Sashe 43
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Tabbas zancenka ya yi Alhassan, kuma In Sha Allah hakan shi ne mafita. Ko babu komai Jawahir 'yar'uwar Tareeq ce, kuma tana son shi, kula da shi a yanayin da yake ciki In Allah Ya yarda ba zai zama matsala ba. Abin da nake so da ku kawai, ku fara shirye-shiryen aure, domin kuwa kamar yadda aka tsaida shi sati mai zuwa, ba za a daÉ—a ba, ba za a rage ba. Za a É—aura shi In Sha Allah. Allah Ya sa hakan ne mafi alkhairi, Allah Ya ba su zaman lafiya, Ya ba wa yarinyar nan ikon kula da Tareeq har zuwa lokacin da zai warke."
"Ameen." Dukkansu suka amsa da hakan, cikin na'am da maganar Dada jin É—ari bisa É—ari.
.... A karo na barkatai ya sake kallon kyakykyawar matarsa da ke zaune a kan kujera. Sai dai ta kwantar da kanta a kan hannun kujerar da take kai ne, hannunta ɗaya yana gefenta kan kujerar, ya yin da ɗayan yake lilo kusa da kanta. Idanunta a lumshe suke, sai dai duk da haka, hakan bai hana ƙwalla sauka a kan kyakykyawar fuskarta ba. Cike da tausayawa yake kallon ta. A kullum a kodayaushe yana rasa ta ina zai soma rarrashinta? Ta ina zai ba ta baki a kan yanayin da ta tsinci kanta? Yana ji a jikinsa tamkar shi ne sila, shi ne silar rugujewar farin cikinta. Sai dai duk da haka, ya zai yi? Ta ya ya zai iya jure ci gaba da kallon ta cikin wannan yanayin? Tunani ya yi wa ƙwaƙwalwarta yawa, a kodayaushe tunani take. Idan aiki take tunani take, idan ta zauna ta yi shiru tunani take, idan bacci take ma duk mafarkin abu ɗaya take, haka zalika ko magana suke, sai dai ya ji shiru, idan ya kalle ta kawai sai ya ga alamar ta faɗa wata duniyar tunani. Wataran kuma sai dai kawai ta zauna ta yi ta kuka, musamman ma idan ba ya kusa da ita, shi ya sa kwata-kwata ba ya son yin nesa da ita. Don ba ya so abin ya yi yawa, kar ya janyo mata babbar matsalar da ta fi wadda take ciki a yanzun wato Depression.
"Fatoum.." Ya faÉ—a a sanyaye kamar yadda ya saba kiran ta da hakan. A karo na farko ba ta ji ba, sai da ya sake maimaitawa sannan ta buÉ—e idanunta da sauri ta tashi zaune sosai tana kallon sa da jajayen idanunta.
"Na'am." Ta faÉ—a tana yin amfani da hannunta wajen goge fuskarta.
"Ba za ki yi ƙoƙari wajen rage damuwar nan ba koh? Kin manta abin da Likita ya faɗa koh? Ki yi haƙuri don Allah ko da ba za ki daina duka ba, don na san hakan abu ne mai matuƙar wahala, amma a ƙalla ki rage don Allah. Ko da ni ma zan samu salamar zuci. A kullum idan na kalle ki cikin irin wannan yanayin, ina ji tamkar ni ne sila, kai ba ma tamka ba, ni ɗin ne dai sila. Don Allah ki yi haƙuri Fatoum ki fawwala wa Allah komai, za mu dace In Sha Allah." Duk tsayin maganar nan da ya yi, murmushi kawai ta yi idanunta na kallon wani wajen ta ce
"Uhumm." Ta faÉ—a tana girgiza kai. Shiru ya yi yana kallon ta, ya sauke ajiyar zuciya kafin a sanyaye ya sake kiran sunanta a tausashe. Sai a lokacin tamkar wadda ta dawo daga tunani sannan ta kalle shi, a hankali ya É—aga mata kai kafin ya ce
"Ki yi mini magana mana." Tamkar jira take, sai kuwa ta shiga girgiza kai, tana jin É—acin kalaman da take tattarawa za ta faÉ—a. Tun kafin fitar su ma tana jin É—acinsu ballantana kuma ta faÉ—e su. Sai dai duk da haka, hakan bai hana ta soma faÉ—in
"Na rasa yadda zan yi, ban san me zan yi in ji daɗi ba. Tunanin nan da nake zaunawa na yi shi kaɗai ne mafita ta. Duk da yadda nake ji tamkar ƙwaƙwalwata za ta tarwatse. Amma ba zan iya hana kaina tunanin yarana ba. Ni idan da mutuwa ne ma suka yi, zan haƙura, na san zuciyata za ta fi samun salamar suna can cikin kwanciyar hankali In Sha Allah. Amma yanzu fa? Ban san inda suke ba, ban san suna cikin wane irin hali ba. Shin a wane waje suke rayuwa? Shi ma ban sani ba. Yaushe ne Allah zai haɗa mu? Duk ban sani ba. Yallaɓai ina ji tamkar zuciyata za ta faso ƙirjina ne ta fito ta tarwatse, ina ji kamar ƙwaƙwalwata za ta fashe idan ina tuna su. Ina iya ƙoƙarina wajen ganin na bar wa Allah komai, amma na kasa daina tunaninsu. Kullum suna cikin ko'ina na jikina a manne, komai nake su ɗin ne dai a raina. Shin ya zan yi ni kam da raina? Ina zan ga yarana?" Ta yi maganar a raunace. Ajiyar zuciya ya sauke, yana jin daɗin yadda yau ɗin ta amayar da abin da ke cikin zuciyarta. Ba kamar sauran ranaku da ta fi son ta yi shiru, ko kuma ta yi guntuwar magana ba. Ya runtse idanunsa yana ji da gasken gaske shi ne sila! Shi ne silar raba wannan uwar da 'ya'yanta. Shin me ya sa ma ya shiga rayuwar Fatima? Tabbas da ya san haka ne zai faru, da bai yi yunƙurin neman auren Fatima ba. Ko kuma ma tun farko ya yi fatan kar Allah Ya haɗa shi da Fatima.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 28
Ya shafe kusan mintuna biyu ba tare da ya ce komai ba. Kallon ta kawai yake yi cike da tausayawa, zuciyarsa kuwa wani irin raÉ—aÉ—i yake ji, raÉ—aÉ—in kuma ba na komai ba, sai na zamowarsa silar rugujewar farin cikin Fatimarsa.
"Ki yi haƙuri, in sha Allah yaran nan suna cikin ƙoshin lafiya, kuma za su dawo miki cikin ƙoshin lafiyar. Abin da nake so da ke kawai ki ci gaba da addu'a, sannan ki rage wannan damuwar da kike yi. Kada ki manta da shawarwarin likita da ya ba mu. In Allah Ya yarda nan ba daɗewa ba za mu samu labarin inda suke, tun da har yanzu ban daina cigiya ko Allah zai saka a dace ba. Ki yi haƙuri ki yi shiru." Ya ƙare maganar cikin rarrashi da taushin murya. Hannu Inna-wuro ta saka ta goge fuskarta a nutse, idanunta a lumshe tana ci gaba da jin bugun zuciyar da take fama da shi kusan kowanne lokaci. A hankali ta buɗe baki da ƙyar ta furta
"Allah Ya sa." Ta faɗa tana maida bayanta ta kwantar kan kujerar da take kai cikin rashin sanin abin yi. Bin ta ya yi da kallo ba tare da ya ce komai ba. Ya rasa ta inda zai ɓillowa wannan al'amari. Shiru kawai ya yi ya ci gaba da kallon ta yana tunanin hanyar da zai bi wajen tsananta bincike ko Allah zai sa a dace su sami inda yaran nan suke.
... Turo ƙofar da aka yi shi ne ya sanya Maama ɗaga ido ta kalli mai shigowar. Umma da kuma Jawahir suka ƙaraso cikin ɗakin. Da murmushi ta miƙe tana faɗin
"Lale marhaba." Maida mata da martanin murmushin suka yi kana Umma ta nemi waje ta zauna. Ya yin da Jawahir ta tsaya a gefen kujerar Umman tana sunnar da kai ƙasa. Gaisawa Umma da Maama suka yi, Umman na tambayar jikin Tareeq.
"Jiki Alhamdulillahi wallahi, zuwa gobe ma idan Allah Ya kai mu, muke saka ran sallama, kamar yadda suka faÉ—a."
"Kai Alhamdulillah, Alhamdulillah. Ashe ƙafar ta yi sauƙi ke nan, ko ma in ce ta warke?" Umma ta faɗa tana murmushi. Sai da Maama ta kalli ƙafar Tareeq ɗin da idanunsa ke a lumshe kamar mai bacci kafin ta ce
"Alhamdulillah kam, ta warke za a ce. Sai dai... Ba ku yi magana da yayan naki ba ne?" Ta ƙare maganar da sigar tambaya. Girgiza kai Umma ta yi tana faɗin
"A'ah, ba mu yi ba kam. Amma yau sun haÉ—u za su yi magana da Abban Jawahir."
"Barka da wannan lokacin Maama." Jawahir ta faÉ—a tana murmushi. Amsa mata gaisuwar Maama ta yi cikin sakin fuska, har ranta tana ji in Allah Ya yarda ta yi sa'ar suruka. Sun kwashe wajen minti 20, kafin Tareeq ya buÉ—e idanunsa.
"Sannu Tareeq." Umma ta faɗa tana kallon sa. Sai da ya ɗan saki murmushi kaɗan, wanda ya ƙawata kyakykyawar fuskarsa sannan ya ce
"Yawwah, Barka da wannan lokacin." Ya yi maganar a haÉ—e.
"Barka dai, ya jikin?" Sai da ya jinjina kai sannan ya amsa da
"Alhamdulillahi." Nan ta sake yi masa fatan samun sauƙi, Maama ta amsa da "Ameen."
"Yah Tareeq ina wuni?" Jawahir ta faɗa tana satar kallon wannan kyawawan ƙwayar idanun nasa. Ta kafe shi da idanunta, tun kafin ma ya ɗago nasa ta kasa kalla. A hankali ya ɗaga nasa idanun ya kalle ta, ya ɗan lumshe su, lokaci guda yana buɗewa ya ce
"Alhamdulillah Jawahir, kina lafiya?" Ya yi ƙarfin halin faɗin hakan. Sai da ta gyara tsayuwa tana jin wani irin farin ciki na mamaye ta sannan ta ce
"Lafiya ƙalau." Daga haka ta sake mazewa a gefe ba tare da ta zauna ba. Hannu Maama ta saka ta yafito ta tana faɗin
"Kin ga ni ba na son wata kunya zo ki zauna. Baƙuwarki ce ni?" Ta ƙare maganar tana dariya. Ita ma Umman dariya ta yi, ya yin da Jawahir ke ta murmushi kawai. Kamar yadda Maaman ta faɗa, don haka ta nemi waje ta zauna kuwa.
Bayan shuÉ—ewar wasu mintuna aka fara kiraye-kirayen Sallahr Maghrib, duk suka yi alwala suka dawo cikin É—akin. Maama ta kalli Tareeq ta ce
"Za ka yi alwalar ne?"