← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 49

Sashe 29

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.. "Akwai wani cikin asibitin nan, mahaifinsa mugun mai kuɗi ne. Ƙodarsa ce ta lalace, ana buƙatar a sauya masa wata. Saboda haka idan dai har kika sadaukar da ƙodarki ga ɗansa, toh tabbas ko ma nawa ne, ko nawa ake buƙata, zai biya a yi wa Ameer aiki. Zai iya fitar da shi ma waje ƙwararrun likitoci su yi masa aiki. Ƙodarki guda ɗaya kawai za ki bayar, daga nan ki saka a ranki ɗan'uwanki ya samu lafiya." Tun da Yohanah ya fara magana Daneen ke kallonsa, tana rarrabe duk wata kalma da ya faɗa. Har bayan kusan minti ɗaya da gama maganar ba ta ce komai ba. Sai zuwa can sannan ta ce

"Ka tabbatar zai biya a yi wa Ameer aiki? Ko da an yi aikin kuma na mutu idan na bar Ameer a hannunka za ka kai mini shi wajen mahaifiyarmu?" Daneen ta faÉ—a cikin sanyayyiyar muryarta. Murmushi Yohanah ya yi, yana É—an shafa gefen kumatunsa. Sai da ya soma girgiza kai sannan ya ce

"Nothing will happen. Just pray as much as you can, za a yi komai cikin nasara. Za ki samu lafiya, ɗan'uwanki ma haka." Ya yi maganar a nutse saboda ya ba ta ƙwarin gwuiwa. Ganin ta sake yin shiru ne, ya sanya shi faɗin

"Za ki iya zuwa ku yi magana da doctor, zai yi miki bayanin komai himself." Ajiyar zuciya Daneen ta sauke, kafin a hankali ta buɗe baki da ƙyar ta ce

"Na amince." Ba ƙoda ba, ko da zuciyarta ce za ta iya sadaukar wa a kan ɗan'uwanta, matuƙar zai samu lafiya. Ballantana ƙoda da aka ce mata guda biyu ce. Ubangiji Allah Ya dubi zuciyarta Ya ba wa ɗan'uwanta lafiya, da ita kanta da za a ciri wani abu daga cikin jikinta. Shi kuma wanda zai siya ƙodar tata Allah Ya sa ya ji tausayinsu, ko da kuɗin da ake buƙata wajen yin aikin, ya fi kuɗin da ya yi niyyar bayarwa, ya taimaka ya biya gaba ɗaya. Ya kuma saka a yi aikin cikin nasara.
Wani irin murmushi Yohanah ya saki, yana sauke ajiyar zuciya. Kai tsaye ya shiga office ɗin likitan don yi masa bayanin abin da ya kawo su cikin asibitin. Duk da da farko ba su nuna ba, don sai da ya bari aka karɓi Ameer tukunna, bayan ya ajje kuɗi masu ɗan tsoka kamar yadda yake a tsarin asibitin.

A sanyaye Abeey da ke sanye cikin wata bluen shadda, ɗinkin babbar riga, ya ke takawa zuwa cikin ɗakin. A hankali ya ɗora hannunsa kan hannun ƙofar ya tura. Har lokacin Maama na zaune kusa da ɗanta hannunta na cikin nasa. Yana kwance kan gadon, rabin jikinsa lulluɓe da bargo, ya yin da idanunsa ke a lumshe tamkar mai yin bacci. Ɗaga idanunta Maama ta yi ta kalli Abeey, bayan ta amsa sallamarsa. Ya ƙarasa cikin ɗakin, idanunsa na kallan fuskar ɗan nasa da ta yi fayau, ya ce

"Sannu Tareeq." Ya faÉ—a yana kallansa cike da tausayawa. A hankali ya shiga buÉ—e idanunsa da suka masa nauyi. Ya sauke su a kan Abeeyn, yana sauke numfashi a hankali kamar wanda ya yi aikin wahala.

"Sannu." Maama ta faɗa a hankali. Sai ya jinjina kai yana ƙaƙalo murmushi ya wanzar a kan fuskarsa kafin ya ce

"Yawwah." Ya ƙare har lokacin da murmushin ƙarfin hali a fuskarsa.

"Yanzu dai ba ka isa ka ce mini ka warke na yarda ba. Ka ma daina mini wanna yaƙen. Ni na fi so ko me kake ji ka sanar da ni Tareeq. Ba garin wannan ɓoye abin da ke damunka ɗin ba ne ya janyo haka ba. Ni dai Abeey ka faɗa masa ya daina wannan ɗab'iar tasa, idan da wani abun ya same shi kafin mu ankare fa? Ko kuma abin da ke damun nasa bai fito fili ba ya ci gaba da cin sa a cikin jikinsa fa?" Ta ƙare maganar tana kallan Abeey. Murmushi Abeey ya yi kana ya ce

"Ya isa haka, shi kenan faɗan ya isa haka. Yanzu dai ki yi haƙuri ki.." Kafin ya kai ga ƙarasa maganar, wayarsa ta ɗauki ruri. Ya zube idanunsa a kan wayar, ganin doctor ke kiransa ya sanya shi saurin ɗagawa. Shiru ya yi na tsawon mintina yana saurarar abin da likitan ke faɗa. Suka ɗan yi magana kafin ya ajje wayar. Ya kalli Maama murmushi na tashi a kan fuskarsa ya ce

"Tun kafin a je ko'ina, har an samu yarinyar da za ta sadaukar da ƙodarta gun yaronki." Da matuƙar mamaki Maama ta ce

"Da gaske Yallaɓai? Ita kuwa me take buƙata a rayuwarta wanda za mu iya biyan ta da shi?" Ta tambaya wani irin murmushin farin ciki na tashi a kan fuskarta.

"Abin mamaki, Likitan ya sanar da ni ba ta buƙatar komai." Shiru Maama ta yi tana kallon Abeey cike da mamakin jin furucinsa.

"Ba ta buƙatar komai kuma?" Jinjina kai Abeey ya yi kafin ya ce

"Ya ce ta bayar da ita ne saboda a yi wa ɗan'uwanta da ke kwance cikin asibitin nan addu'ar Allah Ya ba shi lafiya. Ban da wannan ba ta buƙatar ko sisi."

Littafin DANEEN na kuɗi ne, a kan 500. Sai dai daga farko har ƙarshen Book 1 free ne, Book 2&3 shi ne na kuɗi kuma duka a kan 500. Har yanzu kuma muna cikin Book 1 ne, wato (Free pages). Waɗanda za su fara payment yanzu, su tuntuɓe ni ta 08124818273. Waɗanda kuma sai mun gama Book 1 ne za su yi payment, zan saka muku yadda za ku yi a last page na Book 1.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 19

Jinjina kai Maama ta yi cike da mamakin jin abin da Abeey ya faÉ—a. Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce

"Allah Sarki! Amma abin kam da mamaki. Allah Ubangiji Ya saka mata da alkhairi, Ya ba wa É—an'uwanta lafiya."

"Ameen." Abeey ya amsa da hakan, har lokacin annurin fuskarsa yana nan. Tun da Abeey ya fara magana Tareeq yake kallon sa har ya ƙare. A hankali ya ɗan gyara kwanciyarsa lokaci guda yana lumshe idanunsa. Da sauri Maama da ta lura da shi ta taso tana faɗin

"Me ya faru?" Girgiza kansa ya yi lokaci É—aya yana buÉ—e idanunsa. A hankali ya soma faÉ—in

"Abeey wace ce ita? Ina son ganin ta tukunna." Ya faɗa cike da ƙarfin hali.

"Oh Yah Ilahy Tareeq, ka samu ka samu ka yi bacci kafin mu ji abin da Likita zai faɗa." Girgiza kai Tareeq ya yi kafin ya ce bayan ya riƙo hannun Maama.

"Maama ki bar ni na ga wadda za ta ba ni ƙodarta ba tare da wani dalili ba. Ina buƙatar ganin wace ce ita tabbas." Tun kafin ya ƙarasa Maama ta katse shi da faɗin

"Rashin yardarka ya yi yawa Tareeq, har a kan lafiyarka ma?" Ta ƙare tana kallon sa. Iska ya fesar daga bakinsa, ganin da ya yi kwata-kwata Maaman ta ƙi fahimtarsa, lokaci ɗaya kuma yana mayar da jikinsa ya kwantar a kan gadon, har lokacin idanunsa a lumshe.

"Ya isa haka Fatima. Kin fi kowa sanin halin ɗanki, ina ga kuma hakan ba laifi ba ne. Amma dai a halin da kake ciki ka fi buƙatar hutawa, so ka kwanta ka samu ka yi bacci zuwa an jima. Ni da mahaifiyarka za mu yi magana da yarinyar." Jinjina kai kawai ya yi daga inda yake kwance ba tare da ya ce komai ba. Maama ta bi shi da kallo cike da tausayawa. Hannunta ta kai a hankali ta taɓa wuyansa, jin da ta yi zafin ba sosai ba ya sanya ta sauke ajiyar zuciya har cikin ranta tana jin daɗi. Saboda yadda kwana biyu Tareeq ɗin ya din ga fama da matsanancin zazzaɓi mai zafin gaske. Babu daɗewa aka turo ƙofar ɗakin, Sultanah ce da Hidaya cikin dogayen riguna kusan iri ɗaya sai dai ba kala ɗaya ba ne. Da sauri suka ƙarasa inda Tareeq ɗin yake, kowacce jikinta a matuƙar sanyaye.

"Sannu Yah Tareeq." Suka kusan haÉ—a baki wajen faÉ—in hakan. ÆŠan lumshe idanunsa ya yi kaÉ—an kafin ya ce

"Yawwah."

"Wai Yah Tareeq dama ka san da wannan ciwon?" Hidaya ta faɗa kamar za ta yi kuka. Girgiza kai ya yi, yana ɗan ƙaƙalo murmushi a hankali ya ce

"Kaɗan kaɗan.. Ban san abin ya kai haka ba, duk da ina karɓar gwajin lafiyata a kai a kai, ban san lamarin zai yi tsamari har haka ba." Ya ƙare a ɗan gajiye.

"Wallahi Yah Tareeq mun fi ka kula da lafiyarka. Kai dai kawai ciwon a jikinka yake, amma mun fi ka damuwa da shi." In ji Sultanah tana kallon sa. Yanzu kam sai da ya ɗan yi dariya, daidai lokacin da Abeey ya miƙe yana faɗin

"Ya kamata mu yi waje fa haka." Cikin girmamawa duk suka amsa da "Toh." Ba su É—auki lokaci mai tsayi ba gaba É—aya suka fice suka bar shi shi É—aya zuciyarsa cunkushe da tunane-tunane.

Cikin ikon Allah aka gwada ƙodar Daneen, kuma za ya iya cira a saka wa Tareeq. Don haka Likitan ya tsayar da washe-gari a matsayin ranar da za a yi aikin.
Chapter 29 · 0% Book details