← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 49

Sashe 32

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki ƙara gode wa Allah, saboda da alama an yi aikin nan cikin nasara. Ameer na dab da samun lafiya." Ba ta san lokacin da wani murmushi ya suɓuce mata ba, sam sai ta kasa amsa wa Yohanah maganarsa, ban da ƙarasawa ciki da ta yi don ta gane wa idanunta. Shi ma bai damu da amsar tata ba ya wuce ta gaban su Hidaya da babu wadda ta kalle shi har ya bar wajen.

Cike da sassarfa take ƙarasa wa cikin ɗakin idanunta a kan Ameer da idanunsa ke a lumshe.

"Ameer." Ta faɗa tun kafin ta ida ƙarasawa inda yake. Kamar a mafarki ya ji muryar 'yar'uwarsa, don bai taɓa tunanin zai sake buɗe idanu ya ga wani ɗan'adam ba, a lokacin da za a masa aiki. Sai ga shi da alama an gama masa aikin, ga shi kuma zai ƙara ganin 'yar'uwarsa. Abin da dai bai sani ba kawai shi ne, shin zai sake ganin Inna-wuro?

"Ameer." Daneen ta sake faɗa tana riƙo hannayensa. Wasu irin ƙwalla ne suka sakko daga cikin idanunsa zuwa kan kuncinsa.

"Addatah." Ya faÉ—a muryarsa a wani irin cunkushe.

"Na'am Ameer, ka warke koh?" Ta tambaya tana jin wani irin farin ciki na ziyartar ta. Murmushin yaƙe Ameer ya yi kafin ya ce

"Ba na tunanin har abada zan warke Addaneen. Ina ji a jikina kamar ba zan ƙara ganin Innarmu ba, duk da yadda nake son ganinta. Na so a ce na ga babanmu kafin na tafi na bar ki Addatah. Ban san zuwanmu garin nan shi ne silar rugujewar farin cikinmu ba, da ban matsa mun taho ba. Ban san neman kuɗin koma wa ƙauyenmu zai sake zama wani ɓangare na wargajewar farin cikinmu ba, da ban nema ba. Na yi nadama matuƙa, na janyo wa kaina. Kalli yadda mutanen nan suka lalata mini rayuwa, zuciyata kuma rauninta na da yawa shi ya sa ta kasa daurewa. Adda kin san su ɗin su waye?" Kallon sa kawai take yi tun da ya soma magana har ya dakata, ji take gaba ɗaya maganganun kamar ba na Ameer ba, kamar ba Ameer ɗinta ƙaninta mai tarin ƙuruciya da shiririta ba. Sai ta ji maganganun da suke fitowa daga bakinsa tamkar wanda wani babba yake yin su. 'Shin me yake shirin faruwa?' Ta tambayi kanta tana maida dubanta kan Ameer.

"Ni na faɗa maka ina buƙatar sanin su waye su Ameer? Wanne irin maganganu ne suke fito wa daga bakinka Ameer? Ba ka da hankali ashe dama?" Ta faɗa tana jin yadda ilahirin jikinta ke karkarwa tamkar mazari. Girgiza kai Ameer ya yi, ya yi nasarar kamo hannun Daneen cikin nasa ya ce

"Ban sani ba ko Allah zai sa ki samu dama ki shigar da su ƙara Addah, ban sani ba ko bayan raina za ki buƙaci sanin sunan mutanen da suka datse mana farin cikinmu, suka yi mana katangar ƙarfe da rayuwarmu mai daɗi, suka kuma zamo sanadiyyar rabuwarki da ɗan'uwanki." Wani mari Daneen ta kai wa Ameer a gigice tana jin yadda jikinta ke ci gaba da ɗaukar rawa. Tuni idanunta sun soma zubar da hawaye. Jin maganganun Ameer ɗin take har cikin kowacce gaɓa ta jikinta.

"Ameer ba ka da hankali? Ba ka da hankali ashe dama? Ashe ba ka sona Ameer? Ashe ka tsane ni Ameer ban sani ba? Wasu irin maganganu kake faɗa haka mara sa daɗin ji? Toh ko dai so kake zuciyata ta tarwatse?" Ta tambaya cikin kuka tana kallon yadda ya runtse idanunsa. Duk da yadda ya ji zafin marin, amma hakan bai sa ya ji ya karaya ba. Shi kaɗai ya san me yake ji yanzu haka a cikin gaba ɗaya jikinsa, wasu abubuwa yake ji waɗanda ko za a kashe shi ba zai iya kwatanta su ba. Hannunsa ya saka da iya ƙarfin da yake da shi ya janyo Daneen ɗin, idanunsa a lumshe ya saka bakinsa saitin kunnenta ya soma faɗi a wahalce, sannan kuma a rarrabe, a kuma hankali.

"Ki yi haƙuri Adda, ko da za ki buƙaci sanin su waye su.." Sai ya dakata a nan yana sake riƙe hannun Daneen da masifar gaske.

"Ki fara shari'a da yaron gidan Alhaji Dikko, shi ne shugaba kuma ogan duk waɗanda suka yi amfani da.." Maganar da ta kasa fita kenan, saboda wani yunƙuri da ya yi. Cikin second ɗaya ya saki hannun Daneen, wanda hakan ya tilasta mata saurin kallon fuskarsa. Numfashinsa ne yake fita da wani irin sauri, tuni idanunsa suka soma ƙaƙƙafewa, ya yin da ya fara wata irin shaƙuwa. Wani mahaukacin karkarwa da jikinta ke yi shi ne ya sanya ta runtse idanunta. Ta buɗe su a kan Ameer da ta ga yana wasu abubuwa waɗanda ba ta taɓa ganin irin su ba. Don haka ta yi saurin riƙo shi tana faɗin

"Ameer." Ta faɗa da ƙarfin gaske, tana ci gaba da kallon yadda yake kokawa da numfashinsa. Kwata-kwata tunaninta bai kawo mata ta je ta kira likita ba, don saboda tsananin ruɗewa, kawai kiran sunansa take. Sai zuwa can da ta ga dai babu sauƙi sai a wajen Allah, hakan ne ya sanya ta sakinsa, ta sake sauke luhu-luhun jajayen idanunta a tsakiyar kyakykyawar fuskar Ameer daidai lokacin da ya ja wata ƙatuwar ajiyar zuciya, ta juya don zuwa kiran Likita. Sai dai a maimakon ɗazu da sautin fitar numfashin Ameer ya cika dodon kunnenta, sai ta ji shiru. Cakk ta dakata tana buɗe idanunta da har wani rufewa suke don kansu saboda tsabar kukan da suka sha har suka gaji. Fata take a ce numfashin nasa ne ya daidaita, ya kuma daina duk wasu abubuwa da ta ga yana yi waɗanda ba ta taɓa gani ba. Sai dai wata daƙiƙiyar faɗuwar gaba da ta ji ita ce ta sanya ta sake runtse idanunta na tsawon sakanni, kafin ta buɗe a hankali ta juya idanunta a kan gadon da Ameer ke kai.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 21

Ƙura masa kumburarrun idanunta ta yi tana kallon yadda gaba ɗaya ya wani miƙe a kan gadon, gaba ɗaya sautin nan nasa da take jiyo wa ta daina ji kwata-kwata. Maimakon ta ji farin cikin fahimtar numfashinsa ya daidaita, sai ta ji wata irin faɗuwar gaba ta ziyarce ta, wadda ta sanya ta saurin runtse idanunta. A hankali ta shiga taka wa zuwa kan gadon, har lokacin idanunta a kan Ameer. Hannunta duka biyun ta saka ta riƙo fuskarsa, a sanyaye ta furta

"Ameer." Ta ƙare sunan da ya gama fita da sautin bugawar zuciyarta. Shiru babu amsa. Ba tare da kawo komai cikin ranta ba ta sake kiran sunansa a karo na biyu, nan ma dai shiru, bai kuma motsa ba, haka zalika bai kalle ta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci jikinta ya ɗauki rawa. Ta sake yin amfani da duka hannayenta biyu wajen riƙo shi, ta shiga jijjiga shi a haukace tana faɗin

"Ameer ka tashi, Ameer ka tashi mana. Meye haka kake yi Ameer? Ameer.." Ta ƙare maganar cikin ɗaga murya. Dalili kenan da ya sa Hidaya da Sultanah da ke waje saurin shigo wa cikin ɗakin. Ko sanin sun wanzu cikin ɗakin ba ta yi ba, a haukace ta ci gaba da faɗin

"Ameer ka tashi mana Ameer ka tashi don girman Allah." Ta faɗa muryarta na wani irin sarƙewa. A tsorace suke kallon abin da ke faruwa tsakanin Daneen da Ameer, gaba ɗaya tashin hankali ne ya bayyana a kan fuskarsu. Sultanah ta kalli Hidaya, murya can ƙasa ta ce

"Sisi je ki kira Likita." Sai da Hidaya ta lumshe idanunta tana jin wani irin tausayin Daneen ɗin na kama ta kafin ta fice daga ɗakin. Babu daɗewa suka shigo tare da Likitan, har kuma zuwa lokacin Daneen ba ta haƙura ba, ci gaba take da jijjiga Ameer tana kiran ya tashi, ya buɗe idanunsa. Hidaya ce ta ƙarasa ta riƙo Daneen tana faɗin

"Bari Likita ya duba shi." Hannu Daneen ta saka tana shirin ƙwace jikinta a lokaci ɗaya tana furta

"Kin gan shi fa ba ya motsi." Ta ƙare tana nuna Ameer ɗin da hannunta ke wani irin karkarwa. Riƙe ta sosai Hidaya ta yi tana faɗin

"Ehh, ki bari ya duba shi." Ta faɗa cikin rarrashi tana rungumo Daneen ɗin. Tun kafin ta kai ta jikinta take iya jiyo sautin bugun zuciyarta da yake fita da wani mahaukacin gudu. Gaba ɗayansu ƙura wa Likitan idanu suka yi, suna kallon lokacin da ya fara gwada Ameer. Daneen ta kafe shi da jajayen idanunta tana jira ta ji abin da zai faɗa. Zuwa can sai ta ga ya zame abin da ya saka a kunnensa, ya kuma ja zanin da ke a iya cinyar Ameer ya rufe masa fuska, ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa, kafin ya juyo a sanyaye idanunsa a kan Daneen da ita ma shi take kalla tamkar idanunta za su faɗo.

"Ameer ba ya tare da mu, Ki yi haƙuri Allah Ya karɓi abinsa." Ya faɗa a sanyaye, don shi kansa ya matuƙar gigita da mutuwar Ameer ɗin, saboda yadda bayan an gama masa aikin ya gwada masa komai ya ga normal, kuma suke saka masa ran samun lafiya da yardar Ubangiji cikin ƙanƙanin lokaci, sai ga shi cikin awannin da ba su da yawa Allah Ya karɓi abinsa. Kwata-kwata ma ba ta ji abin da ya faɗa ba, saboda yadda hankalinta ya koma kan Ameer da ta ga Likitan ya lulluɓe.

"Me ya sa za ka rufe shi? Kar ya kasa shaƙar iska." Daneen ta faɗa bayan ta yi nasarar fusge hannunta daga cikin na Hidaya, ta ƙarasa tana ƙoƙarin buɗe Ameer.

"Ki yi haƙuri Ameer ya koma wajen mahalliccinsa." Likitan ya faɗa don ya ga alama ba ta fahimce shi ba.

"Ƙarya kake yi Ameer ɗina bai mutu ba, Ameer bai mutu ba, Ameer ba zai taɓa iya tafiya ya bar ni ba." Ta ƙare cikin ɗaga murya tana kallon Likitan. Kafin ba tare da ta bi ta kansa ba, ta saka hannu ta yaye lulluɓin da ya yi masa, ya zamana tana iya kallon fuskar Ameer, ta ce tana bubbuga fuskar tasa.
Chapter 32 · 0% Book details