← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 49

Sashe 2

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.. Cike da damuwa ta ɗauki Daneen ta taɓa jikinta da ya yi zafi zau kamar wuta. Ta runtse idanunta tana jin duk jikinta babu daɗi, ƙirjinta har wani bugawa yake saboda tsoro. Kuka yarinyar ke yi sosai, Inna-wuro na rarrashinta. Tun tsakiyar dare har sai wajen asuba kafin zazzaɓin ya sauka. Sai a lokacin sannan wani wahalallen bacci ya kwashe ta. A hankali ta sauke ajiyar zuciya tana kafe Daneen da idanunta. Tausayinta na kama ta. Addu'a ta karanto ta tofe ta da ita, ta ɗan ja zani ta sake lulluɓe ta da shi tana addu'ar Allah Ya sa kar zazzaɓin ya sake dawowa.

.. Dada na tsakar gida tana dama kunu lokacin da ta fito daga cikin ɗakin, Baffa kuma na kan kujera suna hira da Dadar. Ƙarasawa ta yi a hankali ta tsuguna, ta gyara kwanciyar Daneen da ke hannunta ta ce

"Baffa don Allah alfarma nake nema a wajen ku." Ta faɗa tana jin ƙirjinta na bugawa, duk wani fatanta a ce su amince da abin da za ta faɗa. Ba tare da ya ce komai ba ya ɗaga kai ya kalli Dada da ta juyo tana kallan Inna-wuro.

"Me ya faru?" Dada ta faɗa cikin tsare gida. Sauke numfashi ta yi tana tunanin ta inda za ta fara. Sai dai ta yi ƙarfin halin soma faɗin

"Don Allah Dada ku taimaka ku kira mini shi a samu a kai yarinyar nan asibiti. Wallahi kullum da zazzaɓi take kwana cikin dare. Kun ga har ta fara ramewa wallahi." Ta ƙare tana sauko da Daneen daga kan kafaɗarta. Ba tare da kowannen su ya ce komai ba, Dada ta kai hannu goshin yarinyar ta taɓa. Ta ja tsaki kafin ta soma faɗin

"Maƙaryaciyar banza, ina zazzaɓin yake a nan? Kina jin jikin yarinya sanyi ƙalau ki ce zazzaɓi? A'ah asibiti ne a kanta." Girgiza kai Inna-wuro ta yi ba tare da ta kalli Dada ba ta ce

"Wallahi da gaske nake Dada. A kwanakin nan kullum cikin dare da shi take kwana, ko bacci ba ta iya wa sai ya sauka. Toh ina tsoron kar wani abu ya faru kuma."

"Ki ji nemawa kai bala'i kuma.." Dada ta faɗa tana riƙe haɓa.

"Kin ga ke.. Inna-wuro, maza koma ɗaki ki zauna tun da dai babu zazzaɓin. Yoh ki je ma ki cewa likitocin me tun da babu zafi jikinta? Ki zauna duk sanda zazzaɓin ya dawo sai a san abin da za a yi." Baffa da tun ɗazun be ce komai ba ya faɗi hakan. Ba ta sake cewa komai ba, sai miƙewa da ta yi a sukwane, jikinta a matuƙar sanyaye ta saɓa Daneen a kafaɗarta ta wuce ɗakinta.

"Ko dai a kira shi a ji ta bakin nasa ne?" Baffa ya faÉ—a bayan ya ga shigar Inna-wuro É—aki. Da sauri Dada ta juya ta kalle shi

"Wai ni kam manta yadda aka yi da shi ka yi? Dududu kwana nawa ya rage ta bar gidan nan? Idan mun yi haƙuri da kansa fa ze zo ba sai mun kira shi ba. Kamar yadda aka yi da shi wata biyu ciff bayan haihuwar, ina da tabbacin ba ze ƙara ba. Toh ni dai kar na sake jin kana wani zancen kiransa. Mu kira shi mu masa me? A'ah don Allah."

"Toh shi kenan Uwar gida, ai komai kika ce ya zauna." Ya ƙare yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi tana maida hankalinta kan kunun da ke hannunta a cikin kofi.

.. Cikin ikon Allah kwanakin da suka biyo baya Daneen ba ta sake kwana da zazzaɓin ba. Farin ciki kamar me haka Inna-wuro ta ji, ta din ga gode wa Allah tana cigaba da kula da 'yarta. Bayan wasu kwanaki ga maɗaukakin mamakinta sai ta ga Dada da kanta ta soma gyara ta. Magunguna kala-kala, da na sanyi da na gyara jiki haka ta din ga ba ta. Ita dai jiki a sanyaye haka take bin Dadar, don ba kirki ne da ita ba. Ba ta ƙi ta ci mata cin mutunci ba a kan ko mene ne.

... Tana zaune a cikin ɗakin, hannunta ɗauke da Daneen da ta yi wayo sosai. Ta ƙara kyau, jikinta ya murje matuƙa. Ita kanta Inna-wuron ta ƙara wani irin kyau, don sosai jegon ya karɓe ta, ta murje ta yi kyau abinta. Tun ɗazu take jiyo hayaniya daga tsakar gida, sai dai ba ta yi ko da yunƙurin fita ba ne, tana cikin ɗakin tana hira da ɗiyarta.

"Inna-wuro! Inna-wuro." Ta jiyo muryar Baffa daga tsakar gida. Da sauri ta miƙe, sai dai cike da takatsantsan, saboda Daneen da ta fara bacci. Ta kwantar da ita a hankali tana sake jin kiran da Baffa ya yi mata har cikin kanta. Cikin ruɗewa ta amsa tana miƙewa ta fice, hannunta ɗauke da ɗankwalin atamfar jikinta.

"Na'am Baffah." Ta sake faɗa daidai lokacin da gama fitowa daga ɗakin. Mummunan ganin da ta yi, shi ne ya sanya ta dakatawa. Take zuciyarta ta soma harbawa lokacin da idanunta suka sauka a kan Alhaji Baita, da ke zaune kan wata kujera, ya yi shirim. A ƙalla a shekaru ya ba wa 40 baya. Don a haife ya haifi Inna-wuro, wadda take da shekaru 18. Sai dai ba kowa ba ne shi, face mijinta, mahaifin abin da ta haifa. Mutumin da kwata-kwata ba ta so ƙara ganin fuskarsa a rayuwarta ba, ko don saboda nunawa da ya yi ƙiri-ƙiri ba ya son abin da ta haifa. Sauke idanunta ta yi ƙasa, tana ji duk jikinta na yin sanyi, ko'ina na jikinta ya ɗauki rawa. Ba ta san lokacin da ta zube a wajen ba, tana jin wata irin ƙwalla na taruwa a cikin idanunta. Shi kuwa Alhaji Baita, tun da Baffa ya soma kiran sunan Inna-wuro ya kafe ƙofar ɗakin da idanunsa, har zuwa lokacin da ta fito. Ya kafe ta da jajayen idanunsa, gaba ɗaya hankalinsa na tafiya kan jikinta. So yake ya ga ko akwai wani canji da ze gani a jikinta. So yake ya ga ko ta sauya daga ainahin Fatima, me kyau, me diri, wadda ta haɗa duk wani abu da yake buƙata a wajen mace. Don kuwa ko daidai da canji ɗaya ya gani a jikinta, ko raguwar kyawunta, ko kuma yamutsewar wani sashe na jikinta, toh tabbas a wajen zai sakar musu 'ya ba tare da an je ko'ina ba. Wannan rawar jikin da duk wani abu da suke ba ze yi tasiri a wajensa ba...

Toh Alhamdulillah, bayan wani lokaci yau Allah Ya sake haɗa mu cikin wannan tafiyar, fatan za ku karɓi wannan labarin da hannu bibbiyu kamar yadda kuka saba. Ina faɗa muku zazzafar tafiya ce, me tsaya wa a rai. 😍❤️

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 02

__ Sai dai ga maɗaukakin mamakinsa, sai idanunsa suka ganar masa tamkar ma sauya masa Fatiman aka yi. Ta ƙara kyau, ta wani irin murje. Duk da da ma Fatiman ba baya ba ce wajen kyawun jiki, amma yanzun ta ƙara cika ta ko'ina. Ya saki murmushi har lokacin ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta. Hannunsa ya kai ya shafa kumatunsa kafin ya lumshe idanunsa yana sauke wani gajiyayyen numfashi.

"Ina kwana?" Inna-wuro ta yi ƙarfin halin faɗin hakan, saboda wata uwar harara da Dada ke jefa mata kamar idanunta za su faɗo ƙasa.

"Ahh lafiya ƙalau Fatima." Ya faɗa yana murmushi, kafin ya ɗora da faɗin

"Ya kamata mu tashi mu tafi koh?" Ya ƙarasa maganar har lokacin yana kallan Inna-wuro. A hankali ta ɗaga idanunta da suka yi laushi ta kalli Baffah, sai dai maimakon idanunta su faɗa cikin na Baffah sai suka faɗa cikin na Dada. Tana shirin kautar da kanta ta jiyo muryar Dada na faɗin

"Ai kam dai ya kamata.. Ka ganta nan ta yi kyau abinta, ai tun jiya na gama gyare maka ita tass, kawai tafiya za ku yi babu wani ɓata lokaci. Malam ɗakko kayan Inna-wuro da na shirya mata cikin jaka." Kallon Baffahn da ya tashi zungwui-zungwui Inna-wuro ta yi, tana mamakin jin wai har an haɗa mata kaya amma duk ba ta sani ba. Toh yaushe? Kuma tana ina hakan ta faru?

"A'ah, dawo ka yi zaman ka. Ba sai an ɗauko komai ba, ni da ma Fatima na zo ɗauka ba wani abu ba." Alhaji Baita ya katse Baffa daga yunƙurin shiga ɗaki da yake. Sai ya juyo yana faɗin

"Kai dai kullum ba ka gajiya da ɗawainiya. Toh madallah." Ya ƙarasa maganar yana murmushi, lokaci guda kuma yana neman waje ya zauna. Miƙewa Alhaji Baita ya yi yana gyara zaman babbar rigar jikinsa, ya saka hannu ya zaro kuɗi a aljihunsa ya dire a gaban Dada yana faɗin

"Ta same ni a mota." Daga haka ya juya don ficewa daga gidan. Cikin farin ciki Dada take faÉ—in

"Mun gode sosai, Allah Ya saka da alkhairi, Ya ƙara arziƙi." Be ce komai ba ya fice daga gidan. Sai a lokacin Baffa ya kalli Inna-wuro ya ce

"Maza tashi ki wuce ku tafi, kar ki bar shi yana jira." Idanunta ta ɗaga ta kalli Baffa, kallo irin wanda take fata ya ji tausayinta, ya kalle ta da idon mahaifi, ya kalle ta da soyayyar mahaifi, ya kalle ta da wannan tausayin da yake kallan ta da shi tun haihuwarta, soyayyar nan tata da ta ƙaru a wajensa tun da ta rasa mahaifiyarta. Sai dai kashh, wannan kallan ya daɗe da zama tarihi. Wannan tausayin ya daɗe da zama shuɗaɗɗe. Baffan da take gani yanzu zaune a gabanta ba halinsa ɗaya da Baffanta na da ba.
Chapter 2 · 0% Book details