Sashe 25
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ameen Abeey." Ya faɗa yana miƙewa. Sallama ya yi da duka mutanen ɗakin kafin ya fice. Kai tsaye sashensa ya wuce, ya ɗauki abin da ze ɗauka ya fice daga gidan. Ba shi ya dawo cikin gidan ba, sai bayan ƙarfe 12pm. Don haka ruwa kawai ya watsa ya kwanta don yadda idanunsa ke buƙatar bacci.
... "Idan da zaɓi za ka ba ni, toh tabbas zan nemi soyayyar Hidaya ne, saboda Sultanah mahaifiyarta duk da kasancewarta aminiyar Ummeey ina shakkar ta wallahi." Abdoul ya ƙare yana shafa kansa. Dariya Tareeq ya yi jin abin da ya faɗa. Ya ja siririn tsaki kafin ya ce
"Amma dai ka ba ni kunya Abdoul.. Amma dai ba wannan ba, ni nan ni ne amininka, kuma ina mai ba ka shawara da ka nemi Sultanah saboda ta fi Hidaya sauƙin kai. Abeey dai shi zai aurar da Sultanah ba Maami ba, idan kuma ba shi ba ni ne. Don haka kar ka ji komai, duk da ma Maami na da kirki wani lokacin, amma fa idan ka fahimce ta." Jinjina kai Abdoul ya yi irin a yatsinen nan, cike kuma da rainin hankali ya ce
"Ehh, haka fa." Wani murmushi Tareeq ya saki ba tare da ya ba wa yanayin Abdoul É—in muhimmanci ba ya ce
"Uhmm." Gyara zama Abdoul ya yi, bayan ya sauke ajiyar zuciya ya ce
"Ka tabbatar?" Jinjina masa kai Tareeq ya yi ba tare da ya ce komai ba. Don haka Abdoul ya ce
"Shi kenan, zan gwada.. Allah Ya ba ni sa'a." Ya ƙare irin a marairaicen nan. Cike da jin daɗin yadda burin ƙanwar tasa ke neman cika ya janyo wayarsa cikin basarwa ya ce
"Bari na soma sanar da ita, don ta fi ɗaukar abin da muhimmanci." Da sauri Abdoul ya riƙo hannunsa yana girgiza kai ya ce
"A'ah kar ka kira ta, kar ya zamana hakan ya koma tirsasawa, gwara ka bar ni da kaina na yi mata magana, na san duk wani abu da ke ranta za ta fito ta faÉ—a mini ba tare da wani shakku ko tsoro ba, tun da ba zan nuna mata ta hanyarka na biyo ba." Sauke ajiyar zuciya Tareeq ya yi, irin 'Shi kenan toh' É—in nan, kafin ya ce
"Allah Ubangiji Ya tabbatar da alkhairi. Amma tsaya ka tabbatar ba karɓar tayin nan ka yi saboda mutuncinmu ba? Za ka so ƙanwata kamar yadda nake fatan ita ma za ta so ka? Ka san ba na son a wulaƙanta mini er'uwa." Dariya sosai Abdoul ya yi, kana bayan ya dena ya soma faɗin
"Tareeq manta wane ne kai kake a wajena, ka manta duk wani abu da ya shafe ka dole ne a wajena na so shi? Toh ka manta da wannan son, ba irin shi zan yi wa Sultanah ba, nata na daban ne, matuƙar dai ta amince da ƙudurin da zan je mata da shi." Wani irin sanyi ne ya ji yana ratsa shi, ya lumshe kyawawan idanunsa yana jin har cikin zuciyarsa farin ciki mara misaltuwa. Wato har abada ba zai daina alfahari da kasancewar Abdoul amininsa ba. Fata yake hakan ya zama silar farin cikin er'uwarsa na har abada. Yana fatan hakan ya zama dalilin sake ɗorewar zumuncinsu da su Abdoul na har abada. Yana fatan wannan abu ya zama ɗaya daga cikin abin da zai zama cikin tarihin gidan Iyalan Dikko na sama-sama.
.. Washe gari ma suna tashi da safe a wajen da suka kwana jiya, Ameer ya yi sallama da Daneen ya tafi inda ya sami aikin. Ita kuma ta ci gaba da zama a wajen, saboda gurin ya fi security, kuma babu mutane da yawa, can kuwa maza ne kawai, kafin ka ga mace ma aiki ne. Shi ya sa ya ce ta zauna, idan ya gama aikin sai ya dawo. Ranar ma be dawo da wuri ba, sai da ya kai kamar jiya sannan ya dawo da abinci mai rai da lafiya. Kamar jiya ma cikin farin ciki ya kawo wa 'yar'uwar tasa abincin, ɗan kuɗin da ya samo suka yi amfani da su wajen abubuwan buƙata, ya yin da Daneen ta ɗauki wani abun ta ajje musu, wanda za ta din ga ɗauka kullum ta ajiye har su kai adadin wanda suke buƙata su nufi ƙauyensu.
Haka Daneen da Ameer suka ci gaba da kasancewa a wannan wajen. Da safe bayan sun gama abin da za su yi Ameer zai tafi wajen aiki, ita kuma ta ci gaba da zama a wajen har ya dawo. Sai dai ga mamakin Daneen, sai ta lura da tun ranar da Ameer ya samu aiki, da kuma washe gari da yake dawowa cikin matuƙar farin ciki, be sake dawowa kamar haka ba. Tun daga ranar duk lokacin da ya dawo jikinsa a matuƙar sanyaye yake. Babu wannan nishaɗin, sai tarin damuwa da kuma tunani.
"Wai Ameer me kake ɓoye mini? Me yake faruwa?" Daneen ta faɗa tana kallansa, cike da sake nazarinsa. Da sauri ya ɗaga idanunsa ya kalle ta a nutse kafin ya buɗe baki ya ce
"Babu komai Adda.. Wani abun kika gani?" Girgiza kai ta yi cikin É—an faÉ—a ta ce
"Shi kenan, amma ka sani daga yau ba za ka sake zuwa wajen aikin nan kai ɗaya ba. Idan ba haka ba kuma sai dai ka dena zuwa gaba ɗaya. A haƙura da tara kuɗin kawai." Be san lokacin da ya ɗaga idanunsa ya kalle ta ba, daidai lokacin da ƙirjinsa ya wani mahaukacin bugawa. Sai ya shiga girgiza kai kamar wani ƙadangare kafin ya ce
"A'ah Adda, kin san gidan biredi babu mata, ba ze yiwu ki ce za ki din ga zuwa ba. Idan ba haka ba za su kore ni gaba É—aya."
"Eh, gwara su kore ka, idan dai har za ka ci gaba da dawowa da damuwa." Sauke numfashi Ameer ya yi, ya lumshe idanunsa masu kama da na Daneen, ya rasa me yake damun ƙwaƙwalwarsa. Gaba ɗaya kansa a hargitse yake. Idan da zai dena zuwa da sai ya fi kowa farin ciki. Sai dai kuma yadda yake ji tamkar ana azalzalarsa da zuwa wajen ya ji kwata-kwata ba ze iya daina zuwa ba. Kai ko da ma Daneen ɗin ce ta ce ya dena zuwa, a yadda yake jin gaba ɗaya tunaninsa da nutsuwarsa ta tafi can ɗin ba ya tunanin zai iya amincewa da hakan. Sai dai kuma gefe guda yana ji shi kansa da zai iya hana kansa dena zuwa da ya dena. Wannan dalilin ne ke sanya shi jinsa tamkar wani zautacce, saboda yadda tunani da ra'ayi biyu ke ta masa yawo a cikin kwanya, kwanyarsa shi ɗaya. Kuma duka hankalinsa ya kwanta da su.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 17
Ƙura masa idanu Daneen ta yi, tana so ta ga ko za ta iya karantar abin da yake ɓoye mata, don tabbas tafarar ɗaya ta fahimci hakan. Sai dai ba ta ce masa komai ba, har zuwa lokacin da ya dawo daga mara armashin tunaninsa ya sauke idanunsa a kanta. Duk kuma sai ya so ya duburbuce saboda ganin tana masa wani kallo da ya fi kama da na tuhuma.
"Adda." Ya faÉ—a a sanyaye. Da sauri ta girgiza kai
"Kar ka kira sunana, kawai ka buɗe baki ka faɗa mini abin da ke faruwa, idan ba haka ba na faɗa maka ba za ka sake zuwa ba." Ta ƙare maganar da iya gaskiyarta har lokacin tana kallon sa. A sanyayen dai ya sake faɗin
"Ki yi haƙuri Addatah, shi kenan ki shirya mu din ga tafiya tare ai shi kenan koh?" Sai a lokacin ta yi murmushi kafin ta ce
"Toh damuwar ta mene ne?"
"Gajiya ce fa kawai." Ya faɗa bayan ya langaɓar da kansa.
"Ai dai mun kusa koma wa wajen Innarmu In Sha Allah." Jinjina kai Ameer ya yi yana murmushi, sai dai bai ce komai ba.
Kamar yadda ya faɗa kuwa, washe gari tare suka tafi wajen aikin shi da Daneen. Suna tafe suna hira, tana kallon duk inda suka wuce, saboda ita ba ta taɓa zuwa wajen ba. Don iyakincinta cikin kasuwa, idan suna buƙatar wani abu ta shiga ta siyo musu, daga nan ta koma inda suke ta zauna. Sun yi tafiya mai ɗan tsayi kafin Ameer ya kalle ta ya ce
"Ki zauna a nan, kin ga cikin layin nan a nan gidan biredin yake, zan je idan na gama sai na fito mu tafi." Kallon layin ta yi kamar mai son hango gidan biredin. Sai dai ba ta hango ba, amma ko babu komai nan É—in zai fi mata kwanciyar hankali tun da tana kusa da É—an'uwanta. Don haka ta gyara tsayuwarta ta ce
"Toh shi kenan Ameer, Allah Ya ba da sa'a, ina jiran ka fa." Ta ƙare a hankali tana kallon sa.
"Toh Adda bari na je." Ya ƙare yana ɗan murmushi, wanda ya yi nasarar lulluɓe tulin damuwar da ke danƙare a zuciyarsa. Wadda ta hana zuciya da ƙwaƙwalwarsa sukuni.