← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 49

Sashe 4

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh ki yi da jiki." Ya ƙare maganar yana fice wa daga cikin ɗakin. Ta bi shi da kallo kamar me son gano wani abun. Sai da ya ida ficewa kafin ta dawo da duban ta kan Daneen. Tun dawowar ta gidan har zuwa yau ɗin nan bai taɓa kula ko tambayar lafiyar Daneen ba, bai taɓa jin yaya ta kwana ko yaya ta tashi ba. Bai taɓa damuwa da ya ɗauke ta ba, ko da hakan zai janyo ƙauna ta shiga tsakanin su ba. Shi dai kawai abin da ya sani, tun da ba ya son cikin, ko da ta haihu ma ba ya ƙaunar abin da ta haifa ɗin. Tun da da ma kamar yadda yake faɗa, be aure ta ba ne don ta haihu. Sai da ta tabbatar ta ƙoshi sosai kafin ta ɗauke ta kamar yadda aka saba ta kai ta wajen Atika kafin ta wuce ɗakin Alhaji Baita.

.. Su uku ne zaune a kan dinning suna break, Alhaji Baita, Hajiya Amina sai Inna-wuro da ke zaune, ita ba cin abincin take ba, sai dai ta riƙe cokali ne kawai tana caccakawa cikin abincin. Hira Alhaji Baita da Hajiya Amina (Abokiyar zaman ta) suke, sam hankalinta ba ya wajen. Ƙoƙari kawai take ta iya tare kanta, ta riƙe kanta kar wannan ƙamshin abincin da ke tashi ya sanya ta yin amai. Wani yamutsawa da 'ya'yan cikinta suka yi, shi ne ya sanya ta jefar da cokalin hannunta. Ta guntse bakinta tana jan wata ajiyar zuciya, duk don kar ta yi abin da take ta gudu, ko don gudun tonuwar abin da ta riga da ta tabbatar da lallai tabbas shi ne. Sai dai ina kwata-kwata ta kasa, cikin sauri ta miƙe ta nufi toilet ɗin da ke cikin palourn ta shiga kwara amai kamar za ta amayar da kayan cikinta. Cikin sauri Hajiya Amina ta ajje cokalin hannunta, ya yin da Alhaji Baita har bai san lokacin da cokalin hannunsa ya suɓuce ba. Cikin tashin hankali suka bi ta da kallo, sai dai babu wanda ya iya furta komai. Har bayan wajen minti 5 sannan Inna-wuro ta fito daga banɗakin cikin mutuwar jiki, ba tare da ta kalli inda suke ba, ta fara ƙoƙarin komawa ɗakinta cike da fatan kar ya yi mata magana. Sai dai tun kafin ta yi taku 5 ta jiyo muryarsa cikin kaushi yana faɗin

"Ke!" Dakatawa ta yi jikinta na É—aukar rawa, ta runtse idanunta daidai lokacin da ta sake jiyo muryarsa yana faÉ—in

"Kar ki sake ki je ko'ina, ƙaraso wajen nan tun kafin raina ya ɓaci na yi miki abin da ba za ki taɓa mantawa ba." Cike da sassarfa ta juya akalarta zuwa inda suke. Tun kafin ta ƙaraso ta jiyo muryarsa da ke ɗauke da zallar tuhuma ya ce

"Me ye ma'anar wannan aman da kika yi? Me kike nufi? Ciki ne da ke?" Ya yi tambayar duka a jere. Kasa É—aga ido ta yi ta kalle shi, ballantana ta ce wani abu. Ta rasa me za ta ce, ta rasa ya za ta yi, gaba É—aya kanta a kulle yake.

"Tambayarki nake ciki ne da ke?" Ya yi maganar yanzu a tsawace. Runtse idanunta ta yi tana jin yadda ta ji muryar tasa har cikin kanta. Ta buÉ—e baki da niyyar yin magana, ya katse ta da faÉ—in

"Kar ki sake ki faɗa mini ba daidai ba, sanar da ni abin da ke faruwa da gaske. Ciki ne da ke?" Jijjjiga kai ta shiga yi tamkar wata ƙadangaruwa, har lokacin kuma ba ta kalle shi ba.

"La ha ila ha illal lahu.." Hajiya ta soma faɗa tana tafa hannu. Shi kuwa Alhaji Baita shiru ya yi don gaba ɗaya kansa ya kulle, ya ma rasa me ya kamata ya yi. Ciki? Ciki ne da Fatiman? Abin da yake ta masa yawo a ƙwaƙwalwarsa kenan. Ya sauke wani zazzafan numfashi yana tunanin ta ina zai fara? Tabbas yana ƙaunar Fatima, uwa uba kuma jikinta. Kaff matansa, da duk irin aure-auren da yake har yanzu bai samu irin Fatima ba. Duk kuwa da ta haihu, amma kullum jin ta yake kamar sabuwa. Sai dai duk da haka ba ya tunanin ze iya zama da ita. Don yana da tabbacin idan dai har ya cigaba da zama da ita, toh kowacce shekara sai ta haihu. Be san yawan adadin shekarun da za su ɗauka tare ba tare da ya gaji da ita ba, kenan 'ya'ya nawa za ta haifa? Ya kuma san ko me ze yi ba za ta yarda a yanke mahaifarta ba, don kuwa ya kwana da sanin ko kaɗan dukiyarsa ba ta gaban ta.

"Ciki kika sake yi?" Tambayar da ke ta masa yawo a ƙwaƙwalwa, ta samu damar fitowa kan laɓɓansa yana kallan Inna-wuro. Da mamaki ta ɗaga jajayen idanunta tana kallansa, kafin ta kai ga cewa komai Hajiya Amina ta ce

"Toh ai Alhaji ina ganin kamar laifinka ne, garin yaya ka bar ta ta shigo cikin gidan nan da mahaifa? Ka san fa 'yan ƙauye da ma akwai zilama." Be bi ta kan abin da Hajiya Amina ta faɗa ba, duk da ta wani ɓangaren maganar tata ta shige shi, amma kuma tun da mai afkuwa ta afku zancen yaushe kuma?

"Wai ba kafin mu shigo gidan nan sai da na kai ki asibiti aka tabbatar mini an tsayar da haihuwar ba? wace irin zulamammiya ce ke? Duk da planning ɗin da kika yi amma sai da kika ɗauki ciki?" Alhaji Baita ya ƙarasa maganar yana jin yadda zuciyarsa ke tururi, tarin baƙin ciki da ɓacin rai na sake tunzura fusatacciyar zuciyarsa.

"Ka yi haƙuri Alhaji." Hajiya Amina ta faɗa cikin salo na kwantar da murya.

"Kin ga maza je ki tattara kayanki ki bar mini gida, ki ɗauki abin da kika haifa, da wannan cikin da ke jikinki ki fice a gidan nan. Wallahi ba zan iya cigaba da zama da ke ba. Idan na ce duk macen da na aura za ta haihu, 'ya'ya nawa zan tara kenan? Ni ba don ki haihu na auro ki ba. Na auro ki ne don ina son zama da ke ke kaɗai, amma saboda ƙauyanci da gidadanci cikin watannin da za a ƙirga su a hannu har kin yi ciki biyu? Ba zan iya ba. Ki je na sake ki saki uku, na kuma yafe abin da kika haifa da kuma wanda za ki haifa nan gaba. Ki je ki riƙe kayanki ba na so, ke kar ma ki taɓa tunanin suna da uba. Kar kuma ki taɓa nuna musu suna da uba. Ki manta cewar ba ke kaɗai kika haife su ba, na yafe har gaban abada. Ke ke kaɗai kika haife su. Saboda haka ke da kika haifa ke kaɗai suke da. Na bar miki su halak malak."

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 03

__ Idanunta a runtse suke tun daga lokacin da ya fara magana har ya kai ƙarshe. Duk yadda ilahirin jikinta ke rawa hakan be sanya ta yi yunƙurin nema wa kanta waje ta zauna ba. Kalaman Alhaji Baita ne kawai ke cigaba da yi mata amsa-kuwwa cikin kunnenta. A hankali wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro daga cikin Idanunta da har lokacin suke a rufe. Cikin ƙanƙanin lokaci bugun zuciyarta ya ƙaru fiye da farkon lokacin da ya fara magana.

"Ki bar wajen nan." Ya faɗa a zafafe yana nuna mata hanya, ba tare da ya kalle ta ba. Don ba ya so ya kalle ta ɗin ka da wani abu ya ɗarsu a ransa, har ya saka ya yi nadamar abin da ya aikata. Ya riga ya tabbatar wa kansa daga yau Fatiman ba tasa ba ce, komai nata ya zama ba nasa ba. Saboda haka kamar yadda ya yanke alaƙarsa da ita har abada ba ya so ya sake kallon fuskarta, jikinta ko kuma ma duk wani abu da ya dangance ta. Maganar da ya yi ita ce ta sake tuna mata da zafafan kalaman da suka yi nasarar jefa zuciyarta cikin wani irin yanayi mara misaltuwa. A hankali ta ɗaga ƙafafunta da suka mata nauyi ta soma takawa don barin wajen, daidai lokacin da ta buɗe idanunta da suka rine suka yi jajir, hawaye sun cika sun tumbatsa cikin idanun, wanda hakan ya sanya take ganin dishi-dishi. Bugu da ƙari kuma maganganun nasa da suka sanya jinta da ganinta ya ɗauke na wucin gadi. Babu abin da ke cigaba da zama daram a ƙwaƙwalwarta, suka fi kuma kowaɗanne kalmomi maimaita kan su sai

"Ke da kika haife su ke kaÉ—ai suke da. Na bar miki su halak malak."

Da ƙyar ta iya kai kanta ɗaki, sai a lokacin zuciyarta da ke cunkushe, ta ba ta damar fashewa da wani irin kuka me cin rai. Kukan da ke fito wa tun daga ƙasan zuciyarta, me zafi wanda ke taimakawa wajen rage raɗaɗin da zuciyarta ke ciki. Ta kwashe fiye da rabin awa tana kukan, ta kasa hana kanta dena wa. Ba sakin da Alhaji Baita ya yi mata ne ya fi damunta ba, face yadda ya nuna ba ya son abin da ta haifa, da wanda za ta haifa nan gaba, wanda ke cikinta a yanzun. Shin ya rayuwar 'ya'yanta za ta kasance idan suka taso suka gane waye mahaifinsu? Wane hali za su tsinci kansu duk lokacin da suka ji labarin mahaifinsu ba ya son su tun samun cikinsu har haihuwarsu? Har ma an saki mahaifiyarsu ne saboda haihuwarsu? Haihuwar da wasu suke ƙarar da dukiyarsu da duk abin da suka mallaka don su samu. Haihuwar da a kanta wasu suke fitowa daga gidajensu. Lallai Allah mai mabambantan halittu, masu kuma mabambantan halayyya. Wani numfashi ta ja tana runtse idanunta, kafin ta miƙe ta ƙarasa inda Daneen take, ta ɗauke ta ta saɓa a baya. Hijab kawai ta ɗauka, ta ɗauki kuɗin da ta san ze kai ta gida, bayan nan ba ta taɓa komai da ke cikin gidan ba. Don kuwa ba ta buƙatar komai da ya dangance shi kuma. Kai tsaye ficewa ta yi daga ɗakin. Dab da za ta gifta inda suke zaune, Alhaji Baita ya saka hannu cikin aljihunsa ya fito da kuɗi, ya jefa mata ƙasan ƙafarta daidai lokacin da ya ce
Chapter 4 · 0% Book details