Sashe 44
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ehh.." Ya amsa mata da hakan. Ƙarasawa ta yi keɓantaccen wajen da aka ajje masa kujerar da ba a daɗe da kawo ta ba, ta ɗakko ta, ta ƙaraso da ita inda yake. A hankali ta shiga taimaka masa don ganin ya zauna a kan kujerar. Wani irin ƙwarewa Umma da ta zuba ruwa a tambulan tana sha ta yi, ruwan da ta ji ya shige mata har tsakar ka. Ta saka hannunta ta shiga bubbuga kanta har lokacin idanunta a kan Tareeq. Har ba ta san lokacin da ta furta
"Ba ya iya tafiya ne?" Ta faÉ—a tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki na bayyana cikin muryarta. Ba tare da kawo komai a ranta ba Maama ta ce
"Wallahi kuwa, kin ga dai ikon Allah." Wani irin bugawa zuciyar Umma ta shiga yi fat!fat!fat! Ba za ta iya jurewa ba, don haka jiki duk a sanyaye ta ce
"Kenan har tsawon wane lokaci zai É—auka yana zama kan kujerar nan?" Tana ci gaba da taimaka masa É—in dai ta ce
"Har zuwa lokacin da Allah Ya nufa. Su kansu likitocin ba su sani ba, sun dai ba mu tabbacin idan Allah Ya yarda watarana zai iya miƙewa a kan ƙafarsa. Shi ne ma dalilin da ya sa Abeeyn Tareeq yake so a yi auren daga zarar an sallame shi, kin ga daga an ɗaura aure sai Jawahir ta ci gaba da kula da shi."
Wani irin kuka mai ƙarfi Jawahir ta fashe da shi, tana jin yadda ilahirin jikinta ke karkarwa. Kawai sai ta zube a kan gwuiwoyinta tana ci gaba da raira shi. Maama ta kalle ta cike da tausayi, don ta san kukan na tausayin halin da Tareeq ya tsinci kansa a ciki ne. Duk da ba ta sake jin wata magana daga bakin Umma ba, ba ta damu ba, ta shiga tura Tareeq zuwa toilet don ya ɗauro alwala. Shi dai bai ce komai ba, bai kuma nuna alamar yana tare da su ba, duk da yadda cikin zuciyarsa yanayin yadda Umma ta yi magana ya shigar da shi wani yanayi na kokwanto da kuma fargaba. Komawa Umma ta yi kawai ta zauna a kan gado idanunta a kan Jawahir. Shiru ba tare da ta ce komai ba, take ci gaba da kallon ta. Ta kasa furta komai, ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne. Ita ta haifi Jawahir, ta kuma fi kowa sanin halinta. Wannan kukan da take, daga ita Jawahir ɗin, sai kuma ita suka san na mene ne.
Suna yin Sallahr Maghrib suka bar asibitin, bayan sun yi sallama da Maama a gaggauce. Shi dai Tareeq bin su kawai ya yi da kallo, don ba ƙaramin mamaki yanayin yadda suka fita daga asibitin ya ba shi ba. Ita kuwa Maama ba ta kawo komai a ranta ba, ta ci gaba da harkokinta.
... "Toh shi ke nan, amma kin san abin da za a yi?" Maami da ke riƙe da waya kare a kunnenta ta faɗa bayan ta nemi waje ta zauna. Daga can ɓangaren aka ce
"A'ah."
"Kin san halin 'yar taki, ba za ta taɓa yarda da auren haɗi ba. Saboda haka ki turo yaron ya zo da niyyar ya zo gaishe ni, daga nan zan san yadda za a yi su haɗu. Bayan ya tafi sai na sanar da ita ya nemi da a ba shi numberta. Kin fahimci fa'idar yin hakan?" Jinjina kai matar ta yi kamar Maamin na gabanta kafin ta ce
"Ehh, na gane. Hakan kuma ya yi matuƙa, Allah Ya haɗa mana kansu."
"Ameen." Maami ta amsa da hakan. Daga haka ba su ƙara wasu mintuna masu yawa ba, suka yi sallama. Murmushi Maama ta saki tana kallon Maman Abdoul da ke zaune kujerar da ke kusa da tata.
"Barkan ki da wannan lokacin Madam."
"Barka dai Hajiyata.. Wai Sultanah ake nema wa abokin haÉ—i?" Ta haÉ—e gaisuwar da tambayar ta yi su lokaci guda. Jinjina kai Maami ta yi kafin ta ce
"Ita fa. Amma ki yi a hankali kar ta ji. Kin san halin Sultanah."
"Na sani kam. Amma me zai hana tun da ga na gida a tafi wani wajen? Wallahi da mun haɗa ta da Abdoul. Ina son yarinyar wallahi, ko don nutsuwarta." Girgiza kai Maama ta shiga yi kana ta ce bayan ta yi murmushin yaƙe
"A'ah ke kam, wani irin haÉ—i kuma tsakanin Abdoul da Sultanah?"
"Wallahi kuwa ƙawata, na ɗauka kamar sai ya fi koh?" Sake girgiza kai Maami ta yi ta ce
"Toh ai kin ga mun riga mun gama magana da Hajiya Ati, da ba mu yi magana ba sai a yi yadda kika faÉ—a É—in." ÆŠan jujjuya kanta Maman Abdoul ta yi sannan ta ce
"Toh hakan ma ya yi. Allah Ya tabbatar da alkhairi." Sai a lokacin sannan Maami ta saki murmushi tana faÉ—in
"Ameen, ƙawata."
... Gyara zamansa Abeey ya yi, kafin ya É—an sauke ajiyar zuciya. Dukka hankalin 'yan É—akin sai ya dawo gare shi. Sai da ya gabatar da addu'a sannan ya soma faÉ—in
"Wato dalilin haɗa wannan taro da na yi ba komai ba ne, face don na sanar da ku ɗaurin auren Tareeq da za a gabatar da shi ranar juma'ar nan mai zuwa idan Allah Ya yarda. Ba kuma shi da kowa ba face 'yar'uwarsa Jawahir. Muna fatan Allah Ya tabbatar da alkhairi, Ya kuma kaɗe dukkanin abin ƙi. Idan wani na da magana zai iya yi."
"Toh, Allah Ya amsa addu'o'in nan, sannan kuma Ya yi muku albarka gaba ɗaya. Ni kam me ya kamata na ce? Bayan godiya ga Allah. Tun da ga shi jikokina biyu suna ƙoƙarin auren junansu. Allah Ubangiji Ya sanya albarka." Dada ji ta faɗa, har cikin muryarta farin cikin da take jin ta ciki na bayyana.
"Ameen." Maama ta faÉ—a tana murmushi.
Wani banzan kallo Umma take watsa wa Jawahir daga inda take zaune. Duk da sanin halin 'yar tata, amma ko babu komai ta san za ta ji kunyar buɗe baki ta yi magana, musamman saboda kwarjinin Abeey. Amma ya za su yi? Ya zame musu dole su magantu. Ita dai Jawahir ta rasa ta inda za ta fara. Shin me za ta furta kai tsaye ba tare da wani kwane-kwane ba, wanda ko ba ta yi bayani ba za a fahimci abin da take nufi? Tabbas ta san tana son Tareeq, ba kuma don komai ba sai don kyawunsa, kyawun surar da Allah Ya ba shi. Tafiyarsa, komai nasa su ne suke burge ta, ko kuma ta ce su ne take so. Toh yanzu kuma ga shi babu ƙafa, yana zaune ne a kan kujera, ya zama gurgu, mara ƙafa. Kenan me za a kira shi? 'Musaki?' Ta ji zuciyarta ta yi saurin ba ta amsa. Ta runtse idanunta tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da bugawa. Ke nan duk yadda ta tsarawa rayuwarta hakan ba zai yiwu ba? Wato suna nufin ta auri Tareeq a yadda yake a yanzun, ke nan me za ta je yi gidan auren? 'Bauta' Ta sake jiyo hakan a cikin kwanyarta. Tuni har ta fara hasaso kanta a cikin gidan Tareeq. Duk da kayan alatun da ke gidan, ta san muddin ta shiga gidan nan tata ta ƙare. Sai dai ta lalace a banza a wofi wajen kula da nakashashshshen mijin da ake ƙoƙarin liƙa mata. Ita ba ta san da gaske ba shi take so ba, ƙirar jikinsa take so ba sai yanzu. Yadda kuma ta ji zuciyarta ta yi na'am da hukuncin da suka yanke ita da Ummanta ya ƙara tabbatar mata da hakan. Don haka cikin ƙarfin hali, ta tattaro jarumta ta afawa kanta. Ta haɗiye tsoron da take ji, kafin ta runtse idanunta na tsawon wasu sakanni, kana ta buɗe. A hankali ta buɗe bakinta da ƙyar ta soma faɗin
"Abeey don Allah ka yi haƙuri, amma ba zan iya auren Yah Tareeq a halin yanzu ba." Gaba ɗaya mutanen ɗakin kallon ta suke yi cikin matuƙar tashin hankali, idan ka cire Umma. Cikin matuƙar mamaki Maama ke ci gaba da kallon ta, tana jin abin kamar wani wasan yara. Cikin ƙarfin hali ta furta
"Jawahir, kin san me kike faɗa kuwa?" Ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye, wanda ya ja har muryarta ma a sanyayen take. Shiru Jawahir ta yi, ta kasa ɗaga ido ta kalli Maaman. Sam Maama ba ta yi tunanin za ta sake jin wata magana daga bakin Jawahir ba, duk kuwa da ita ta tambaye ta. Amma sai ta ji ta ce
"Eh Maama. A yi haƙuri don Allah."
Wani irin kallo Sultanah da Hidaya suke bin Jawahir da shi. Gaba ɗayansu sun kasa furta komai. Ganin abin suke kamar almara, ko kuma shirin film. Anya kuwa Jawahir ɗin ce? Jawahir dai Jawahir masoyiyar Yah Tareeq? Cike da ƙarfin hali, da kuma ƙaryata abin da kunnuwanta suka jiye mata Dada ji ta ce bayan ta sauke duka idanunta a kan Umma.
"Maimunatu, kin ji abin da yarinyarki take faÉ—a kuwa?"