← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 49

Sashe 30

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba ɗaya jikinta a matuƙar sanyaye yake, lokacin da take taka wa tana bin bayan wani da zai raka ta ɗakin da Ameer yake ciki. Sai da ya tura ƙofar ɗakin sannan ya juya ya bar wajen. Daneen ta bi shi da kallo kafin ta maida idanunta cikin ɗakin. Runtse idanunta ta yi, tana jin yadda zuciyarta ta karye, saboda hango ɗan'uwanta da ta yi kwance, har kuma lokacin ba ya iya numfashi shi ɗaya sai da taimakon na'ura. Kamar wadda ke tsoron taka ƙasa haka take takawa zuwa cikin ɗakin idanunta a kansa. Ta zuba wa kyakykyawar fuskar Ameer idanunta lokacin da yake bacci kai sai ka rantse cikin kwanciyar hankali yake, babu wani abu da ke damunsa. A nutse ta kai hannunta ta riƙo hannunsa cikin nata, tana jin wata irin ƙwalla na tarar mata. Idanunsa ya shiga buɗewa a hankali kamar ya san wadda ke tsaye a wajen. Sai dai shi ma cike yake da fatan a ce ya buɗe idanunsa ya ga 'yar'uwarsa a gefensa. Aikuwa cikin ikon Allah yana buɗe su ɗin kuwa ya sauke a kan Daneen. Runtse idanunsa ya yi kafin ya buɗe a hankali daidai lokacin da wasu kyawawan ƙwalla suka zubo daga cikin idanunsa.

"Ameer." Ta faɗa, tana kai hannunta kan bakinta ta toshe don kar kukan da take ta riƙewa ya fito.

"Adda." Ya yi ƙarfin halin faɗa. Rasa abin da za ta yi ne ya sanya ta zube wa a wajen kawai, ta kifa kanta a kan gadon ta shiga raira kukanta a hankali. Hannunta da ke kusa da na shi ya riƙo sosai, dalili kenan da ya sanya ta saka hannunta ta share fuskarta kafin ta miƙe tsaye tana kallon sa.

"Kin ga abin da na ja mana koh?" Ya faÉ—a a raunace. Girgiza kai ta yi tana barin hawayen cikin idanunta damar zubowa.

"Ka dena mini irin wannan maganar Ameer, ba ka ja mana komai ba. Duk abin da ka ga ya faru dama rubutacce ne. Bawa kuma ba ya taɓa wuce wa ƙaddararsa." Murmushin yaƙe Ameer ya yi, yana sake jin yadda gaba ɗaya duniyar ta fice masa a ransa. Ji yake tamkar zuciyarsa za ta yi bindiga saboda tsananin ciwon da yake ji a cikinta. Cikin sanyi da ƙarfin hali ya soma faɗin

"Adda ba na tunanin zan rayu kowanne irin aiki aka yi mini. Ni kaɗai na san abin da nake ji. Bayan zuciyata Adda cikina na yi mini wani irin ciwo da na kasa fahimtar wane iri ne shi. Idan na mutu ki nemar mini yafiya gurin Innarmu, duk abin da ya faru ni na jawo. Sai da kika ce mini kar mu baro ƙauyenmu amma na kafe, yanzu ga abin da ya faru." Ya kai ƙarshen maganar yana sauke wani numfashi a mugun wahalce.

"Ameer ba na so, ka dena na faɗa maka. Ba za mu koma wa Inna a wani irin hali ba, In Sha Allah za mu koma mata ne a yadda muka baro ƙauyenmu. Za ka warke da yardar Ubangiji. Na kuma roƙe ka da ka cire wannan damuwar da kake ɗora wa kanka ko don samun lafiyarka, Ameer ka san lafiyarka ita ce tawa don Allah." Daneen da muryarta ke fita da ƙyar cikin kuka ta faɗi haka. Girgiza kai kawai ya yi ya ce

"Toh Adda na dena, na dena.." Ya faɗa yana wani lumshe idanunsa. Sai da ya yi bacci tana cikin ɗakin sannan ta fice ƙwaƙwalwarta fall tunani kamar za ta tarwatse.

..Tana nan zaune inda Yohanah ya bar ta, bayan ya ba ta uzurin zai je ya dawo. Ta zauna ta yi shiru cikin rashin sanin abin yi. Ita kanta tunani nema yake ya yi wa ƙwaƙwalwarta yawa, sai dai babu yadda ta iya. Haka nan take zaune, a ido tana wajen amma a zahiri ita ce zaune a wajen kawai, amma gaba ɗaya hankali da duk wani tunaninta yana wani wajen daban.

"Doctor na son ganin ki." Shi ne kawai abin da ta ji, wanda ya yi nasarar dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi.

"Na'am?" Ta ƙare maganar da alamar tambaya tana kallon wadda ta yi mata magana. A karo na barkatai ta sake maimaita mata saƙon Likitan tana nazarinta. Miƙewa Daneen ta yi tana faɗin

"Tohm." Daga haka ta bi matar a baya zuwa office É—in Likitan. A bakin wani É—aki suka rabu, ya yin ita matar ta kalli Daneen ta ce

"Ki shiga." Kallon ta Daneen ta yi tamkar mai neman ƙarin bayani, sai dai kuma ba ta ce komai ba, illa jinjina kai da ta yi. Daga haka matar tayi gaba ya yin da ita kuma ta tura ƙofar ɗakin da sallama ɗauke a kan laɓɓanta. Kusan a tare suka amsa sallamar, dukkan su idanunsu a kanta. Kasancewar ba ta san za ta yi ido huɗu da wasu fuskokin ba, ya sanya ta yin turus tana ɗauke kanta daga kallon su.

"Ƙaraso mana." Maama ta faɗa har lokacin idanunta a kan Daneen. Cike da sassarfa Daneen ta ƙarasa cikin ɗakin tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa.

"Taho ki zauna a nan." Maama ta faÉ—a, ba tare da jin komai ba ta ja hannun Daneen É—in ta yi mata mazauni a gefe kaÉ—an da ita. Babu musu Daneen ta zauna hannunta É—aya cikin É—aya, zuciyarta fall tunanin shin su waÉ—annan É—in su waye su?

"Ina wuni?" Ta yi ƙarfin halin faɗa a hankali.

"Alhamdulillahi, ya jikin ƙanin naki?" Maama ta faɗa.

"Alhamdulillahi." Ita ma Daneen ta ba ta amsa a sanyaye. Hidaya da ke gefen Maama ta ce

"Wai ita ce za ta ba wa Yah Tareeq ɗin ƙoda?" Jinjina kai Maama ta yi tana murmushi. Cikin matuƙar farin ciki Hidaya ta miƙe ta koma kusa da Daneen, tana jin wata irin ƙaunarta lokaci guda. Tun shigowar ta take yaba irin kyawun da Allah Ya ba ta, sai dai da yake ba ta san wace ce ba ya sanya ta kama kanta.

"Amma na ji daɗi, Allah Ya ba ki abin da kike nema duniya da lahiya, Allah Ya biya miki buƙatunki na alkhairi."

"Ameen." Sultanah ta amsa addu'o'in Hidaya tana murmushi.

"Ya sunanki?" Hidaya ta faɗa tana kallon Daneen da murmushi a kan fuskarta. Sai da ta ɗaga kyawawan idanunta da suka ƙanƙance sannan ta ce

"Daneen."

"Woww, suna mai daɗi. Sannu Daneen." In ji Hidaya tana murmushi. Godiya sosai suka ci gaba da yi wa Daneen, suna kuma yi wa Ameer addu'a. Abin da ya matuƙar faranta ranta kenan.

"Sultanah ku je gida tare da ita ta samu ta yi wanka ta yi bacci ta huta kafin goben da za a yi aikin." Maama ta faɗa bayan ta miƙe tsaye. Da sauri Daneen ta kalli Maama tana girgiza kai. Tana kai wa ƙarshen maganarta ta soma faɗi cikin sanyayyiyar muryarta.

"A'ah, ba zan iya tafiya in bar ƙanina ba. Ki yi mini afuwa don Allah ba zan iya ba." Kallon ta su duka suke yi, abin bai ba su mamaki ba, don duk tana hakan ne a kan ɗan'uwanta. Su ma kuma sun san me ake nufi da ɗan'uwa.

"Shi kenan, ki je zuwa an jima sai ku dawo idan kin huta." Kamar za ta fasa kuka haka ta ji. Tabbas matar ta yi mata kwarjini amma duk da haka ba ta ji ko nan da can za ta iya matsawa daga asibitin, bayan Ameer na ciki a kwance. Don haka cikin girmamawa ta ce

"Don Allah ki yi haƙuri ki bar ni wajen ɗan'uwana." Ta faɗa lokacin da ƙwalla ta cika cikin idanunta. Cike da tausayawa Maama ta ce

"Babu damuwa. Allah Ya ƙara lafiya, Ya kuma saka miki da alkhairi." Wata ƙatuwar ajiyar zuciya Daneen ta sauke, tana jin wani sanyi na ratsa ta. Haƙiƙa ta ji daɗin kai ƙarshen maganar da matar ta yi, don da ta ci gaba da cewa ta je ɗin ba ta tunanin za ta iya ci gaba da yi mata musu. A sanyaye ta amsa da

"Ameen." Daga haka suka yi sallama da Daneen suka fice daga ɗakin. Ita ma ba ta ƙara wasu mintina ba ta fice zuwa inda take zaune ɗazun.

Washegari ita ce ranar da za a yi wa Daneen aikin cire ƙoda, ya yin da za a yi wa Tareeq na dashen ƙodar. A kuma safiyar ranar ne Yohanah ya je ya biya duk kuɗaɗen da ake buƙata na aikin da za a yi wa Ameer. Cike da mamaki Likitan ke kallon sa, ya ce har lokacin ya kasa dena tantamar anya kuwa Yohanahn kafiri ne da gaske?

"Amma me zai hana ka nuna fuskarka wajen Alhaji Alhassan. Alkhairinka yawa gare shi wajen iyalinsa." Murmushi Yohanah ya yi kafin ya ce

"Babu damuwa, ina yin komai ne saboda Allah, kuma ba na so ya sani. Akwai dalilin yin hakan, ina so ne na rama abin da ya yi mini. Kamar yadda yake taimakawa mutane a bayan ido, shi ya sa nake so na rama masa ba tare da ya sani ba." Jinjina kai Likitan ya yi, bayan ya sauke ajiyar zuciya ya ce

"Duk da haka, ko da sau ɗaya ne ka bari ya ganka ya gode maka. Ka samo wadda za ta ba wa ɗansa ƙoda. Duk da a matuƙar buƙatar kuɗi take, hakan bai sa ka bar ta da shi ba. Ka kuma ƙi barin Alhaji Dikko ya biya kuɗin aikin a matsayin kuɗin ƙodar yarinya, shi ma ka ɗauke masa. Kuma duk da haka ba ka so ya sani, bayan kai ɗin na daban ne, mai ɗumbin alkhairi a gare shi." Kafin Yohanah ya ce komai wayarsa ta shiga ringing, ya kalli mai kiran nasa, kawai sai ya tura ta cikin aljihunsa kafin ya ɗaga idanunsa ya maida su kan Likitan ya ce

"Please doctor a yi abin da na ce. Ita yarinyar babu damuwa za ta iya haɗuwa da shi, amma ni babu buƙatar hakan kamar yadda na faɗa maka." Yohana ya ƙare maganar yana sakin wani murmushi, lokaci ɗaya yana kai hannunsa guda ɗaya ya shafa haɓarsa har lokacin idanunsa a kan Likitan.

#YOHANAH
#KIDNEY
#DANEEN
#TAREEQ
#AMEER

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 20

Jinjina kai Likitan ya yi kafin ya ce
Chapter 30 · 0% Book details