Sashe 19
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mu je in wanke miki kai." Matar nan ta faɗa tana kallan ta. Ita ma kallan ta Daneen ta yi kafin ta juya a hankali ta koma cikin banɗakin. Haka tana ji tana gani, ta buɗe kanta a gaban matar, ta shiga wanke mata sassalkan gashin kanta da ya fi kama da wanda ya jiƙu da tsadaddun maya-mayai. Yadda yake a kwance, a miƙe sai ka ɗauka wani shahararren gyara take masa na fitar hankali. Hakan ne ya sa ba su daɗe ba ta wanke mata kan da ruwa kafin suka fito. Ita ta taimaka mata ta gyara mata kan tsaff ta tufke mata shi da wani ribbon, ya kuwa zuba har gadon bayanta. Tana gama wa kuwa Daneen ta ɗauki ɗankwalin da ta cire ta lulluɓe kanta, don ta riga ta saba idan dai har ba a gaban Innarsu ba ko Ameer ba ta taɓa iya buɗe kanta. Sai ga shi yau wata ce ma ta wanke mata.
"Kar ki mayar da kayan nan, ki bari yanzu zan kawo miki wasu." Matar ta faɗa tana ƙoƙarin juya wa. Bin ta da kallo Daneen ta yi, ba don ba don ba da sai ta ce matar nan ta fiya iyayi. Dan dai kawai babba ce. Ta gyara zama tana cuno bakinta fuskar nan a haɗe.
***
Ta kai wajen mintina goma tana juya wayar a hannunta, ta rasa ta ina za ta fara. Number Abdoul ta daÉ—e cikin wayarta, ji take kamar ta kira su gaisa ko ta É—an samu sassaucin abin da take ji a cikin zuciyarta. Sai dai da ta kai hannu za ta kira, sai ta fasa. Ba ta so ta yi wani abu ba tare da sanin Yah Tareeq ba.
"Sultanah." Ta jiyo muryar Maami ta ambata daga gefen ta. Da sauri ta É—aga kai ta kalli Maamin, don kwata-kwata ba ta ji zuwan ta wajen ba. Tsaya wa ta yi tana kallan ta na tsawon sakanni, kafin ta gyara tsayuwarta.
"Ba ni wayarki na gani." Maami ta faɗa cikin tsare gida tana kallan Sultanah. Jikin Sultanah a matuƙar sanyaye ta miƙa wa Maamin wayar idanunta a kan fuskarta. Daidai lokacin da wayar Maamin ta shiga ruri, ta kalli mai kiran ta, kafin ta maida duban ta kan Sultanah ta ce
"Kar na ji kar na gani Sultanah." Ta faɗa tana miƙa mata wayar. Jinjina kai ta yi da sauri, tana saka hannu ta karɓi wayar. Maami ta yi cikin ɗaki tana amsa wayarta, ya yin da Sultanah ta bi ta da kallo. Ita gaba ɗaya ta kasa fahimtar Maamin a kwana biyun nan. Gaba ɗaya ta kasa gane dalilin da ya sa ta saka mata idanu a kwanakin nan, bayan hakan ba ɗabi'arta ba ce. Yah Tareeq ya fi kowa saka wa rayuwarsu ido ita da er'uwarta, sai dai ga shi cikin kwanaki kaɗan gaba ɗaya Maamin ta bi ta sauya, ta tsiro da wani nau'i na takura, wanda kwata-kwata ba ta saba da shi ba. Ta sake rungume wayar cikin tafin hannunta tana rasa ta inda za ta fara. Gaba ɗaya zuciyarta a dame take, ta rasa yadda za ta yi. Ko ishashshen bacci ba ta samu a kwana biyun nan.
***
"Yah Tareeq don Allah ina son mu yi wata magana." Shi ne saƙon da ya gani a saman wayarsa bayan ya kunna ta. Cikin mamaki ya ɗan ƙanƙantar da kyawawan ƙwayar idanunsa yana kallan number da ta turo saƙon. Maimaita saƙon ya sake yi kafin kai tsaye ya danna kiran number Sultanah yana miƙe wa tsaye. Ya riga ya san idan har irin haka ta faru, toh tabbas wani babban abu ne. Kwata-kwata ba shi da wasa a kan duk wani abu da ya shafi ƙannensa. Sanin hakan ne ma ya sa ko da wani abu ne ya faru, shi suke fara samu da maganar, ko da wata matsala ce shi suke sanarwa. Shi kuma ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya magance musu ita da taimakon Ubangiji. Tun da kuma ya ga Sultanahn ba ta kira shi kai tsaye ko ta masa magana da baki ba, ya san tabbas wani abun ne.
"Sultanah." Ya ambata lokacin da ya fara taka wa kamar mai shirin fita daga office É—in.
"Na'am Yah Tareeq." Ta faÉ—a a sanyaye.
"Ba ki da lafiya ne?" Ya tambaya a nutse, kamar wanda ba ya so a ji abin da ya faÉ—a. Girgiza kai ta yi kamar yana kusa da ita kafin ta ce
"A'ah lafiya ta ƙalau."
"Ohk, kina gida?"
"Eh, ina nan." Ta ba shi amsa tana tashi zaune daga kwancen da take.
"Toh mu haÉ—u palourn Dadaji." Ya faÉ—a, sanin da ya yi ta ji shi ne ya sa kafin ta kai ga amsa wa ya tura wayar cikin aljihunsa ba tare da ya kashe ba ya fice daga office É—in.
***
A ɗaya ɓangaren kuwa tana nan zaune bayan wajen minti 10 sai ga matar ta dawo hannunta ɗauke da wasu kaya cikin leda. Ta ƙarasa inda ta bar Daneen da kalle-kallen tsarin da aka yi wa ɗakin ta ajje kayan kafin ta ce
"Ga shi nan ki saka, zan jira ki a palour. Kar ki daÉ—e."
"Tohm." Ta faɗa a ranta tana tunanin irin wannan iyayin. Don kawai za su yi musu aikin wanke-wanke da shara har sai sun yi wanka, har da wani wanke kai da wasu kaya. Ita ba ta san haka en birnin suke da fi'ili ba. Matar ba ta sake cewa komai ba ta fice daga ɗakin. Daneen ta bi ledar da kallo, kamar ba za ta taɓa ba. Sai kuma ta janyo ta, ta shiga fidda kayan da ke ciki. Rigar da ta soma gani ta ɗaga tana kalla. Rigar ta fi kama da irin ta arnan nan, domin kuwa idan mutum ya saka, wuyansa duk a waje yake. Don kuwa har rabin ƙirjinsa kan iya fito wa. Ta jinjina kai tana cigaba da kallan rigar.
"Chaɓɓ! Wace er iska? Wallahi ba zan saka ba." Ta faɗa tana hararar kayan. Abin da ta ji ya faɗo daga cikin rigar shi ne ya sanya ta kai idanunta ƙasa. Ta ajiye rigar hannunta, tana kai hannu ta ɗauki abin da ya faɗi ɗin. Da mamaki take bin abin da ta gani a hannunta. Idan dai har idanunta ba su yi ƙarya ba, sharbale ce take gani. Ta kai hannu ta toshe bakinta cike da mamaki. Ita duk sai ta ji kunya ma ta kama ta. Duk da tun a ƙauyensu Inna ta siya mata half vest amma ai ba ta kai ta saka sharbale ba, dududu ma nawa take? Ina ƙudan yake ballantana romonsa? Jefa ta kan gadon gefen ta ta yi tana faɗi a fili
"Babba da ita amma ga wani iskanci." Ta ƙare maganar tana harara tamkar idanunta za su faɗo.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 13
Ta kai wajen mintina goma zaune a gefen gadon tana ta saƙe-saƙe. Tana kuma cigaba da kallan cikin ɗakin. Sai ji ta yi an taɓa ƙofar ɗakin. Da sauri ta ɗaga idanunta ta kalli mai shigowar. Matar ɗazun nan ce dai, tun da ta shigo take kallan ta, har ta ƙaraso. Da mamaki shimfiɗe a kan fuskarta ta ce
"Me kike jira har yanzu ba ki shirya ba?" Ta tambaya tana sauke idanunta a kan kayan da ta ba ta. Ita ma Daneen kayan ta kalla kafin ta maida duban ta kan matar ta ce bayan ta girgiza kai.
"Ba zan iya sakawa ba." Sake kallan kayan matar ta yi, kana ta sake maida duban ta kan Daneen ta ce
"Ba su yi miki bayanin abin da za ki yi cikin gidan nan ba?" Ta tambaya a mamakance. Ba don ta fahimci abin da matar ke nufi ba ta girgiza kai. Matar ta shiga jinjina kai na tsawon sakanni, kafin ta juya ta fice daga ɗakin. Daneen ta bi ta da kallo tana mamakin wane irin gida ne wannan suka kawo kansu? Ko kuwa dama haka en birnin suke? Haka suke saka kaya waɗanda marabar su da babu duk ɗaya ne? Ita dai ba zuwa ta taɓa yi ba, ballantana ta san haka ɗin ne ko ba haka ba. Tana nan zaune bayan shuɗewar wasu mintuna, haka nan ita dai ta kasa samun sukuni da zaman. Ban da bugun zuciyar da ya ɗan yi sanyi yanzu da take ji. Sai kuma yadda kusan rabin hankalinta na kan ɗan'uwanta. Ɗaga dogwayen lashes ɗinta ta yi ta kalli ƙofar ɗakin jin da ta yi an turo. Maimakon ɗazu, yanzu su biyu suka shigo da Aunty. Kallan ta Aunty take yi tun daga ƙasa har sama. Wato duk yadda ake so yarinyar nan ta kai. Ta riga ta san tabbas yau kuɗin da za ta samu suna da yawa. Kyau Allah Ya ba wa yarinyar. Gashi tamkar er india. Duk da yadda take babu wayewa, hakan bai hana kana mata kallo ɗaya ka gano tsantsar tsagoron kyawun komai da Allah Ya ba ta ba. Duk kuwa da ƙananan shekarunta hakan bai hana fitowar dirinta ba. Ita har tunani take idan da ta fi haka girma da ya za ta gan ta? Murmushi ne ya suɓuce mata a kan fuska, lokacin da ta ƙarasa dab da Daneen. Gabanta ya yanke ya faɗi, ta ɗan lumshe kyawawan fararen idanunta da babu kwalli cikinsu.
"Ga waɗannan kayan maza ki saka ana jiran mu." Aunty ta faɗa tana watsa mata wani sassanyan murmushi. Ba ta san lokacin da ajiyar zuciya ta ƙwace mata ba, ta saka hannu ta karɓi kayan, ba tare da ta ce komai ba ta shiga duba su. Kaya ne irin na mutane masu mutunci, riga da skirt. Sai a lokacin ta ji hankalinta ya kwanta. 'Wato kenan wannan ta fi waccan matar hankali' Ta raya hakan a cikin zuciyarta. A fili kuma sai ta ce
"Toh." Daga haka ta juya banɗaki don sakawa. Har matar nan na ƙoƙarin dakatar da ita, Aunty ta yi azamar dakatar da ita ta ce
"Rabu da ita, bi ta a hankali, yarinya ce." Jinjina kai matar ta yi ba tare da ta ce komai ba.
"Ki kawo mini ita palourn ƙasa ina jiran ku yanzun." In ji Aunty.