← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 49

Sashe 24

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar idanunta za su faɗo, haka take ci gaba da kallon hanyar da ta ga Ameer ya bi. Zuwa can dai ta miƙe a kan ƙafafunta, ba ta kuma san yadda za ta iya ci gaba da zama a wajen ba, bayan takamaimai ba ta san inda ɗan'uwanta yake ba. Ga shi kuma har an idar da Sallahr Azahar. Sai dai miƙewar da ta yi ya yi daidai da lokacin da muryar Ameer ta daki dodon kunnenta.

"Adda." Ai ba ta san lokacin da ta juya da sauri ba. Take idanunta suka sauka a kan Ameer. Wani murmushi mai haɗe da ƙwalla suka wanzu lokaci guda a kan fuskarta. Idan ta ce tana farin ciki ma ɓata baki ne, don kuwa fuskarta kawai za ka kalla ka fahimci tsananin farin cikin da ta tsinci kanta a ciki bayan ganin Ameer.

"Ameer ina ka je?" Ta yi tambayar da ke ta ci gaba da yi mata lugude a ka. Murmushi ne ya suɓuce masa kafin ya ce

"Aiki na samo Adda, kina zaune zan din ga yin aiki muna samun kuɗi. Mu samu na cin abinci da komai ma, har kuma mu tara na koma wa ƙauyenmu." Ya ƙare yana murmushin dai. Wani sabon murmushin ne ya sake ƙwace mata, ta ce

"Da gaske?" Jinjina kai ya yi kafin ya ce

"Ehh, amma dai ki zauna ki fara cin abinci yanzu. Ya jikin naki?" Sai da ta harare shi kafin ta ce

"Bayan duk ka gama tsoratar da ni."

"Wallahi Adda ina can ina tunanin kar ganin na daɗe ki ce za ki je ki nemo ni, in zo kuma ban gan ki ba in shiga 3." Ya ƙare fuska a marairaice. Har ba ta san lokacin da dariya ta suɓuce mata ba.

"Mu je mu samu ruwa mu yi sallah tukunna." Ta faÉ—a. Be musa mata ba, ya amsa da "Toh."

... Tun daga farkon layin idan ka kalla za ka fahimci lallai wani gagarumin al'amari ke faruwa. Saboda yadda motoci ke ta kai-kawo cikin layin, 'yan sanda na ta zagaye, haka zalika mutane na ta kai da kawowa. Kowa ka kalli fuskarsa cikin annushuwa yake, wanda hakan ze alamta maka cewa ko ma mene ne abin da ke faruwa abin farin ciki ne. Tahowar wata ƙatuwar hamshaƙiyar mota da kallo ɗaya za ka mata ka san kuɗinta ba na wasa ba ne, shi ne abin da ya sa masu gadin gidan wangale ƙatuwar ƙofar gidan tun kafin motar ta ƙaraso. Tuni kyakykyawan dattijon mutumin da ke sanye cikin farar shaddar da ta matuƙar yi masa kyau, ta kuma sake bayyana kwarjininsa da kamalarsa ya gyara zamansa. Tun kafin ya ce komai, drivern ya yi hanzarin wangale glasses ɗin motar. Wanda hakan ya ba wa mutanen da ke tsaye suna jiran zuwan Alhajin nasu damar soma ganinsa. Cikin lokaci ƙanƙani fuskarsa ta cika da annuri, ya yi amfani da hannunsa wajen ɗaga musu hannu fuskarsa na cigaba da nuni da yadda ya yi farin cikin ganin su. Alhaji Alhassan Dikko kenan, mutum mai matuƙar kima da mutunci a idon jama'a, mutum mai matuƙar taimako da jiki da dukiyar da Allah Ya ba shi. Mai kirki, mai matuƙar kula da buƙatun mabuƙata, maƙotansa da kuma mutanen gari. Wanda hakan ya saya masa soyayyar mutane da dama, ya kuma ƙara masa kimar da tun tale-tale yake da ita. Har sai da suka dangana da cikin gidan sannan mutane suka haƙura. Daga haka aka rufe gate ɗin bayan motocin da ke bin bayan ta Alhaji Alhassan su ma sun shige cikin gidan. Shi har ya riga ya saba, duk lokacin da ya yi tafiya irin wannan haka mutane ke masa duk ranar da ze sauka a ƙasar. Don kuwa ƙarya ne mutum ya ce be yi kewarsa a en kwanakin da ya yi ba ya ƙasar ba. Saboda yadda ya kasance mutum mai matuƙar kula da duk wanda ke kusa da shi. Duk da kafin ya tafi yana ɗora wani a kan abubuwan da yake yi, amma duk abin da ze yi, ba ze kai wanda yake yi ba. Shi ya sa idan yana nan abubuwa da dama suka kasance na daban, suke kuma tafiya a tsari.

Ko a cikin gida ma hakan ce ta kasance, mutanen da ke zaune cikin gidan tuni suka fara zuwa suna kwasar gaisuwa, kamar kodayaushe fuskarsa cike da annuri yake amsa musu. Kai tsaye sashensa ya wuce kamar yadda ya saba, sashen nasa na nan a gyare tsaff-tsaff kamar yadda ya tsammata. A gaggauce ya watsa ruwa a jikinsa kana ya sake shiryawa cikin babbar rigar shadda ita ma fara. Kai tsaye ya wuce sashen Dada ji da gaba ɗaya iyalan nasa ke jiran sa a can ɗin. Ai kuwa cikin matuƙar farin ciki dukka suka tarbe shi lokacin da ya iso. Kowa ka kalli fuskarsa ka san tabbas yana cikin farin ciki. Sai da ya shafe wajen mintina goma, sannan Maami ta iso, ita da Mom Abdoul, ba ta yi tsammanin kai tsaye nan ɗin ze wuto ba. Shi ya sa ta din ga tsumayin ganin inda ze nufa, sai dai shirun da ta ji ne ya tabbatar mata da tabbas nan ɗin ya nufo. Wannan ne dalilin da ya sa ta ɗebo 'yan matan ƙafafunta ta taho, duk da ta so tare suka shigo. Dan da ta san ma ba zai shiga sashenta ba, tun a harabar gidan za ta je ta tarbe shi don su shiga sashen Dadan a tare. Ko minti 5 ba su yi da zama ba, bayan sun yi wa Abeey barka da zuwa, Amininsa Alhaji Bashir ya iso gidan, mahaifi ga Abdoul. Sosai farin cikin Abeey ya daɗu. Bayan kwanaki masu yawa, yau ga shi tare da iyalansa, ga kuma abokinsa ƙwalli ɗaya takk da yake da shi tun yarinta shi ma. Wannan dalilin ne ya ƙara ƙawata zaman nasu. Nan aka shiga hirar yaushe gamo. Kafin zuwa can aka nufi ɗakin da ya kasance na cin abinci, nan cikin sashen Dada ji. Sultanah, Hidaya da Jawahir su ne suka kwaso komai daga kitchen ɗin Dada ji suka jere shi kan dinning ɗin. Abubuwa ne kala-kala masu aji, waɗanda aka yi abubuwan da Abeeyn ya fi so a rayuwarsa. Baƙin-ciki kamar ya kashe Maami, da ta tuna abincinta na can jibge yana jiran Abeeyn. Kenan idan ya zauna ya ci abincin a nan, ita kuma nata ya za ta yi da shi? Ita fa dama wannan tsohuwar tana matuƙar shige mata hanci da ƙudundune, tana yawan kawo mata cikas a cikin al'amuranta.
A kusa da Dada ji ya zauna, don babu ƙarya ya yi kewar mahaifiyar tasa. 'Yan matan ba su zauna ba, sai da suka yi serving na kowa kafin suka ja kujera suka zauna. Duk yadda Sultanah ke ƙoƙarin ta jure, ba ta din ga satar kallon Abdoul ba, hakan ya gagara, ta kasa daurewa. Don haka a ɗan fuzge ta din ga satar kallon shi, cike da fatan kar ya kama ta, ko kuma Yah Tareeq ya gan ta, ya tuna be yi mata faɗa a kan abin da ta yi ba. Don kuwa tun da ta ga ya kalli saƙon be ce komai ba, ta san tabbas wani abun yake shiryawa, dalilin kenan da ya sa take jin jikinta a matuƙar sanyaye. Ita dai Jawahir sai sakin murmushi take yi, saboda yadda Ummanta ta sanar da ita Maama ta tabbatar mata da za ta isar wa da Abeey maganarta ita da Tareeq. Ita kuma dama ba ta da wani buri illa na mallakar Tareeq ɗin. Ba tun yau ba, kyawunsa ke matuƙar kashe ta, tana ƙaunarsa ainun, tana matuƙar son kallon kyakkyawar fuskarsa, da kuma irin ƙirar da Allah Ya ba shi. Sai bayan sun gama cin abincin sannan suka koma palourn Dada ji, nan aka cigaba da hira sosai. Sai dai idan dai har abin ya shafi Maama, toh ba za ka ji Maami ta ce komai ba. Don ita hirar ta ta fi kasancewa ne tsakaninta da Hajiya Zulai, da kuma Alhaji Bashir. Duk abin da take Dada ji na lura da ita, ta yi dai kamar ba ta gani ba ne. Don ita kam har ta gaji da yi mata magana a kan halayenta. Maamin wata irin mata ce da lokuta da dama ka kan kasa gane kanta. Ban da haka idan hali mai kyau ne Maama ta fi ta. Amma kuma ita burin ta kawai kowa ya yi harkarsa, ba ta son wani abu ya haɗa ta da abokiyar zaman nata kwata-kwata. Sai ka ce masu zaman gaba, wanda ita Dada ji ba za ta ɗauki hakan ba. Duk da hakan ya fi saka wa su zauna lafiya, amma kuma babu yadda za a yi su zauna babu magana, bayan suna zaune ne cikin gida ɗaya, ƙarƙashin mutum ɗaya. Kuma hakan ya samo asali ne, tun wani ɗan tashin hankali da ya faru tsakanin su, Dada ji ɗin da kanta ta shirya al'amarin, ta ce babu ruwan kowa da kowa. Shi kenan Maami ta riƙe wannan maganar, a cewar ta ai an ce da ita babu ita babu Maama. Ya yin da ta ɓangaren Maama, duk wani abu da ya shafi Maami babu ruwanta da shi, amma tabbas idan suka haɗu za ta mata sallama, da sauran su. Girgiza kai Dada ji ta yi. 'Mace sai ka ce mai zuciyar kafirai, kina abu tamkar ƙaramar yarinya. Toh ai ga mijin naku nan ya dawo, sai ki ci gaba da gaba da abokiyar zaman naki' Ta raya hakan a ranta.

Kallon Tareeq Abeey ya yi da ya miƙe yana gyara tsayuwarsa hannunsa ɗauke da waya.

"A'ah, Tareeq ina za ka je ne?" Ɗan murmushi ya yi a kan laɓɓansa kafin ya ƙarasa gaban Abeeyn ya tsuguna a gefen kujerar da yake kai ya ce a nutse

"Abeey, ina buƙatar fita ta gaggawa." Daga haka suka ɗan yi magana ta tsawon mintina biyu a hankali, wanda babu wanda ze ce ya ji abin da suka faɗa. Kallan Tareeq Abeey ya yi, kana ya ce

"Ubangiji Allah Ya tsare, zuwa gobe ma samu mu tattauna." Abeey ya faÉ—a yana É—an kafe shi da idanunsa, saboda tabbatar da abin da idanun nasa ke ganar masa a fuskar É—an nasa.
Chapter 24 · 0% Book details