Sashe 35
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Za ki iya zuwa ki huta, za mu ƙarasa maganar." Miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba, duk da yadda ta ji jiri na shirin mayar da ita, hakan bai sanya ta komawa ta zauna ba, ta soma takawa a hankali tana runtse idanunta lokaci bayan lokaci.
"Amma kar ki sake ki sanar da su kina da iyaye a can wani waje. Ka da ki sake ki nuna musu kina da iyaye, na sake maimaita miki. Idan har da gaske a kan ɗaukar fansar ɗan'uwanki za ki je gidan yi, toh kar ki sake su san da wannan maganar. Ki bari tukunna sai bayan komai ya kammala sai ki koma wajen mahaifiyarki da zancen mutuwar Ameer, sai dai kuma tare da kyakykyawan labarin kin ɗauki fansa a kan wanda ya yi sanadin mutuwar ɗan'uwan naki." Maganganun Yohana suka daki dodon kunnenta. Ta ɗan dakata kaɗan, amma ba tare da ta juyo ba. Kenan hakan na nufin za ta ci gaba da zama tare da su ba tare da ta koma wajen Innarta ba? Ko da yake lokaci ne ƙanƙani, daga zarar ta samo wa Yohana abin da yake so, shi kenan Tareeq ya shiga hannu, kamar yadda ya sanar da ita, ta kuma san lokacin ne hukuma za ta ƙwatar wa Ameer haƙƙinsa. Don haka kawai ta jinjina kai, a kan laɓɓanta ta furta.
"Toh." Wanda ita kanta ba ta da tabbacin ya ji ta ko bai ji ta ba, don ita kanta ba ta ji sautin maganar tata ta fita ba. Tamkar wata er maye haka ta ci gaba da takawa don isa ɗakin da aka kwantar da ita. Duk kuwa da irin yadda jiri ke ci gaba da kwasarta, yana ƙoƙarin kifar da ita hakan bai sanya ta dakatawa ba. Gaba ɗaya zuciyarta ta bushe, ta ƙeƙashe, Fansar nan dai ita kaɗai ke yawo a cikin zuciya, ruhi da ƙwaƙwalwarta.
Numfashi Yohana ya fesar lokacin da ta ida ficewa daga cikin É—akin, ya fito da wayarsa yana sake fesar da iska daga bakinsa, har lokacin idanunsa a kan wayar.
"Kai baba shege ne wallahi, ka fiya takura. Toh yanzu ga shi garin abin da na yi da kake ta kushewa ya janyo mana wata hanyar mafi dacewa. Ga shi nan yanzu mafita ta same mu cikin sauƙi. Ya kamata ka sara mini, don wallahi kaina na wuta, ka jira ni gani nan zuwa, idan na zo zan yi maka bayani." Daga haka ya katse wayar yana miƙewa, ba tare da ya bi ta kan kowa ba ya fice daga asibitin.
... Sun fi awa cikin asibitin, amma ta kasa matsa wa ko nan da can ne daga kusa da Tareeq É—in. Duk da wanzuwar Maama, Ummanta har ma da Abeey hakan bai dame ta ba.
"Ya kamata fa a yi maganar auren yaran nan Yaya." Umman Jawahir ta faÉ—a daga inda take zaune tana kallon Jawahir. Shi ma Abeey kallon su ya yi kafin ya ce
"Kar ki damu, daga zarar yaron nan ya samu lafiya, za mu yi magana da mahaifin Jawahir a tsayar da ko sati ɗaya ne. Ban ga amfanin ɓata lokacin ba, saboda haka ku ma ku fara shiri." Cikin wani irin farin ciki Umman Jawahir ta ce
"Alhamdulillahi, Allah Ya ƙara girma Yaya, Ya kuma tabbatar mana da alkhairinsa." Murmushi ya yi kafin ya amsa da
"Ameen." Daidai lokacin da Dada ji ta shigo cikin É—akin, Maama da ba ta daÉ—e da fita ba na bin bayanta. Ta nemi waje ta zauna lokaci É—aya tana amsa sannu da zuwan da suke mata.
"Alhassan har yanzu fa sau É—aya matarka ta zo duba yaron nan." Dada ji ta faÉ—a tana kallon Abeey. Sai da ya É—aga kai ya kalle ta sannan ya ce bayan ya sauke numfashi kaÉ—an
"Ki bar ni da ita Dada ji, babu damuwa." Girgiza kai ta yi ta ce
"A'ah, kar ka yi mata komai. Na tambaya ne dai in ji ko ba ka sani ba, toh amma tun da ka sani ɗin bar ta. Ta ci gaba da duk abin da ta ga shi ne daidai, babu damuwa." Dada ji ta ƙare maganar tana irin murmushin nan na gefen baki.
"Ai Dada ji da kin bar Yaya ya yi mata ko ma mene ne, ban da iskanci kuna cikin gari É—aya, gida É—aya a ce wai sau É—aya ta zo ta duba Tareeq duk uban jikin da yake sha? Mu kan mu da ba ma garin gaba É—aya hankalinmu na nan, ba shi ne dalilin da ya sa muka dawo yau ba. Ai da ba yau za mu dawo ba. Amma ita ki ga abin da take fa."
"Ummu Kulsum ki yi shiru ki bar mutum da halinsa, akwai ranar ƙin dillanci." Dada ta katse ta da faɗin hakan. Jijjiga kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
... Tun da ta shigo Hidaya ke kallon ta. Ta tashi da sauri don ta taimaka mata saboda yadda ta ga tana tafiya tana wani rangaji, sai Daneen ta yi amfani da hannunta wajen dakatar da ita kafin a fili ta furta can ciki.
"Zan iya." Hidaya ba ta takura mata ba, ta koma ta nemi waje ta zauna, ya yin da ita kuma Daneen ta ƙarasa kan gadon ta kifa kanta a kan gwuiwarta ta runtse idanunta. Sai a lokacin sannan ta ji wannan abin da ya tokare mata ƙirji ya soma warwarewa, lokacin da wasu hawaye suka taru a cikin idanunta, kafin ka ce mene wannan sun soma sintiri a kan kuncinta. Wasu zafafan hawaye ne, da suke sakkowa da zafin su, wanda kuma ba na komai ba ne sai na nadama, takaici, da kuma baƙin cikin ba da ƙodarta ga mugu, azzalumi, wanda ba ya tsoron Allah!!
"Yah Tareeq!" Hidaya ta faɗa tana miƙewa bayan ta amsa sallamarsa.
"Wai da kanka?" Ta ambata tana kallonsa murmushi fall kan fuskarta. Shi ma murmushin ya É—an yi kafin ya jinjina kai kawai.
"Alhamdulillahi, sannu, ka ƙaraso Yaya." Babu musu ya ƙarasa shigewa cikin ɗakin a nutse cike kuma da takatsantsan. Ya nemi waje ya zauna kan wata kujera, idanunsa a kan Daneen da ake iya jiyo sautin shashsheƙarta. Sai da ya ɗaga kai ya kalli Hidaya kafin ya ce bayan ya ɗan ƙanƙantar da kyawawan idanunsa.
"Subhanallahi! Har yanzu ba ta bar kukan ba?" Sai da Hidaya ta rausayar da kanta kafin ta ce
"Wallahi kuwa, na rasa yadda zan yi." Hannu ya saka ya É—an murza goshinsa, har ga Allah ya ji mutuwar yaron nan, ba kuma zai so a ce wadda ta zama silar ci gaba da rayuwarsa tana zaune cikin wannan halin ba. Don haka cikin muryarsa mai daÉ—in saurara ya ce
"Sannu.."
"Daneen.. Yah Tareeq.." Hidaya ta faÉ—a tana murmushi.
"Ohh.." ya faɗa yana ɗage girarsa ɗaya. Kamar daga sama ta ji sunan Tareeq da Hidaya ta ambata, sunan da tun da Yohana ya sanar da ita shi ne ɗan gidan Alhaji Yohana ta ji ta tsani jin sunan, ballantana kuma a kai ga ganin mamallakin sunan da ba ta taɓa ganinsa ba. Sai dai tarin abin da ya bar mata danƙare a cikin zuciya na da yawa. Har ba ta san lokacin da ta ɗaga jajayen idanunta ta sauke su a kan Tareeq ba. Karo na farko da ta fara ganin kyakykyawar fuskar Tareeq, wadda a gare ta baƙa ƙirin ce, fuska mafi muni a rayuwarta, fuskar mutumin da ya zamo silar wargajewar farin cikinta. Shi ma wannan ne karo na farko da ya soma ganinta. Idanunta cikin nasa suka faɗa, saboda yadda ta ɗago ba tare da ta shirya ba. Duk da tsananin tasirin da idanun Tareeq ke da shi, hakan bai sanya ta ko da ƙoƙarin janyewa ba ne, sai ma ci gaba da jefa masa wani mummunan kallo da ta yi, tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da zafi, wata uwar wutar fansa na sake ruruwa a ƙirjinta. Cikin basarwa, duk da yadda ya tsargu da irin kallon da take bin sa da shi, sai dai ƙaryar mutum ya fahimci hakan, ya ɗan gyara zamansa kaɗan kana ya ce
"Ya ƙarin haƙuri? Ki yi haƙuri Allah Ya gafarta masa, Ya sa can ta fiye masa nan. Ke kuma Allah Ya saka miki da alkhairi. Na gode sosai, na kuma yaba da ƙoƙarinki." Runtse idanunta Daneen ta yi tana jin yadda kalamansa ke ratsa kunnuwanta, jin tasirin su take tamkar ana soka mata mashi a ƙirji. Jin su take kamar yana watsa mata ruwan zafi tafasasshe.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 23
Har kusan bayan minti ɗaya da gama maganar ba ta ce komai ba. Shi ma kuma bai damu ba, don ko shi wani lokacin ya kan tsinci kansa cikin rashin son yin magana. Musamman ita kuma da take cikin wannan hali, dole ne ya yi mata uzuri. A nutse cike kuma da takatsantsan ya miƙe tsaye ba tare da ya sake kallon inda Daneen take ba ya dubi Hidaya, kafin ya ce komai ta ce
"Yaya sai haƙuri, mutuwar ta taɓa ta sosai wallahi. Tun kuma da aka ce an fitar da gawarsa daga cikin asibitin nan abin ya sake yin gaba. Ka ga duk ta takura kanta, tun ɗazu ba ta umm ba ta umm umm. Kawai dai a takure take." Ta ƙare maganar a dame. Ɗan lumshe idanunsa ya yi, yana buɗe su lokaci guda. A nutse ya ɗan juya ya kalli Daneen kafin ya juyo bayan ya ɗan sauke numfashi. Sai da ya kai hannunsa saitin ƙirjinsa kafin ya ce
"Allah ne Ya sa zan rayu, amma ta sanadin yarinyar nan, saboda haka ki kula da ita tamkar yadda za ki kula da kanki Hidaya. Ko da yaushe ki din ga tuna akwai muhimmiyar tsokarta a jikina, wadda nake tsaye a nan saboda ita." Murmushi Hidaya ta yi, saboda yadda ta ji matuƙar daɗin yadda ya nuna damuwa da kulawa a kan yarinyar da bai taɓa ganinta ba sai yanzun.
"In Sha Allah Yah Tareeq. Ko ba ka faɗa ba wannan ya zame mini dole." Jinjina kai ya yi yana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin, Hidaya ta yi saurin faɗin
"Bari na taka maka." Daga haka suka jera suka fice daga É—akin.