Sashe 39
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Book 1
Pg 25
Kamar yadda ya kwatanta mata haka ta yi, kamar wadda ya koyawa ga ta ga shi, sai ga shi har ta gane duk abin da ya koya matan. Maganarsa ce kaɗai cikin Whatsapp ɗin, don haka kawai sai ta taɓa sunan nasa da ya yi saving da YOHANA B. Tarin messages ne, duka daga shi ɗaya. Har bayan ta shiga ma wasu ba su daina shigowa ba. Tsayawa kawai ta yi tana kallon ikon Allah. Duk da ya yi mata bayanin komai, amma a wannan karon kuma ba ta san mai za ta yi ba. Amma dai sai ta shiga karanta saƙonnin da suke a rubuce ɗaya bayan ɗaya. Daidai lokacin da wayar ta soma ƙara kenan. Yanzun ma dai shi ke kira, don haka ta ɗaga tana kara wa a kunnenta.
"Kina ji na?" Shi ne abin da ya faÉ—a. Ta jinjina kai tamkar tana gabansa. Sai kuma tunawa da ta yi ba ya ganin ta ya sanya ta buÉ—e bakinta ta ce
"Ehh.." Nan da nan ya shiga yi mata bayani tamkar ɗazun. Ta yi shiru tana saurara, da kiyaye duk abin da yake faɗa mata. Wajen mintina 20, sannan suka yi sallama. Sai a lokacin ta koma cikin Whatsapp ɗin suka ci gaba da magana ta nan. Ƙura wa wayar idanu ta yi tana kallon takardun da ya turo mata. Ta iya karatu daidai gwargwado, saboda haka ta shiga karanta duk abin da ta gani rubuce a jikin takardar. Wasu abubuwan ta fahimci me ake nufi, ya yin da wasu suka yi mata tsaurin fahimta. Hakan ne ya sa maimakon ta fahimci abin da take karantawa, sai ya zamana kawai karantawar take yi ba tare da tana fahimtar komai ba. Don inda ba ta fahimta ba, ya fi inda ta fahimta sau fiye da biyar. Taɓe baki ta yi, tana mamakin dalilinsa na son nemo masa irin takardun.
"Ashe ma shi duk a kan takarda yake wannan abin." Ta raya hakan cikin zuciyarta tana ɗan juya manyan idanunta. Shiru kuma ta yi na tsawon mintuna, kafin murmushin gefen baki ya ɗan bayyana a kan laɓɓanta, murmushin da yanzun ya maye gurbin murmushinta tun bayan mutuwar Ameer. Ba ta taɓa tunanin bayan ganin gawar ɗan'uwanta za ta iya ci gaba da walwala ko murmushi ko da kuwa na yaƙe ne ba. Ba ta taɓa tunanin idan Ameer ya rasu za ta iya ci gaba da rayuwa ba. Sai ga shi ta iya rayuwar, har ma ga shi tana iya murmushi. Ta ɗan lumshe idanunta da lokaci ɗaya kalarsu ta sauya daga fari zuwa ja.
"Toh ko dai ya yi haka ne duk saboda ni?" Ta sake raya hakan a ranta. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ji tabbas haka ne, idan ma ba haka ba ne, toh ko ma waɗanne irin takardu ne suna da muhimmanci, duk da ita ba ta ga wani muhimmancinsu ba. Don haka ko ma mene ne za ta yi yadda za ta yi ta ɗakko masa takardun. 'Don dai takarda?' ta furta hakan a kan laɓɓanta. Lokaci guda tana lumshe idanunta. A ranta tana sake jinjina kirki irin na Yohanah. Gefe guda kuma tana tuna yadda daga zarar ta ɗakko masa takardun, nan ba da daɗewa ba za ta ga Tareeq a gaban kotu. Asirinsa ya tonu a idon duniya. Sannan kuma a yanke masa hukunci.
... "Ba kwa jan yarinyar nan a jiki, shi ya sa kullum take zaune ita É—aya. Kada dai shiririta ta mantar da ku alkairinta gare ku." Maama ta faÉ—a tana kallon Hidaya da Sultanah. Tareeq da ke zaune ya kalle su a É—an fuzge kafin ya ci gaba da danna wayarsa. Ita kanta Maama da take zaune ba ta yi tunanin yana da abin da zai ce ba, sai lokacin da ta ji ya buÉ—e baki ya ce
"Kuma ina yawan ba su amanarta ba." Ya faÉ—a ba tare da ya kalle su ba.
"Yah Tareeq Allah kuwa muna kula da ita. Yanzu haka ma barin ta muka yi ta yi bacci." Hidaya ta faÉ—a bayan ta karyar da kanta gefe.
"Ke Sultanah maza je kira mini yarinyar nan." Da "Toh." Sultanah ta amsa tana miƙewa. Kai tsaye ta wuce ɗakinsu. Cigaba da zama suka yi cikin ɗakin, lokaci zuwa lokaci Maama kan jefo wata maganar, shi ko Hidaya wani ya amsa ta. Har zuwa lokacin da Sultanah da Daneen suka shigo ɗakin, Daneen na sanye cikin hijab ɗinta kamar koyaushe. Don ko a cikin gidan ma da aka tashi yi mata siyayyar kaya, har hijabi suka kawo mata da yawa. Ba ta sani ba ko gani suka yi tana son shi ko haka nan ne kawai, ita dai ba ta sani ba. A hankali take takawa cikin ɗakin, kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Abin da ya ƙara wa tafiyar armashi kenan, sai ta zama kamar tana tafiyar ƙasaita ne. Ƙasan kujerar da Maama ke kai ta nema ta zauna, a nutse ta ce
"Barka da rana."
"Barka ka dai, ya jikin naki?" In ji Maama.
"Alhamdulillah." Daneen ta faÉ—a har lokacin a sanyaye. Tun kafin ta iso cikin É—akin ta tabbatar da wanzuwarsa ciki. Sai kuma da ta yo kusa-kusa, sai ta ji duk ya cika É—akin. Sai dai kuma gefe guda, ita kaÉ—ai ta san abin da take ji. Ta kuma saka ranta ba za ta gaishe shi ba. Akan me ye ma za ta gaishe shi? Waye shi É—in? Mutumin da ya yi sanadiyar mutuwar Ameer shi za ta gaisar? Lallai kuwa da ta cika cikakkiyar mara lafiya.
"Toh Alhamdulillahi, Allah Ya ƙara afuwa. Sannu kin ji Daneen?" Maama ta faɗa tana murmushi. Ita ma ɗan murmushin ta ƙaƙalo tana gyara zamanta. Kamar ya ce mata ya jiki, ko kuma dai wani abun, sai kawai ta gintse, duk da ya san da wanzuwarta cikin ɗakin, amma bai nuna ba. Don kuwa ci gaba ya yi da danna wayarsa kamar bai san ta shigo ba. Tun da har ba ta san ta gaida babba ba, bari ya kama kansa, ko ita ma ta saita nata. Dakatawa kuma ya yi da danna wayar, ya ɗan yi shiru sai dai har lokacin idanunsa na kan wayar ne. Amma kuma idan ya yi hakan ya yi daidai? Yarinyar da ta ba shi ƙoda ba tare da wani dalili ba fa? Ya ɗan runtse idanunsa hannunsa a kan goshinsa yana murzawa.
"Na bar muku sashena a buÉ—e, wata a cikin ku ta É—an je ta gyara mini. Zan É—an fita ne." Da mamaki Maama ta kalle shi ta ce
"Unguwa kuma Tareeq? Ina za ka je?" Sai da ya ɗan gyara zamansa sannan ya sanar da ita inda zai je. Ta yi masa addu'ar Allah Ya tsare, ƙannensa na amsawa da Ameen sannan ya fice daga ɗakin. Ta lumshe idanunta tana jin wani irin daɗi na ratsa ta, 'Sashensa a buɗe?' Ta sake tuna hakan cikin zuciyarta tana ji kamar ta tashi ta taka rawa. Ba ita ta bar palourn ba sai da Maama za ta wuce ɗaki ta ɗan yi bacci. Ta yi sallama da Maaman, don dama ɗazun su Hidaya sun fita. Daga haka Maama ta wuce daƙinta, ya yin da Daneen ta wuce nasu ɗakin. Babu ɓata lokaci ta kira Yohana ta sanar da shi abin da ke faruwa. Ya yi shiru yana saurarar ta har ta gama, sannan ya ce yana murmushin da har a cikin muryarsa kana iya ji.
"Da gaske?"
"Ehh.." Ta amsa masa a taƙaice, kamar yadda ya taƙaita tambayar tasa.
"Yanzun nan zai fita? Yawwa toh ki yi amfani da wannan damar wajen shiga sashen nasa, kar ki yi sanya. Na san ba yanzu zai dawo ba. Don haka ki yi abin da na sanar da ke. Sannan kuma tsaya, ki sake tabbatar mini da yanzun zai fita." Ba tare da kawo komai ba ta jinjina kai, kafin ta buÉ—e baki ta ce
"Eh, yanzun nan ya fita."
"Toh shi kenan zan ajje waya. Ki yi duk abin da ya dace ina jiran kiran ki."
.... A fuzge ya kalli wayarsa da ta shiga ringing. Ya É—auke kai yana maida hankalinsa kan driving É—in da yake, Abdoul da ke gefensa ya kalli mai kiran. 'Jawahir' Shi ne abin da ya bayyana a kai.
"Ba za ka É—aga ba ne?" Abdoul ya faÉ—a yana kallonsa. Lumshe manyan idanunsa ya yi kafin ya ci gaba da driving, kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya sanya hannunsa ya É—auki wayar. Bai kai ga É—agawa ba ya ce
"Haka na faÉ—a maka?" Ya faÉ—a bayan ya juya ya jefa masa harara. Murmushi kawai Abdoul ya yi, saboda ganin da ya yi ya kara wayar a kunnensa, alamar ya É—aga. Ajiyar zuciya Jawahir ta sauke kafin ta ce
"Har na cire ran ba za ka É—auka ba wallahi."
"Saboda haka ne halina?" Ya faɗa cikin basarwa, lokaci ɗaya yana sauya hannun da ya riƙe wayar da ɗayan hannun. Duk sai ta dabirce, ba wai don wani abu ba, sai don yadda ya yi magana ya dake ta, har sai da ta ji wani yarr.
"A'ah.. fa.. ba haka.. nake nufi ba." ÆŠa. Jinjina kai kawai ya yi a hankali kafin ya ce
"Toh yanzu dai ya aka yi? Ina driving ne." Ya yi maganar a haÉ—e.
"A'ah babu komai, kira na yi kawai na ji muryarka, sannan na sanar da kai yadda na yi kewar ganin kyakykyawar fuskarka." Ta ƙare maganar tana ɗan sauke numfashi gami da murmushi. Ɗan sauke wayar ya yi daga kunnensa, yana jin waɗannan kalmomin nata sun daɗe da ginsarsa. Ko ba ma haka ba, ya daɗe da daina jin wasu abubuwa da suka shafi soyayya za su birge shi. Sai dai kuma ita burinta kullum ta faɗi yadda take ƙaunar ganin kyakykyawar fuskarsa, abin da ba ya so kenan, amma ta kasa ganewa.
"Toh ya yi, zan samu na shigo." Ya faÉ—a kamar a gajiye. Murmushi ta yi tana faÉ—in
"Yawwah sai ka zo Habiby." Daga haka ya sauke wayar ya ci gaba da driving É—in da yake.