza goshinsa ya ce

"In Sha Allah Maama." Murmushi ta yi, tana jin farin cikin yadda ta ga jikin yaron nata ya yi matuƙar kyau, wanda hakan ke nuna yadda ya samu lafiya. Sai da ta miƙe sannan ta ce

"Bari na wuce."

"Toh Maama." Daga haka ta fice daga ɗakin. Sai da ya tabbatar ta fice daga sashen sannan ya sauke ajiyar zuciya, ya dawo da dubansa cikin ɗakin, idanunsa a kan laptop ɗinsa da ke ajje gefe guda. Ya ɗan fesar da iska daga cikin bakinsa kafin ya miƙe. Kai tsaye toilet ya faɗa, ya yi wankan da ya kwana biyu bai yi irinsa ba da ruwa mai matuƙar ɗumi. Ya kwashe kusan awa guda sannan ya fito, yana jin iska na ratsa ko wacce kafar gashi ta jikinsa. Kai tsaye gaban mirror ya nufa, ya shiga taje kwantacciyar sumar kansa. Ya taje ta tsaff, sannan ya shafe jikinsa da turarukansa masu matuƙar daɗin shaƙa. Cikin wata doguwar rigar jallabiyya ya shirya, wadda kalarta ta karɓi kalar fatarsa. Tattausar fatar jikinsa ban da sheƙi babu abin da take yi. Key ya ɗauka ya ƙarasa ya kulle ƙofar gaba ɗaya, sai ya bar key ɗin ma a jiki. Kai tsaye ya wuce kan gadonsa, ya zauna. Ƙafarsa ɗaya na tankwashe a kan gadon, ya yin da ya saukar da guda ɗaya ƙasa. Ya saka hannunsa ya ja laptop ɗin da ke ajiye ya kunna ta. Kamar yadda ya tsammata ayyuka ya tarar jingim a gabansa. Ya lumshe idanunsa yana tunanin ta ina zai fara. Ɗaya bayan ɗaya ya din ga bin komai da ya kamata ya duba. Har zuwa bayan wani lokaci. Ya fito da wayarsa da tun da ya kwanta a asibiti bai sake bi ta kanta ba ya kunna. Tun kafin ya kai ga buɗe ta kira ya shigo cikin wayar. Ya fesar da zazzafar iska daga bakinsa yana kallan mai kiran nasa. A nutse ya amsa wayar, ya shafe wajen rabin awa suna magana kafin ya katse, ya kira wata number. Daga can ɓangaren aka ce bayan sun gaisa

"Yallaɓai za ka iya shigowa kuwa? Abubuwa da yawa suna jiran ka." Sai da ya ɗan yi jimm kafin ya ce

"Zan yi ƙoƙarin shigowa, ni kaina na yi kewar komai, ba kuma na son abubuwa su haɗe mini, saboda haka zan shigo gobe idan Allah Ya kai mu, ka tura mini duk wani abu da ya kamata na sani kafin na zo." Daga haka ba su daɗe ba ya katse wayar. Haka ya din ga yin waya a daren kusufa-kusufa. Daga wannan sai wannan, wani su daɗe suna wayar, wani kuma ba sa wuce mintina kaɗan. Ranar dai gaba ɗaya haka ta ƙare ba tare da ya rintsa ba. Domin kuwa bayan ya gama abin da zai yi, sai yi shiga yin sallolin da ya saba duk dare, bayan ya idar kuma ya shiga muraja'ar Al Kur'ani.

... Tun da suka shigo ɗakin take kallon sa, ita dai i zuwa yanzu ta daina mamakin irin waɗannan tanƙama tanƙaman ɗakunan na alfarma. Wani irin ƙaton ɗaki ne da ya ji kaya masu kyau matuƙa. Komai a wataye yake ba tare da takura ba, abubuwa kala-kala masu ƙawata ɗaki duk ɗakin ya ji su. Komai biyu ne cikin ɗakin, wanda hakan ke nuna kowa na da mallakinsa. Ta ɗaga kai a hankali tana kallon wani waje da tabbas ya fi yi mata kama da banɗaki, don i zuwa yanzu ta soma fahimtar abubuwa da yawa tun bayan shigowar su cikin garin Kano.

"Ki shiga ki yi wanka." Ta jiyo muryar Hidaya. Da sauri ta kalle ta, sai kuma ta jinjina kai tana ƙaƙalo murmushi. Kawai sai ta yi gaba, wannan ledar da take ta fata a ce an shigo da ita ta hanga, don haka kai tsaye can ta nufa don ɗauke wayar da Yohana ya ba ta.

"Akwai komai na buƙata a ciki, bari mu je mu dawo." Hidaya ta sake faɗa. Sai da ta lumshe idanunta tana jin daɗin hakan, sannan ta ce bayan ta juyo

"Tohm." Daga haka suka fice daga ɗakin a tare. Sauke ajiyar zuciya ta yi, kai tsaye ta nufi jakar nan, ta yi saurin ciro wayar ta riƙe a hannunta. Juya ta ta shiga yi, don kamar yadda ta faɗa masa kwata-kwata ba ta san yadda za ta yi amfani da ita ba. Kamar jira yake, sai ta ji hannunta yana girgiɗi, ta yi saurin kallon wayar ganin dalilin girgiɗin hannun nata daga wayar ne. Sai ta ga number na yawo a kan wayar. Ƙura wa wayar idanu ta yi kamar mai jiran wani abu, sai kuma ta kai hannunta, tana tuna abin da ya faɗa mata. Don haka ta danna 'Accept' tana kara wa a kunnenta.

"Daneen." Ta ji an ambata daga can ɓangaren.

"Na'am." Ta ambata tana gyara tsayuwarta, don ko ba a faÉ—a ba, ta san shi ne.

"Kun isa gidan?" Ya tambaya. Jinjina kai ta yi tamkar yana gabanta, sai kuma ta buÉ—e baki a hankali ta ce

"Ehh."

"Madallah, kamar yadda na faɗa miki ki yi takatsantsan da wayar nan. Zan din ga kiran ki a kai a kai. Yanzu ma kuma na kira ne don na sanar da ke, kar ki ce za ki din ga zama cikin ɗaki, a'ah.. ki din ga ƙirƙiro duk wani abin da zai sa ki din ga ganar mana takun Tareeq. Duk wani takunsa ya kasance kina sane da shi, kina kuma sanar mini, ta hakan ne kawai zai sa mu cimma abin da muke so."

"Tohm." Ta amsa masa bayan ta gama jin bayanin nasa.
Chapter 37 · 0% Book details