Sashe 33
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ameer ka tashi ka ƙaryata abin da mutumin nan yake faɗa, ka tashi ka yi mini magana Ameer. Ameer don Allah kar ka tafi ka bar ni, kar ka yi mini haka Ameer. Ya ya zan yi da rayuwata idan ya zama babu kai? Mai zan koma na cewa Inna idan ka yi mini haka? Don Allah idan wasa kake yi ka tashi Ameer. Me ya sa zuciyarka ba ta da juriya ne Ameer, me ya sa ka koyi rashin juriya bayan a da kai ne me juriyar. Yanzu ni za ka yi wa haka Ameer? Tafiya ka yi ka bar ni a wannan duniyar Ameer?" Daneen ta faɗa cikin gigitaccen kuka tana girgiza kanta. Idanunta har wani hazo-hazo take gani saboda tsabar kuka.
"Ka tashi Ameer, ni ce fa nake ce maka ka tashi, wai so kake su sake ce mini ka mutu? Ameer me ya sa za ka yi mini haka?" Ta ƙare maganar tana kifa kanta a ƙirjin Ameer, ta shiga girgiza kanta tana fidda wani irin sautin kukan da ke fitowa tun daga can ƙarƙashin zuciyarta. Hannu Hidaya ta kai ta riƙo Daneen, duk da yadda ta kasa ko gezau ne ta ƙi ɗaga jikin Ameer, hakan bai hana Hidaya yin iya ƙoƙarinta ba wajen ɗago ta. Sai kuwa ta faɗa jikinta tana fashewa da sabon kuka, mai tsuma zuciyar mai sauraro. Kuka take irin kukan nan da ke fita haɗe da zafin da ɗan adam ke ji a cikin zuciyarsa.
"Kin ga ya ƙi kula ni koh? Ya ƙi yi mini magana don in yarda da abin da wancan mutumin ya faɗa. Me ya sa Ameer zai mutu ya bar ni? Bai san yadda nake ƙaunarsa ba ne?" I zuwa lokacin Hidaya kasa jurewa ta yi, kawai ita ma sai ta fashe da kukan tana saka hannunta ta dafe kan Daneen da ke kan kafaɗarta. Wani irin tausayin Daneen ɗin na ci gaba da ratsa ta. Nauyin da ta ji ne a jikinta ya sanya ta kai hannunta ta goge hawayen kan fuskarta, daidai lokacin da Sultanah ke faɗin
"Hidaya kamar ta suma fa?" Ta ƙare maganar kamar mai tambaya. Likitan da kansa ya yi kiran nurses aka zo aka fitar da Daneen ɗin da ta fice a hayyacinta gaba ɗaya daga cikin ɗakin. Duka suka bi ta da kallo ba tare da kowa ya ce komai ba.
Lokacin da su Maama suka ji labarin rasuwar Ameer ba ƙaramin tashi hankalinsu ya yi ba. Kusan gaba ɗaya suka ɗauki salati, cike da tausayin Daneen ɗin da wasu daga cikinsu ke kallon ta tamkar 'yar'uwarsu, tun lokacin da ta sadaukar da wani abu daga jikinta zuwa Tareeq.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Tareeq ya faɗa yana runtse idanunsa. Haƙiƙa tabbas ya ji mutuwar yaron, duk da bai taɓa ganinsa ba sai labarinsa. Ita kanta wadda ta ba shi ƙodar har yanzu bai taɓa ganinta ba, duk da yadda yake so ya haɗu da ita ya ga wace ce ita, sannan kuma ya yi mata godiya a bisa wannan sadaukarwar da ta yi. Sai ga shi lokaci guda ana faɗin ɗan'uwan nata da take komai saboda shi ya rasu.
"Ubangiji Allah Ya gafarta masa." Ya faÉ—a yana jin har zuciyarsa babu daÉ—i.
"Ameen Ya Rabbi. Allah Sarki yarinyar nan, wallahi tausayi take ba ni, tana matuƙar ƙaunar yaron, ko awa ɗaya ka zauna da ita sai ka fahimci irin ƙaunar da take wa yaron. Ashe ɗazun sallama ta je su yi, kai ya ilahil alameen ka gafarta wa yaron nan, wai ƙaramin yaro da ciwon zuciya." Dada ji ta faɗa jiki a sanyaye.
"Ciwon zuciya?" Tareeq ya faÉ—a cike da mamaki. Jinjina kai Dada ji ta yi kafin ta ce
"Wallahi kuwa, ai a kan hakan ma aka yi masa aiki. Ashe ashe ma ba zama zai yi ba."
"Ikon Allah! Allah Ya gafarta masa." Tareeq ya faÉ—a shi ma jikin nasa a sanyaye.
Hidaya ce take zaune a É—akin da Daneen ke kwance, ta kwashi fiye da awa uku kafin ta farka.
"Ameer." Nan ma da abin da ta farka kenan. A kan laɓɓanta Hidaya ta furta
"Ya Allah." Tana miƙewa ta ƙarasa kan gadon.
"Me nake a nan? Ina É—an'uwana yake?" Ta faÉ—a a zabure tana kallon gefe da gefen ta.
"Ki yi haƙuri ki zauna Daneen, don Allah ki yi haƙuri." Girgiza kai Daneen ta shiga yi, daidai lokacin da wasu sabbin hawaye suka fara zubowa sharr sharr a kan kuncinta.
"Shi kenan Ameer ɗina, zuciyata zafi take yi mini, ina jin tamkar za ta fito daga ƙirjina, ta ya ya zan iya jure rashin ɗan'uwana rabin jikina? Wai Ameer ne ya rasu? Ameer fa, ya rasu? Ya tafi kenan ya bar ni? Ba zan sake ganinsa ba, ba zan sake jin maganarsa ba? Ba za mu sake zuwa makaranta tare ba? Ba za mu sake fita kasuwa tare ba? Dada ba za ta sake saka mu aiki tare ba? Ba za mu sake yi wa Innarmu aiki tare ba? Ba zan sake ganinsa yana dariya ba? Ba zai sake zama kusa da ni yana ba ni labari ba, ba zai sake ɗora kansa a kan kafaɗata ya yi kuka ba, ya sanar da ni matsalarsa, ya kira ni Addarsa. Ashe ɗumbin ƙaunar da nake masa ta ƙanƙanin lokaci ce, ashe ba za mu daɗe da shi ba? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Ya Allah Ka sassauta mini abin da nake ji, zuciyata za ta iya tarwatsewa. Wayyo Ameer ɗina." Ta ƙare maganar lokacin da wani sabon kuka ya ƙwace mata. Jikin Hidaya ne ya ƙara yin sanyi, ta shiga share hawaye saboda yadda maganganun Daneen ɗin suka sake jefa ta cikin tausayinta matuƙa.
"Ki yi haƙuri." Shi ne abin da ta iya faɗa a sanyaye. Daidai lokacin da Likitan ya ƙaraso cikin ɗakin, ba tare da ya ce komai ba, ya ƙarasa haɗa allurar hannunsa. Ya yi wa Hidaya alama da kansa, miƙewa ta yi ta ƙarasa inda Daneen take ta riƙe ta, da taimakonta ya yi wa Daneen wadda ke shirin soma magana allura. Wani irin runtse idanunta ta yi na tsawon sakanni, maganar da ta kasa fitowa kenan. Kawai sai ta koma ta kwanta a kan gadon numfashinta na fita da sauri da sauri, A hankali ta ji wani irin bacci na fizgarta, lokaci guda tasirin baccin ya yi nasarar danne duk wani abu da take ji, don haka cikin ƙanƙanin lokaci wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. Kusan a tare Doctor Adam da Hidaya suka sauke ajiyar zuciya, ya kalli Hidaya ya ce
"Na yi mata allurar bacci don tana buƙatar ƙwaƙwalwarta ta huta, idan ba haka ba za a iya samun matsala. Ki kula da ita."
"In Sha Allah." Hidaya ta faÉ—a tana jinjina kai. Daga haka ya fice daga É—akin, ya yin da ta ci gaba da zama idanunta a kan Daneen É—in cike da matsanancin tausayinta.
... "Daneen." Hidaya ta faɗa da sauri tana ƙarasawa inda Daneen ɗin ke tsaye, bakin ƙofa tana ƙoƙarin fita daga ɗakin.
"Ina za ki je?"
"Wajen Ameer." Ta ba ta amsar tana kallon ta.
"Ya Ilahy." Hidaya ta faÉ—a tana dafe goshinta.
"Ina so ne kawai in sake kallon fuskarsa, duk da na san ba magana zai yi mini ba." Sai a lokacin sannan Hidaya ta sauke ajiyar zuciya jin abin da Daneen É—in ta faÉ—a.
"Amma dai ya kamata ki je ki É—an huta tukunna."
"Uhmm.. uhmm." Ta faɗa tana girgiza kai, ta lumshe idanunta tana jin yadda kanta ke juyawa kamar zai rikito ƙasa. Ganin haka ne ya sa Hidaya ta bi bayanta. Har ɗakin da Ameer ke ciki Daneen ta shiga, sai dai ga mamakinta babu kowa a ciki, ta ƙarasa tana sake duddubawa hankali a tashe.
"Ina suka kai mini ɗan'uwana?" Ta tambaya a razane, lokacin da ƙwalla ta kawo idanunta.
"Bari na kira miki Likita." Hidaya ta faÉ—a tana ficewa daga É—akin. Bin ta da kallo kawai Daneen ta yi kamar wata doluwa, har zuwa bayan wasu mintina Doctor Adam ya shigo cikin É—akin. Muryarta har rawa take lokacin da ta furta
"Ina Ameer? Ina É—an'uwana yake?"
"Ɗan'uwanki Yohanah ya karɓi gawarsa. Mun yi duk wasu abu da ya kamata lokacin kina bacci, ba zai yiwu kuma a jira ki ba saboda ba bacci ne mai ƙarewa da wuri ba, shi ya sa ma ya karɓe shi kawai." Wani irin bugawa da zuciyarta ta yi, shi ne ya sanya ta saurin kai hannunta kan ƙirjinta tana lumshe ido, kawai sai ta koma ta yi yaɓar a kan gadon, daidai lokacin da wani irin jiri ya soma ƙoƙarin kayar da ita, duk kuwa da a zaune take.
"Thank god, zo ka yi magana da ita." Doctor Adam ya faɗa yana kallon Yohanah da ya shigo cikin ɗakin. Babu ɓata lokaci kuma ya fice bayan sun gaisa da Yohanah.
"Daneen." Yohanah ya faɗa yana ƙarasawa inda Daneen take, sai a lokacin ta iya ɗaga idanunta da suka yi mata wani irin nauyi ta kalle shi, tun kafin ya ce komai ta ce
"Ina ka kai mini ƙanina?" Sai sa ya fesar da iska daga bakinsa sannan ya ce
"An binne shi." Amsawar da ciwonta ya yi, shi ne ya tuna mata akwai É—anyen aikin da ba a daÉ—e da yi mata shi ba. Ta runtse idanunta tana girgiza kai. Kafin a hankali ta É—aga su ta kalle shi, muryarta na karkarwa ta ce
"Ameer musulmi ne, kai kuma ba musulmi ba ne." Girgiza kai Yohanah ya yi kafin ya ce
"Kar ki damu, wajen wani maƙocina na kai shi, shi ya yi masa komai na musulmai." Kukan da take ta ƙoƙarin dannewa shi ne ya ƙwace mata, ta zube a wajen tana soma raira shi. Shi kenan Ameer ya tafi ya bar ta, shi kenan da gaske ita da Ameer sai dai a lahira. Kwata-kwata ta kasa cewa komai, sai kukan da take gaba ɗaya jikinta na wani irin rawa.