← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 49

Sashe 42

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na gode." Shi ne abin da ya iya furtawa kawai, daga haka ya miƙe ya miƙa masa
hannu kana ya juya ya fice daga office ɗin. Bin sa da kallo Likitan ya yi, yana jin wani irin tausayinsa da na ɗan nasa na kama shi. Kai tsaye Abeey ɗakin da Tareeq ke ciki ya nufa. A hankali ya tura ƙofar ɗakin har lokacin jikinsa a matuƙar sanyaye. Har zuwa lokacin Maama tana zaune gefen ɗan nata. Ya ƙarasa a sanyaye bakinsa ɗauke da Sallama, ya ja kujera ya zauna daidai lokacin da Maama ke amsa sallamar tasa. Gaba ɗaya idanunsa na kan Tareeq da sai a lokacin ya amsa sallamar Abeeyn, saboda yadda hankalinsa ya ɗan yi wani wajen.

"Tareeq." Abeey ya ambaci sunansa.

"Na'am Abeey." Ya amsa yana kallon sa. Sai da ya kalli ƙafarsa kafin ya ce bayan ya maida duban sa kan Tareeq ɗin.

"Ya ƙafar taka? Ya kake jin duka jikinka?" Shiru Tareeq ya yi na ɗan wasu sakanni, yana nazarin abin da ya kamata ya ce. Don kuwa idan har gaskiya zai faɗa, toh ba zai iya kwatanta abin da yake ji a cikin ƙafarsa ba. Ya ɗan sosa goshinsa a nutse kafin ya ce

"Alhamdulillahi Abeey, da sauƙi." Murmushin yaƙe Abeey ya yi, a ransa yana ji ina ma a ce hakan ne. Domin kuwa, daga yanayin yadda Tareeq ɗin ya yi magana za ka fahimci kawai ya faɗa ne.

"Allah Ya ƙara lafiya Tareeq. In Sha Allah za ka samu lafiya, kamar ba ka taɓa yin ciwo ba." Jinjina kai ya yi yana murmushi, lokaci ɗaya yana gyara zamansa saboda ciwon da ƙafarsa take ya ɗan motsa. Maama ce ta amsa da "Ameen." Ya yin da shi kuma ya sake kwantar da kansa gefe idanunsa a lumshe.

.... Kallon ta kawai Umma take, duk lokacin da ta shigo ba tare da ta ce da ita ko uffan ba. Ita ma ba ta ce wa Umman komai ba, fita kawai take yi, ta É—auko kayan ta shigo da su sai kuma ta sake fita. Har zuwa lokacin da ta dawo cikin É—akin ta zauna jagab a kan kujera tana faÉ—in

"Washh.." Ta yi maganar tana zame hular kanta idanunta a lumshe. Sai a lokacin sannan Umma ta ce, bayan ta É—auke duban ta daga kan kayan zuwa kan Jawahir.

"Jawahir, waÉ—annan kayan fa?" Ta faÉ—a tana nuna su. BuÉ—e idanunta Jawahir ta yi ta kalli kayan, sannan ta gyara zamanta a kan kujerar ta ce

"Umma kayan kitchen ne fa." Ta ƙare maganar tana turo baki.

"Iyeeee, yau na ga ikon Allah. Wai Jawahir me ye haka ne? Ba za ki iya haƙuri cikin satin nan na je na siyo miki duk abin da kike buƙata ba?" Sake tura bakinta ta yi kafin ta ce

"Toh Umma ba ga shi na rage miki wasu abubuwan ba. Kuma ma na ga har yanzu kin ƙi zuwa, bayan bikin saura 'yan kwanaki." Dariya Umma ta yi tana girgiza kai. 'Wato a kan Tareeq Jawahir ba ta da kunya.' Ta raya hakan cikin zuciyarta. Ya yin da a fili kuma sai cewa ta yi

"Toh ya yi, sai ki tashi ki shigar da su ciki ki wuce mu je mu duba jikin Tareeq." A razane ta ce

"Jikinsa kuma? Me ya faru da Yah Tareeq É—in?" Ajiyar zuciya Umma ta sauke kafin ta ce

"Ba ki ga missed call É—ina a wayarki ba? Wallahi ya samu hatsari ne."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Na shiga uku? Amma dai babu abin da ya same shi?" Ta tambaya a ruÉ—e idanunta a kan Umman.

"Tashi mu je." Umma ta faɗa tana miƙewa. Ko sake bi ta kan kayan ba ta yi ba, ta ɗauki jakarta ta zura a hammata, har tana riga Umman ma ficewa daga ɗakin.

A cikin satin aka yi wa Tareeq aiki a ƙafarsa, aikin da cikin ikon Allah aka dace matuƙa yadda ba su yi tsammani ba. Don haka cikin farin ciki Likitan da ya jagoranci aikin yake miƙa wa Abeey hannu fuskarsa ɗauke da murmushi yake faɗin

"Congratulations Sir, an yi aiki cikin nasara In Sha Allah." Cikin wani irin farin ciki Abeey ya miƙa masa hannu suka gaisa, fuskarsa na nuni da irin farin cikin da yake ciki.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah." Shi ne abin da Abeey ya din ga faÉ—a. Likitan bai tari numfashinsa ba, sai da ya gama sannan ya ce

"Sai dai za a ɗan ɗauki lokaci gaskiya kafin ya iya taka wa da ƙafar tasa. Ina nufin za a samar masa kujera ne ya din ga duk wasu abubuwa da zai yi a kai. Aikin ƙafa kam an yi nasara, amma ba yanzu zai iya takawa ba, sai zuwa lokacin da Allah Ya nufa, amma fa a yadda muka ga ƙafar tasa, muna kyautata zaton nan ba da daɗewa ba ne In Sha Allah." Jinjina kai Abeey ya yi, duk da yadda ya ji jikinsa ya yi sanyi. Amma kuma idan ya tuna inda Allah Ya taimake su aka yi aikin lafiya sai ya ji sanyi a ransa. Godiya sosai ya yi wa Likitan da ya yi ta sinnar da kai cike da kunyar jin Alhaji Dikko guda na yi masa godiya haka tamkar wanda ya yi masa wani babban abu na musamman.

Ta ɓangaren Daneen kuwa abubuwa sun cakuɗe mata, domin kuwa idan dai har tana lissafi daidai, yanzu haka saura sati ɗaya bikin Tareeq. Don haka gaba ɗaya ta ruɗe, duk wata hanya da za ta sada ta da ɗaki, wajen ajiyar kayan Tareeq kawai shi take nema. Sau da dama ta kan faki idanun mutane ta je sashen nasa, sai dai kamar kodayaushe a kulle dai. Ga shi kusan kullum suna asibiti. Babu damar ta ce ba za ta je ba, don tana tsoron kar a zargi wani abun.

.... "Sannu Yah Tareeq." Hidaya ta faɗa a karo na barkatai. Murmushi Tareeq ya yi har fararen jerarrun haƙoransa na bayyana kaɗan.

"Hidayaaaa.." Ya ɗan ja ƙarshen sunan, jin yadda motsi kaɗan sai ta ce masa sannu. Murmushi ta yi kana ta ce

"Na'am Yah Tareeq."

"Na warke fa." Ya faɗa yana ɗan gyara zaman ƙafarsa.

"Allah Ya sa." Ta faÉ—a a sanyaye. A hankali ya É—an kalli gefensa kafin ya maida duban sa kanta ya ce

"Ina Daneen?" Da mamaki shimfiɗe a kan fuskarta ta ɗaga kai ta kalle shi. Tana matuƙar mamakin yadda yake iya kula da rayuwar Daneen ɗin, sosai da sosai yake barin ta da mamaki ya kusan kashe ta. Yadda ya haddace sunanta cikin ƙanƙanin lokaci, yana ɗaya daga cikin abin da ke matuƙar ba ta mamaki. Sai dai abin da ba ta sani ba, kula da rayuwar Daneen ya zama dole a wajensa. Ko babu komai yanzu haka rayuwa take a cikin gidansu. Ya zama dole ya saka wa duk wani takunta ido. Duk yadda aka yi ma Hidaya manta halinsa ta yi. Gefe guda kuma take-taken yarinyar bai yi masa ba. Dalili kenan da ya sa yake lura da duk wani motsinta.

"Yah Tareeq.." Ta ambata cike da mamaki ba tare da ta ba shi amsar tambayar da ya yi masa ba. Sarai ya fahimci abin da take nufi, don haka ya saki wani miskilin murmushi da ya matuƙar ƙawata fuskarsa kafin ya ce

"Ba ni amsa ta." Ya faɗa cikin basarwa. Kafin ta kai ga cewa komai, Daneen ta yi sallama cikin ɗakin kanta a ƙasa kamar wata munafuka. Dukkan su suka bi ta da kallo, kafin Tareeq ya janye nasa idanun. Ga maɗaukakin mamakinsa, abin da bai taɓa ji daga bakin yarinyar ba, sai ga shi ta ce

"Barka da wannan lokacin." Kusan a tare shi da Hidaya suka sake kallon kyakykyawar fuskarta da har zuwa lokacin ba ta ɗaga ta ta kalle su ba. A karo na biyu ya sake janye idanunsa yana ɗan taɓe bakinsa, kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce

"Barka dai. Ya jikinki?" Har ta É—aga kai za ta kalle shi, sai kuma ta fasa, don so take duk wani zargi da ta fara karanta a kan fuskarsa ya fice masa a rai. Don haka so take ya É—auka kunya ce da rashin sabo ke hana ta gaishe shi, ko kuma yi masa ya jiki, duk da yadda shi ba ya gajiya, a kullum idan za su haÉ—u sai ya yi mata ya jiki, duk kuwa da ta warke, sai É—an abin da ba a rasa ba.

"Alhamdulillah. Ya jiki?" Ta yi ƙarfin halin faɗar hakan, a yanzu tana kallonsa. Ba tare da ya kalle ta ba ya amsa da "Alhamdulillah." Daga haka gurin ya ɗauki shiru. Ita dai Hidaya kallon su kawai take yi su duka kamar ta samu T.V. Sai zuwa can sannan ta ce

"Sister ki zo ki zauna mu yi hira." Murmushin nan na yaƙe, wanda ake cewa ya fi kuka ciwo Daneen ta saki tana girgiza kanta. Da ƙyar ta iya furta

"A'ah, bari na É—an je waje." Ta yi maganar tun kafin ma Hidaya ta ce komai ta fice daga É—akin. Hidaya ta bi ta da kallo tana murmushi kafin ta maida duban ta kan Tareeq.

.... Shiru Maama da Dada ji suka yi, bayan da suka gama sauraron bayanin Abeey duka. Bayan wajen shuÉ—ewar mintina biyu sannan Maama ta ce

"Yanzu ya za a yi kenan?" Ta tambaya a sukwane. Ajiyar zuciya Abeey ya sauke kana ya ce

"Toh! Ni dai ban yanke komai ba. Amma abin da yake akwai kawai shi ne aurensa da Jawahir za a yi cikin satin nan kar a fasa. Idan ya so kin ga faÉ—uwa ta zo daidai da zama, sai ta ci gaba da kula da shi. Amma ya kika ce Dada ji?" Cikin na'am da zancen Abeey Dada ji ta ce
Chapter 42 · 0% Book details