Sashe 40
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Aboki Allah Ya sa sau kana son Jawahir." Abdoul ya faÉ—a yana kafe shida idanunsa, kamar mau son gano gaskiyar abin da zai faÉ—a. Tareeq bai kalle shi ba, illa ci gaba da abin da yake yi da ya yi. Bayan shuÉ—ewar minti É—aya, wanda sai ka É—auka ba zai amsa ba ne sannan ya ce bayan ya sauke gajeriyar ajiyar zuciya
"Idan dai har na aure ta zan koyi sonta. Abin da na sani kenan." Ya yi maganar kamar ya gama kenan, sai dai kafin Abdoul ya ce komai ya cigaba da faÉ—in
"Amma idan dai har halayenta sun yi mini." Da mamaki Abdoul ya kalle shi cikin rashin fahimta ya ce
"Ban gane ba? Idan kuma halayen nata ba su yi maka ba fa?"
"Za ma su yi mini, tun da har na amince da ita yanzun." Jinjina kai Abdoul ya yi yana murmushi kafin ya ce
"Toh Allah Ya tabbatar da alkhairi. Ameen." Ya yi addu'a da amsar duka a tare, don ya san halin mutumin nasa ba lallai ya amsa ba. Ko zai amsa ma sai dai ya amsa a zuciya, wanda shi ba zai gane ya amsa É—in ba.
"Sauke ni nan Tareeq." Abdoul ya faɗa yana kallon inda suke ƙoƙarin wucewa. Babu musu Tareeq ya gangara gefen titi ya tsaya. Suka yi sallama da Abdoul sannan ya tashi motar ya bar wajen.
Sanye cikin hijab ɗinta take ci gaba da tafiya, ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ba ta waige-waige saboda kar a gano ta. Dab da za ta isa sashensa, ta yi kiciɓus da Sultanah da riƙe da waya a hannunta. Dakatawa ta yi tana jin zuciyarta na harbawa, ita ma Sultanah dakatawa ta yi tana kallon ta da murmushi a kan fuskarta ta ce
"A'ah, Daneen.. me ya fito da ke?" Wani daƙiƙin murmushi Daneen ta ƙaƙalo tamkar za ta fashe da kuka.
"Ko kin gaji da zaman cikin ne?" Sultanah ta katse ta da faɗin hakan a daidai lokacin da take tsaka da lalubo abin da za ta faɗa. Har wata ajiyar zuciya ce ta suɓuce mata, sai kawai ta shiga jinjina kai tana murmushi.
"Allah Sarki mu je in taka miki." Lokaci guda gaba ɗaya murmushin ya ɗauke. Ta yi maganar tana soma takawa. Kamar ta rusa ihu haka ta ji, sai dai babu yadda ta iya, haka ta bi bayanta suka soma tafiya. Tun kafin su yi nisa, wayar Sultanah ta shiga ƙara. Daneen ba ta ji abin da aka faɗa daga can ɓangaren ba, ta dai ji Sultanah ta ce a sanyaye
"Toh Maami." Daga haka ta sauke wayar daga kunnenta. Ta kalli Daneen a nutse ta ce
"Ki ƙarasa kawai 'yar'uwa, bari na je ciki, Maami na kira na."
"Tohm." Daneen ta faɗa tana jin wani irin farin ciki na mamaye ta. Sai dai ba ta nuna a kan fuskarta ba, saboda yadda take ji a ranta ya zama dole ta saita kanta, ta sauya takunta, idan ba haka ba a ramfo ta. Sai da ta daina gano Sultanah sannan ta ci gaba da tafiya, addu'a take a ranta kada Allah Ya sa ta sake haɗuwa da kowa har ta je inda za ta je. Addu'ar tata kuwa ta karɓu, don har ta ƙarasa inda yake da tabbacin nan ne sashen Tareeq ba ta haɗu da kowa ba. A wannan lokacin ma sai da ta ɗan tsaya ta dudduba, ta ga babu kowa sannan ta wuce cike da sassarfa, har tana ji kamar za ta kifa. Wata kasalalliyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buɗe idanunta da ke a lumshe a kan ƙofar sashen nasa. A hankali ta saka hannunta ta tura. Kamar yadda ta tsammata kuwa, a buɗe take. Ta ji wani sanyi ya ratsa ta, ta saki murmushi tana saka kanta cikin sashen nasa. Sai dai yaɓe-yaɓe! Don kuwa tana taɓa ƙofar ɗakin ta ji ta ɓame da mukulli. Dakatawa ta yi tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. 'Anya kuwa a kullen take?' Ta raya hakan a ranta tana kallon ƙofar ɗakin. Sai kawai ta sake saka hannunta da ke ɗan rawa kaɗan da niyyar turawa, nan ma dai shiru. 'Kenan ƙarya yake, da ya ce sashen nasa a buɗe yake?' Ta tambayi kanta har lokacin idanunta a kan ƙofar. Shiru ta yi na tsawon sakanni, 'Toh ko dai yana nufin sashen ne kawai a buɗe ban da ɗakunansa' Cikin lokaci ƙanƙani wannan tunanin ya faɗo mata. Tunanin da ɗazun kwata-kwata bai kawo mata ba. Saboda yadda ta ƙagu da neman hanyar shiga sashensa kafin cikar sati biyun nan. Cike da ɓacin rai ta fito daga sashe. Ko dubawa ma ba ta yi ba ko da wanda ke kallon ta. Ta ci gaba da takawa gaba ɗaya fuskarta a cakuɗe, jikinta a sanyaye ya yin da take taku cike da sassarfa kuma a hanzarce. A haka har ta ƙarasa sashen Maama. Kamar wadda ba ta da laka, haka taka takawa cikin sashen, zuciyarta gaba ɗaya a cunkushe. Ta ma rasa wanne tunanin za ta ba wa zuciyarta haɗin kai su yi? Ita dai ta san burinta ɗaya ta samu damar shiga ɗakin Tareeq. Don haka dole ne ta miƙe tsaye, ta samo ɗin ko a yi a wuce wajen.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Shi ne abin da kunnuwanta suka soma tsinto mata lokacin da take dab da shiga É—akin. Ta dakata tana jin yadda zuciyarta ta harba lokaci guda.
"Hatsari kuma? A ina? Tareeq? Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Maama ta faÉ—a cikin wani masifaffen tashin hankali. Cikin sakannin da ba su wuce goma ba, jikin Daneen ya É—auki rawa ba kaÉ—an ba. Ta runtse idanunta tana ci gaba da jin yadda kalaman Maaman ke mata amsa-kuwwa a cikin kunne. Ta kai wajen minti 5 a hakan kafin ta buÉ—e idanunta.
"Yanzun nan zai fita? Yawwah ki yi amfani da wannan damar wajen shiga sashen nasa, kar ki yi sanya. Na san ba yanzu zai dawo ba. Don haka ki yi abin da na sanar da ke. Sannan kuma tsaya, ki sake tabbatar mini da yanzun zai fita." Maganganun da suka koma yi mata amsa-kuwwa kenan a maimakon na Maama. Tuni ɓarin jikinta ya ƙaru, gumi ya shiga tsatstsafowa daga ko'ina na jikinta. Ta runtse idanunta a karo na barkatai tana tunanin shin me yake faruwa ne?
Afwan da ji na da kuka yi shiru kwana biyu. Na É—an yi busy ne a kwana biyun, saboda ba na gida. Amma In Sha Allah daga gobe shi kenan.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 26
Duk da yadda take jin ƙirjinta na bugawa ba a daidai ba. A hankali yake bugawa, sai dai da wani irin ƙarfi, hakan bai hana ta yin kasada ba, kawai ta runtse idanunta sannan ta faɗa cikin ɗakin. Daidai lokacin da Maama da idanunta suka yi jajir take faɗin
"Dada ji Tareeq ne wai ya samu hatsari." Yadda ƙafar Dada ji ta yi ƙass ne, tun farkon da ta ji Maama ta ambaci sunan Tareeq ya sanya ta saurin koma wa ta zauna hannunta a kan ƙafar tata. Sai dai cikin tashin hankali take faɗin; idanunta a kan Maama
"Hatsari? Ya Hayyu Ya Qayyum." Ta faɗa har lokacin hannunta na kan ƙafarta. Duk da yadda take jin tana mata zafi, amma tashin hankalin da ta ji kanta a ciki na hatsarin Tareeq ɗin ya danne komai. Ɗaukar mayafi kawai Maama ta yi tana shirin yin waje, Hidaya ta shigo cikin ɗakin. Haka kawai ta ji zuciyarta ta buga tun kafin ta ji abin da ya faru. Kamar kar ta tambaya saboda duk wasu alamu sun nuna ba lafiya ba. Amma kuma hakan ba za ta yiwu ba, don haka ta ce bayan ta ɗan lumshe idanunta
"Maama me ya faru?"
"Hidaya zo ki taimaka mini in miƙe mu tafi. Yayanku ne ya samu hatsari yanzun nan." Wani irin harbawa da ta ji zuciyarta ta yi, shi ne abin da ya sanya ta saurin kai hannunta saitin zuciyarta ta dafe. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka tara hawaye fall. Kwata-kwata ma sai ta kasa furta komai. Ficewar da Maama ta yi ita ta dawo da ita daga hayyacinta. Kawai sai ta fashe da kuka, daidai lokacin da ta ƙarasa inda Dada ji take. Ta sanya hannunta da ke karkarwa ta taimaka mata ta miƙe.
"Ya isa, kukan ya isa haka Hidaya. In Sha Allah ba wani abu ne babba ba." Cikin muryar kuka ta furta
"Ameen." Tana kai hannunta kan fuskarta ta share hawayen. A ranta kawai hasaso ɗan'uwanta take. Fata take Allah Ya sa ba wani abu babba ne ya samu ɗan'uwan nata ba. A tsaye kawai take kamar wadda aka dasa, ban da karkarwa babu abin da jikinta yake yi. Sai da suka fice daga ɗakin gaba ɗaya sannan ta ƙarasa shigewa ciki. Kawai sai ta zube a kan kujerar tana sauke numfashi. Ta kai wajen mintina biyar, kafin ta miƙe ta faɗa cikin ɗakinsu. Ba ta yi wata-wata ba, wajen danna wa number Yohana kira ba. Ringing 1 ya ɗaga wayar, yana shirin fara magana ta katse shi da faɗin
"Me ye alaƙarka da hatsarin da Tareeq ya yi?" Cikin wani irin amo Yohana ya furta
"Hatsari kuma? Yaushe? Ina Tareeq É—in yake?" Cike da tsoron kar abin da take zargi ya tabbata ta ce cikin dakiya.
"Kar ka nuna kamar ba ka sani ba mana." Ta faɗa da gaba ɗaya gaskiyarta, bayan ta yi ƙoƙari wajen danne duk wani tsoro da fargabar da take ji.