← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 49

Sashe 10

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

... Su uku ne zaune cikin palourn, manyan mata guda biyu, ya yin da matashiyar budurwa ke zaune ita ma a kan kujera. Sanye cikin wata doguwar rigar atamfa da ta matuƙar yi mata kyau. Kyakykyawa ce ba can ba, hasken fatar da Allah Ya ba ta shi ya haska kyawun nata. Hannunta ɗauke da waya tana dannawa, lokaci lokaci ta kan ɗaga ido ta kalli iyayen nata da ke magana. Zuwa can ma sai danna wayar ya gagara, musamman da ta ji maganar da suka fara ɗin ta shafe ta. Don haka gaba ɗaya ma sai ta ajje wayar ta maida gaba ɗaya hankalinta kan su. Daidai lokacin da Momynta ke faɗin.

"Amma Maama ba kya ganin tun da bare ta watsa mana ƙasa a ido, me zai hana mu haɗa shi da Jawahir, er uwarsa wadda dukka kowa ya san halinta" Murmushi matashiyar ta saki tana sake kama kanta a kan kujerar da take. Ita a lallai dole kunya ta ji, saboda tana gaban sirikarta. Buɗe ido Maama ta yi, kafin ta shiga jinjina kai

"Babbar magana.. Tareeq É—in?" Ta ambata ba tare da wata damuwa ba. Jinjina kai ita ma Momy ta yi tana faÉ—in

"Ehh shi fa Maama.. Ai hakan shi ne daidai. Don na san daga ke dai har Yaya ba za ku sake bari ya nemo wata a waje ba, ballantana har a zo a samu matsala."

"Ba wannan ba ne Hajiya A'isha.. Na san halin Tareeq, ke kan ki kin san halinsa. So bayan duk abin da ya faru ba na tunanin a nan kusa ze iya amincewa da wata kuma. Kin san dai yadda abin da ya faru ya illata zuciyarsa. So gaskiya yana buƙatar lokaci kafin a je masa da irin wannan maganar."

"Ba don kar ki ce na katse ki ba, da na sake tuna miki Jawahir fa er uwar Tareeq ce ta jini. Wadda ya san halayenta, uwa uba kuma tana ƙaunar sa." Momy ta ƙarasa maganar tana dafa kafaɗar Jawahir. Sake yin ƙasa da kai Jawahir ta yi tana wasa da yatsun hannunta da murmushi kwance a kan fuskarta. Fatan ta ɗaya Maaman ta amince da wannan haɗi. Don ta san idan dai har ta amince toh fa shi ma Tareeq ɗin abu mai sauƙi ne zai amince. Jin Maama ta yi shiru ya sanya ta sake faɗin

"Ki yi tunani a kan wannan al'amari, sannan ki duba abin da idon basira. Za ki gane da gaske Jawahir ce kawai ta dace da auren Tareeq.."

Abin da ya tsinta kenan lokacin da ya kawo kansa cikin ɗakin. Sai dai yadda fuskarsa take, kai ba za ka taɓa cewa ya ji ko da makamanciyar maganar da suke yi ba. Yana sanye cikin wasu sheggun ƙananan kaya da suka karɓi jikinsa. Ya yi wani shahararren kyau tamkar da ma don shi aka yi kayan. Ya sakaya baƙar sumar kansa da wata haɗaɗɗiyar facing cap, hakan ne ya sa ba a iya ganin sumar tasa. Sai dai ka hangi sumar da ke kwance luff a ƙeyarsa. Da sallama ya shiga cikin ɗakin, ba tare da ya kalli kowa da ke cikin ɗakin ba. Duk kuwa da tun kafin ya shigo ɗakin ya gama ganin su waye a ciki. Don haka gefen Maama ya je ya zauna. Cikin girmamawa ya gaishe da Momy da ta katse zancen ta saboda ganin shigowar sa.

"Lafiya ƙalau Tareeq.. Ya kuma wannan abu da ya faru? Toh Ubangiji Ya sa haka ne mafi alkhairi."

"Ameen." Kawai ya amsa da hakan yana maida duban sa kan Maama, don kwata-kwata ba ya so zancen ya yi tsayi. Ya kuma san halin Momyn sarai na son gutststsira zance. Don haka dan kada ma ta sake ce masa komai ya ce yana kallan Maama

"Barka da wannan lokacin Maama."

"Barka dai Tareeq, kana lafiya?" Shi ne kawai abin da ta faÉ—a. Duk da tana so su yi magana sosai da É—an nata, amma wanzuwar Momy a wajen ya sa ta kama bakinta kawai.

"Alhamdulillah.. Hidaya ba ta nan ne?" Ya tambaya saboda rashin ganin gilmawar ta, bayan hakan ba É—abi'arta ba ce, kusan kodayaushe ta fi zama gefen mahaifiyar tasu. Sai dai idan sister É—inta na nan, kuma ya san ba sa cikin gidan ma yanzu haka.

"Ohh, ta bi driver zuwa ɗakko su Sultanah." Maama ta faɗa. Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, yana shirin miƙewa Jawahir da ke ta sake gyara zama, tana tsara yadda za ta masa magana ta ce

"Barka da wannan lokacin Yah Tareeq." Sai a lokacin sannan ya ɗaga idanunsa ya mata kallo ɗaya, kafin ya ɗauke idanunsa. Ya ɗan ƙaƙalo murmushin da ya tsaya a kan laɓɓansa ya ce

"Barka Jawahir.." Daga haka ya maida duban sa kan Maama ya ce

"Bari na É—an fita.."

"Toh Allah Ya tsare." Maama ta faÉ—a cikin kulawa. Amsawa ya yi da "Ameen" yana ficewa daga É—akin. Jawahir ta bi shi da kallo tana jin wani irin farin ciki na ziyartar ta. Wato duk lokacin da aka ce wannan kyakykyawan, haÉ—aÉ—É—en guy É—in ya zama mallakinta nata ita kaÉ—ai, ba ta san kuma a wane yanayi za ta tsinci kanta ciki ba.

"Allah sarki! Kin ga har yanayinsa ya ɗan chanja wallahi. Taimako ɗaya za mu masa mu nuna masa ƙauna ta hanyar aura masa Jawahir a kurkusan nan ko don ya manta da raɗaɗin da mace ta sanya shi a ciki." Momy ta sake faɗar hakan bayan fitar Tareeq babu daɗewa. Sauke numfashi Maama ta yi, ita kam i zuwa yanzu ai ya ci a ce ta bar maganar gaba ɗaya ko don fahimtar da ta yi ba ta da ra'ayi a kai. Don ita dai haka kawai ta ji haɗin bai kwanta mata ba. Musamman kuma da ta san halin Tareeq ɗin. Ga kuma abin da ya faru.

"Amma me ya sa ba ki samu Yayanki ko Dadaji kin mata maganar ba?" Murmushi Momy ta yi kafin ta ce

"Ke fa ke ce mahaifiyar Tareeq. Ke kika fi dacewa na fara tuntuɓa da wannan maganar. Idan har ke kika fara masa maganar zai fi ɗaukar ta da muhimmanci. Kin fi kowa sanin halin ɗanki shi ne dalili."

"Toh shi kenan, Ubangiji Ya zaɓa abin da ya fi zama alkhairi."

"Ameeeeen.." Momy ta faÉ—a tana jan Ameen É—in cikin farin ciki.

... A nutse ta ƙarasa fitowa daga cikin ɗakin jikinta a matuƙar sanyaye. Don haka kawai ta ƙi jinin kiran Dada, domin da wuya idan na alkhairi ne. Ƙarasawa ta yi ta nemi waje ta zauna cikin ladabi ta ce

"Dada ga ni." Ƙarasa abin da take Dada ta yi, kafin ta dawo ta nemi waje ta zauna gefen Baffa ta ce

"Toh ke sai ki fara shiri, domin kuwa mun yi miki miji. Miji ya zo, Baffanki ya gan shi ya masa, ni ma kuma na gan shi ya yi mini. Don haka gobe zai zo ki je ku gaisa. Ba wani da yawa za a saka ba, cikin ƙanƙanin lokaci za a yi komai a gama." Dada ta faɗa maganar tamkar da ita mutumin da ya zo suka yi magana. Tun lokacin da Dada ta ambaci miji ta ji zuciyarta ta buga. Ba ta tsaya ba, sai cigaba da bugawa da ta yi. Ta runtse idanunta tana tuna lokacin da suka gabatar mata da Alhaji Baita a matsayin mijin da za ta aura. Daga zuwa siyar nono. Ba tare da sanin waye shi ba. Mene ne asalinsa, su waye iyayensa duk ba su sani ba. Haka kawai suka ɗauke ta suka ba shi don kawai ya yi musu ɓarin kuɗi. Toh idan kuma shi ma wannan ɗin halinsa ɗaya da Alhaji Baitan fa? Abin da ya fara zuwa kwanyarta kenan, tana jin wani sabon tashin hankalin na ziyartar ta. Duk wani tunaninta, burinta, da duk wani fatanta ba ya wuce a kan inganta rayuwar 'ya'yanta. Toh idan dai har suka ce ta yi aure yaya rayuwar 'ya'yanta za ta kasance? Ko kuwa wanda suka sake zaɓar mata a karo na biyu zai yarda ya riƙe 'ya'yanta? Tunanin nata ya katse ne, lokacin da hayaniyar da ake a waje take sake kusanto gidansu.

"Ɓarawo, Ɓarawo.." Shi ne abin da kafatanin mutanen ke faɗa cikin ɗaga murya. Haka nan kawai ta ji ƙirjinta ya sake bugawa a karo na barkatai. Daidai lokacin da aka soma buga ƙofar gidan da ƙarfi, wanda ke bugawa ɗin yana faɗin

"Ina mutanen gidan suke ne? Ku fito tun kafin in ba wa mutane umarnin shigowa su muku rashin mutunci wallahi. Ku fito na ce.." Ya ƙare maganar yana sake dukan ƙofar kamar wanda ze jijjige ta. Kusan a tare dukansu suka miƙe. Daneen ma da ke cikin ɗaki ta yo tsakar gidan babu shiri. Gaba ɗaya suka nufi ƙofar gidan don ganin abin da ke faruwa, ko kuma ma ya farun..

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 07

__ Dandazon mutanen da ta gani a ƙofar gidan nasu, shi ne abin da ya sake tsinkar mata da gaba. Ta runtse idanunta tana ambaton sunan Allah, lokaci ɗaya tana buɗe idanun, a daidai lokacin da ta sauke idanunta a kan Habule da ke riƙe da kwalar rigar Ameer. Ya cukwuikuye ta kamar wanda ke shirin zame ta daga jikinsa.

"Ɓarawo." Kunnenta ya sake tsinto mata wannan kalmar.

"Ya isa haka.." Mutumin da ke riƙe da kwalar rigar Ameer ya faɗa bayan ya yi amfani da hannunsa wajen alamta musu abin da ya faɗa. Kamar dama shi ya saka su, sai kuwa suka yi shiru.

"Ameer." Daneen ta faÉ—a idanunta da take suka sauya a kan Ameer, ban da lugude babu abin da zuciyarta take.

"Na shiga 3 ni Hanne.. Me kuma ya faru?" Dada ta faɗa har da dafe ƙirji kamar gaske.
Chapter 10 · 0% Book details