← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 49

Sashe 41

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma ba ki kyauta mini ba Daneen, kuma a gaskiya zan faɗa miki ban ji daɗi ba. Me ya sa zan saka hannu wajen yin wani mummunan abu a kan Tareeq? Bayan dukkanmu so muke a hukunta shi a hukumance. Na ɗauka na tura miki abin da nake so ki samo mini a wajen Tareeq, takardu ne fa kawai. Ban da su babu komai. Ke ce fa mai fansar da ta fi muhimmanci da kuma girma, so kike a ɗaukar miki fansar ɗan'uwanki. Kuma shi ne dalilin da ya sa na dage, nake kuma son ke ma ki dage. Amma idan kin ga ba za ki iya ba, ko kuma za ki saka zargi a cikin ranki, toh ina ga babu amfanin ci gaba da zaman ki cikin gidan nan, kawai ki fito ki koma ƙauyenku, ki sanar da su mutuwar Ameer kawai. Idan ya so sai ku nemi wata hanyar da kuke ganin za a iya hukunta Tareeq ɗin." Ya ƙare maganar cikin wani irin yanayi, da ke nuni da yadda ya ji babu daɗi da gaske. Shiru Daneen ta yi, tana jin yadda jikinta ke ƙara yin sanyi. Sai da ta daure, ta yakice komai, sannan ta iya yago magana ta ce

"Toh amma me ya sa ka din ga tambaya ta da gaske yanzu zai fita?" Ta tambaya a sanyaye.

"Kawai so nake na ji, saboda ki je sashensa. Shi ne kawai dalilin da ya sa na tambaye ki. Ban da haka ina ruwana da inda zai je da kuma yake? Duk fa saboda ke ne. Ki yi tunani mana." Shiru Daneen ta yi tana nazarin duk maganganun da ya faÉ—a. Wajen minti 2, sannan ta sauke ajiyar zuciya, wadda shi kansa sai da ya jiyo sautinta. Ya gyara zamansa daga inda yake zaune kafin ya ce

"Ban ji daÉ—in yadda zargi ya shiga tsakaninmu ba." Ya faÉ—a a hankali. Wata ajiyar zuciyar Daneen ta sake saukewa kana ta ce

"Ka yi haƙuri, na kasa ƙaryata abin da zuciyata ke ta hasaso mini ne." Daga haka kawai sai ta ajiye wayar ba tare da ta sake jin wani abu da ya ce ba. Ta zauna yaɓar a kan gadon ɗakin zuciyarta na wani irin zafi. Wata irin kewar Innarta ta ji tana ratsa ta, gefe guda kuma tunanin Ameer ɗin da kullum yana cikin mafarkinta. Ta ƙagu komai ya kammala ta gan ta a kusa da Innarta. Ko ta samu ta ɗora kanta a kan kafaɗarta ko cinyarta su yi kukan rashin Ameer tare, su yi wa Ameer addu'a tare, su kuma tuna shi tare. Miƙewa ta yi a hankali ta shiga zagaye ɗakin, hannunta duka biyun cikin na juna. Gaba ɗaya kwanyarta ta cushe da tunanunnuka kala-kala. Tsoron ta ɗaya kada a ce Tareeq ya rasu a asibiti yanzun. Ba ta so ya mutu ba tare da an hukunta shi ba, ba ta so ya mutu ba tare da an masa hukunci daidai da muguntar da ya yi wa ɗan'uwanta ba. Don haka za ta yi ta masa addu'ar ya rayu, ko don ya karɓi kashinsa a hannu. Tana ci gaba da zagaye ɗakin Sultanah ta shigo da sauri.

"Sister shirya mu wuce asibitin da aka kai Yah Tareeq. Yah Tareeq ne ya yi hatsari." Sultanah ta yi maganar, gaba É—aya yanayinta na nuni da yadda take cikin tashin hankali. Bin ta da ido kawai Daneen ta yi, ita ma duk nata hankalin a tashe yake. Sai dai ba na komai ba ne face kar ta je Tareeq ya mutu ya bar ta da fansar da ba ta É—auka ba. Dogon hijab É—inta Sultanah ta É—auka ta saka a gaggauce, sai da ta yi hanyar fita sannan ta ce

"Ki fito mu tafi." Daga haka ba ta jira Daneen É—in ta ce komai ba ta fice daga É—akin. Babu musu Daneen ta bi bayanta, gwara ta kasance tana kusa, ko babu komai za ta din ga sanin a halin da Tareeq É—in yake ciki.

... Lokacin da suka isa, an daɗe da shigar da Tareeq emergency, saboda mummunan raunin da ya samu a ƙafarsa. Babu wanda ya samu damar ganinsa. Dukka sai suka yi cirko-cirko suna jiran jin halin da yake ciki hankali a tashe. Sai dai kowannen su addu'a yake, Allah Ya sa ko ma mene ne zai zo ya zo da sauƙi.

"Ubangiji Allah Ya ba ka lafiya yaron nan." Dada ji ta faÉ—a a sanyaye. Sultanah ce ta iya amsa wa da "Ameen." Ita ma jiki a sanyaye. Ita dai Daneen sai raba ido take. A zahiri ita kanta ma neman lafiyar tasa take, sai dai abin nasu ya fita daban. Don su suna so ne ya samu lafiya kawai, ya yin da ita kuma nata son ya samu lafiyar saboda fansarta ne. A nan suka ci gaba da zama har zuwa shuÉ—ewar wasu lokuta masu tsayi. Zuwa lokacin har Abeey ma ya iso shi da babban amininsa Alhaji Abubakar. Abdoul ma tuni ya iso, don har ya riga ma su Abeey zuwa cikin asibitin.

... Kansa a kwance yake a kan pillow, ya yin da hannunsa ɗaya ke kan fuskar tasa, idanunsa a rufe. Turo ƙofar da aka yi ne ya sanya shi buɗe lumsassun idanunsa da kalarsu ta ɗan sauya. Bai yi yunƙurin tashi ba, duk da ba ya iya ganin mai shigowar. Sai dai tun kafin ta ƙaraso ya fahimci wace ce, don haka a hankali ya shiga miƙewa zaune. Da sauri Maama ta ƙarasa ta gyara masa zaman. Ya zube idanunsa da suka faɗa a kan Maaman yana jin wani irin rauni na kama shi. Ita ma shi take kallo ba tare da ta ce komai ba. Ta ma rasa me za ta ce, ko kuma ta ina za ta fara.

"Maama ni kuma ƙaddarata a ciwwuwwuka take. Ina ta saka ku cikin fargaba koh? Ni kaina ba na jin daɗin hakan. Amma ya zan yi Maama?" Ya ƙare maganar a sanyaye. Kafe shi da idanunta Maama ta yi, tuni fuskarta ta ɗinke tsaff. Kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta girgiza kai ta ce

"Ga ka dai a haka kamar ka girma ka yi hankali, har kana da ƙannen da za ka tsawatarwa, ashe ba haka ba ne. Tareeq yanzu ni za ka kalla faɗa wa wannan maganar? Waye yake ɗora cuta? Akwai wanda haka kawai yana sane zai ɗora wa kansa cuta? Allahn da Ya jarabce ka da ita shi zai yaye maka In Sha Allah. Za ka samu lafiya cikin yardar Ubangiji." Lumshe kyawawan idanunsa ya yi a hankali kamar mai jin bacci, ya buɗe su a kan Maama kafin ya ce

"Ki yi haƙuri Maama. Amma kuma kina tunanin wannan ƙafar za ta warke kuwa?" Ya ƙare maganar idanunsa a kan ƙafarsa da ke ajje kawai a nannaɗe. Shi kaɗai ya san azabar da yake ji daga cikinta, tamkar ana daddatsa ta da wuƙa irin kakkaifar nan. Ita ma kallon ƙafar tasa ta yi da jajayen idanunta, ta kai wajen minti 1 tana kalla kamar mai nazarin wani abu, sannan ta buɗe baki a nutse ta ce

"Ai Allah na ce." Jinjina kai kawai ya yi, yana koma wa baya, ya jinjina da pillow. A hankali ya É—an fesar da iska daga bakinsa, kamar wanda ke shirin sake cewa wani abun. Sai kuma ya tsuke bakinsa ya yi shiru. Maama ta nemi waje ta zauna tana kallon É—an nata cike da tausayawa.

...."Alhamdulillahi, cikin ikon Allah abubuwa da dama da sauƙi. Sai dai kuma.." Likitan ya ɗan dakata a nan yana girgiza bironsa a kan takardar gabansa. Jinjina kai Abeey ya yi alamar yana tare da shi, hakan ne ya sanya shi ɗan ajiye numfashi kafin ya ci gaba da faɗin

"Ƙafarsa.. Gaskiya ƙafarsa ta samu mummunan rauni sakamakon yadda ta maƙale cikin motar sosai, da ƙyar aka iya zaro ta. Kamar yadda aka sanar da ni kenan. Wannan ne dalilin da ya sa.." Sai ya sake dakatawa a nan.

"Ya Hayyu Ya Qayyum." Abeey ya faɗa a fili idanunsa a lumshe. A ransa yana ji lallai lokaci ya yi da Tareeq zai ajiye ko ma mene ne, ya tsayar da hankalinsa a kan kasuwanci kawai. A hankali ya juya ya kalli likitan, yana jin yadda ilahirin jikinsa ya yi matuƙar sanyi, sannan ya ce

"Kaa ga kada ka ɓoye mini komai. Tareeq ɗana ne, saboda haka ka sanar da ni komai a kan matsalar ƙafar tasa."

"Ba zan ɓoye maka ba Ranka ya daɗe, fatanmu na warkewar ƙafarsa har ya miƙe ya ci gaba da tafiya ba shi da yawa. Ƙafarsa ta samu mummunan rauni kamar yadda na faɗa maka, wanda zai iya taɓa lafiyar tafiyarsa. Ba ma fata, ba kuma za mu cire rai ba, In Sha Allah za mu yi masa aikin da idan Allah Ya yarda za a dace. Amma sai dai ka yi haƙuri Yallaɓai, don hakan ba lallai ba ne." Likitan ya ƙare maganar a sanyaye, saboda yadda ya ga yanayin Abeey. Ya san yadda yake matuƙar ƙaunar yaransa, musamman ma kuma Tareeq. Sai dai ga shi Allah Ya fi jarabtarsa da ciwuka. Bai ga kuma amfanin ɓoye masa komai ba, tun da da kansa ya nemi ya sanar da shi hakan. Gwara ma ya sanar da shi gaskiyar, ba su da tabbacin za a samu nasara a aikin, saboda kar sai an yi ba a dace ba, a zo ana wallahi tallahi.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 27

Ɗan jimm Abeey ya yi na tsawon minti ɗaya ba tare da ya ce komai ba. Kafin zuwa can ya sauke ajiyar zuciya, a hankali a kan laɓɓansa ya furta

"Ya Ilahy." Kafin ya maida dubansa kan Likitan ya ce, ilahirin jikinsa a sanyaye.
Chapter 41 · 0% Book details