Sashe 22
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.. A wajen su Daneen suka cigaba da zama har lokacin da dare ya yi. Suna ganin yadda mutane ke cigaba da kai komo, har zuwa lokacin da garin ya yi shiru. Sai er hayaniyar da ba a rasa ba. Zuwa lokacin Daneen ta lulluɓe jikinta cikin mayafi saboda wani irin sanyi me shiga jiki da ke ta ratsa ƙasusuwanta. Ameer dai na gefen ta, yana kallan abubuwan da ke wakana a gari, zuwa can dai sai ya juya ya kalli er'uwar tasa kafin ya juya ya cigaba da kalle-kalle.
"Addaneen." Ya faɗa yana kallan ta. Ɗaga lumsassun idanunta da suka buɗe da ƙyar saboda wani irin ciwon kai da ya zo ya mata dirar mikiya lokaci guda ta yi ta kalle shi, ba ta iya amsawa ba sai kallan sa kawai da ta yi.
"Ko ba ki da lafiya ne?" Ya tambaya yana kallan ta sosai. Jinjina kai ta yi, tana sake haÉ—e jikinta waje É—aya ta ce a hankali
"Zazzaɓi nake ji Ameer." Cikin lokaci ƙanƙani fuskarsa ta sauya, ya shiga kallan ta cike da tausayawa
"Sannu Adda kin ji?" Ya faɗa bayan ya gyara zamansa. Jinjina kai ta yi tana ƙaƙalo murmushi ta wanzar a kan fuskarta. Haka suka cigaba da zama a wajen har cikin dare daga ita har shi babu wanda ya runtsa. Ita zazzaɓin ya hana ta baccin, ya yin da shi kuma tausayin er'uwarsa ne ya hana shi yi. Kafin safiya sosai zazzaɓin ya sake rufe Daneen, Ameer ya rasa yadda ze yi. Wajen ƙarfe 8 na safe ne, zuwa lokacin en kasuwa duk sun soma fitowa. Ya kalli Daneen ya ce
"Adda mu bar wajen nan tun da masu wajen sun fara zuwa." Kallan cikin kasuwar ta yi da idanunta da suka ɗan ƙanƙance kafin ta ce
"Toh." Daga haka ta soma ƙoƙarin miƙewa. Sai kuma Ameer ya katse ta da faɗin
"Zauna a nan bari na je na samo miki abinci." Girgiza kai ta yi da sauri tana faÉ—in
"A'ah mu je kawai." Duk da yadda take jin jikinta hakan be hana ta ƙoƙartawa ba, Ameer ya taimaka mata suka bar wajen. Sun yi tafiya me ɗan tsayi babu laifi, suna tafiya suna tsayawa saboda ta huta. Har zuwa lokacin da ta shiga sauke numfashi lokacin da take zaune a wani waje.
"Ameer na gaji." Ta faÉ—a a wahalce.
"Kina jin yunwa?" Ya tambaya don ya san dole za ta ji, dan ko shi ma yana jin ta. Yanzu kam babu musu ta jinjina kai. Ya kalli inda suke, ya sake kallan inda suke kafin ya maida duban sa kanta ya ce
"Ki jira ni a nan komai daÉ—ewar da zan yi zan nemo mana abin da za mu ci kin ji? Kar ki je ko'ina a nan zan zo na same ki." Kallan sa ta yi na tsawon sakanni kafin ta ce
"Ameer ina za ka je?"
"Zan je ko ma ina ne Adda, yunwa kike ji. Zan yi aiki kowanne iri ne don na ga kin samu abin da za ki ci. Ki jira ni kin ji?" Ya sake faÉ—a yana kallan ta.
"Na fi so ko'ina za ka je ina kusa da kai Ameer, ba na son ka tafi wani wajen ni kuma ina nan."
"Adda ba ki da lafiya ai shi ya sa. Ki jira ni kin ji?" Sai ta jinjina kai kafin ta ce
"Allah Ya tsare."
"Ameen." Ya amsa da hakan da murmushi É—auke a kan fuskarsa.
.. A ɗaya ɓangaren kuwa, ya shafe fiye da rabin awa a toilet ɗin, bayan ya sakar wa kansa ruwa mai ɗumi. Duk kuma daɗewar da ya yi tunani ne jibge a cikin ƙwaƙwalwarsa. Zuwa can dai ya ɗauro tattausan towel ya fito ɗakinsa. Be bi ta kan wayarsa da ke ajje kan gado ba, kai tsaye ya ƙarasa gaban mirror ya shiga sake kwantar da sumar kansa da ko da ze kwana nawa ba tare da ya taɓa ta ba ba za ta nuna ba. Sai dai da yake ya riga ya saba, duk lokacin da ya fito daga wanka ya kan gyara ta yadda take sake zama haɗaɗɗiya, mai matuƙar birgewa. Be jima ba ya ida shiryawa cikin wata tattausar jallabiya da ta matuƙar ɗaukar kalar fatarsa. Kasancewar ba zai sake fita daga gidan ba ya sanya shi jan laptop zuwa kan gadonsa, saƙon nan dai ya sake nemowa ya shiga yana sake karanta abin da ke rubuce da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai kamar wanda ke koyar yadda ake karatun. Ya yi nisa ba tare da ya ankara ba sai ji ya yi an turo ƙofar ɗakin. Da sauri ya ɗaga idanunsa ya kalli mai shigowar. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya Maama ta sauke lokacin da ta ga ɗan nata zaune da alama cikin ƙoshin lafiya. Saurin rufe laptop ɗin gabansa ya yi, yana ajje ta gefe ya soma ƙoƙarin sakko wa daga kan gadon. Ƙarasawa Maama ta yi.
"Tareeq ina ka shiga ne tun ɗazu ina kiran wayarka ba ka ɗagawa? Ka san fa ba na son hakan, kana tayar mini da hankali wallahi." Maama ta faɗa tana kallan sa bayan ta nemi waje ta zauna. Sai da ya duba inda ya ajje wayarsa, ya janyo ta ya kunna ta. Tarin missed calls ɗin da ya gani danƙare a kan wayar tasa ya sanya shi ɗaga kai ya kalli Maama.
"Ki yi haƙuri Maama, na ajje wayar ne ban san kin kira ba."
"Wani abin kake yi ne?" Sai da ya É—an kalli laptop É—in kafin ya shafi gefen kansa ya girgiza kai
"A'ah, na ɗan duba wani aiki ne. Ki yi haƙuri Maama." Ya sake faɗa a karo na biyu. Murmushi ta yi kafin ta gyara zama ta ce
"Shi ke nan, za mu iya yin wata magana?" Jinjina kai ya yi kana ya buÉ—e bakinsa ya ce a nutse
"Eh." Sai da ta É—an ja wasu sakanni kafin ta ce
"Ina takardun nan na Diyana?" Shiru ya yi kamar mai tunanin wani abin, kamar ba ze ce komai ba, sai kuma ya É—an fesar da iska daga bakinsa kana ya ce
"Na ƙona su gaba ɗaya." Kallan sa Maama ta cigaba da yi, ya yin da ya basar duk da ya san shi take kalla.
"Toh Allah Ya ƙara kiyayewa. Amm kaa ga gobe idan Allah Ya kai mu Abeeynku zai dawo, Umman Jawahir kuma tana ta cigaba da yi mini maganar haɗa ka da Jawahir. Tun hankalina bai kwanta da hakan ba, har kuma ya zo ya kwanta. Tun da ko babu komai dai Jawahir er'uwarka ce. Don haka nake so na ji daga bakinka, idan dai har ka amince zan sanar wa da Abeeynku wannan maganar sai a san abin yi. Idan kuma ba ka amince ba shi ma ka sanar da ni, amma abin da nake so ka tuna shi ne ni mahaifiyarka na amince da haɗin ɗari bisa ɗari, musabbabin hakan kuma saboda kasancewar Jawahir er'uwarka." Tun da Maama ta soma magana yake kallan ta har ta ƙarasa. Ya yi mamaki matuƙa da ya kasance Maaman da kanta take yi masa zancen wata mace bayan abin da ya faru kwata-kwata ba a daɗe ba. Kamar ta san me yake tunani, sai cewa ta yi
"Kar ka damu Tareeq, na yi hakan ne sanin cewar a kurkusan nan ba lallai ka iya samun nutsuwar fitar da matar aure ba. Shi ya sa na amince da wannan al'amari. Ka yi tunani sosai zuwa gobe sai mu yi magana." Maama ta ƙare maganar tana kamo hannunsa ta riƙe har lokacin tana kallan sa. Ɗan dafe ƙirjinsa da ya yi masa nauyi ya yi, kafin ya janye hannunsa cikin sakannin da ba su wuce uku ba, ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe a kan Maaman, yana tunanin abin da ya kamata ya ce mata. Shin ya amsa da cewar ya amince bayan abin da ya faru tsakaninsa da Diyana? Ko kuwa ya ce be amince ba saboda fidda rai da ya yi a kan mace. Idan ya buɗe baki ya ce ya amince ya kuma kasance ita kanta Jawahir ɗin halin su ɗaya da Diyana fa? Tun da ita ma Diyanan duk daɗewar da suka yi bai taɓa sanin halinta na zahiri ba sai ana dab da ɗaura musu aure.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 15
Cigaba da kallan sa Maama ta yi tana jira ta ji ko ze ce wani abu. A hankali ya zuro ƙafarsa daga kan gadon zuwa ƙasa. Ya miƙe a kan ƙafafun nasa kafin ya ce
"Shi kenan Maama, duk abin da kika yanke wa rayuwata daidai ne. Amma tun da kina son ji daga bakina In Sha Allah zan yi istihara duk yadda ake ciki zan sanar da ke. Babu damuwa za ki iya sanar da Abeey kafin lokacin." Ya ƙare maganar fuskarsa babu yabo babu fallasa. Cikin ransa fata yake ka da Maaman ta sake jan maganar da nisa, don kuwa har ta ginshe shi. Ba don ma Maaman da kanta ke masa maganar nan ba, da ko haɗin kai ba ze bayar ba. Murmushi ne ya wanzu a kan fuskar Maaman, ta miƙe ita ma kafin ta ce
"In Sha Allah. Allah Ya tabbatar mana da abin da ya fi zama alkhairi."
"Ameen." Ya amsa a saman laɓɓansa yana kai hannunsa guda cikin sumar kansa ya shafa. Maama ba ta ƙara mintuna masu yawa cikin ɗakin ba, ta fice ta bar shi tsaye cike da saƙe-saƙe.
.. "Yah Tareeq ka yi haƙuri, ban san wane irin kallo za ka mini ba, ban kuma san wane irin hukunci za ka yi mini ba, idan na sanar da kai cewa na kamu da soyayyar abokinka Abdoul. Ka yi haƙuri Yaya." Hidaya da ta karanta saƙon da Sultanah ta gama rubutawa ta tura.
"Wallahi Hidaya ina tsoron fushin Yah Tareeq." Sultanah ta faÉ—a kamar za ta yi kuka.