← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 49

Sashe 47

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba haka ba ne Maama, hakan ne amma kuma har yanzu ba mu gane ta ba? Ko ma hakan ne ƙoda fa ta ba ni Maama, idan dai har dukiyata take so, ba ma sai ta yi abin da Diyana ta yi ba, wallahi zan iya mallaka mata. Wanda ba na tunanin ma hakan ce a ranta. Idan kuma za ta ƙi ni ne saboda wani abu, ina ganin a yau ɗin nan zan fahimta. Don kuwa idan har kin ba ni dama, toh zan je in same ta ne da maganar a yau ɗin nan. Ina so ranar da su Abeey suka shirya ɗaura aurenmu da Jawahir, a ɗaura a ranar kar a fasa, idan dai kun amince." Ya ja wata ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa cike da gajiya da dogwayen maganar da yake ta yi, wanda za ka iya fahimta ta cikin muryar tasa.

"Ko dai da ma tuntuni kana sonta ne?" Maama ta faÉ—a idanunta a kansa. ÆŠan murmushin gefen baki ya yi kafin ya ce

"Maama, a jiya na yanke shawarar auren ta, da ba a fasa aure na da Jawahir ba ba zan yi wannan tunanin ba. Hakan na nufin akasin abin da kika faɗa kenan?" Ya ƙare maganar kamar mai neman amsa, sai dai ba amsar yake so ba, don haka ya ɗora da faɗin

"Amma dai tabbas na amince zan aure ta, a matsayin mace mafi muhimmanci a rayuwata. Wadda ta sadaukar da wani sashe na jikinta ta ba ni. Sannan kuma ta amince da aure na, duk da yadda 'yar'uwata ta ƙi ni saboda ƙafata."

"Idan ta amince ke nan?" Maama ta yi masa wannan tambayar. Sai ya jinjina kai kawai a nutse. Maama ta gyara zaman ta kana ta ce

"Ba mu san wace ce ita ba, ba mu san zuciyarta ba. Saboda haka sanar da ni, auren naku na tsawon wane lokaci ne? Abin da kake nufi, za ka aure ta ne har zuwa lokacin da za ka warke ko kuwa me kake nufi?" Cike da mamaki yake kallon Maaman, bai taɓa tunanin waɗannan maganganun daga bakinta ba. Sai yake ganin kamar ba Maamansa ba. Anya kuwa ita ɗin ce? Ya tambayi kansa. Sai dai abin da bai sani ba, tsantsar soyayyar ɗanta ce ke nema ta rufe mata idanu.

"Ke nan hakan na nufin in aure ta saboda wata manufa Maama? Idan na yi hakan na yi wa kaina adalci kuwa? Muna tare da Jawahir da Umma tun yarinta, amma ba mu taɓa sanin abin da ke zuciyarsu ba sai yanzun. Kin ga ke nan rashin sanin wace ce Daneen ba komai ba ne. Amma Maama ki faɗi duk abin da kike so na aikata, In Sha Allah ni mai biyayya ne a gare ki." Shiru Maama ta yi na tsawon mintuna ba tare da ta ce komai ba. Bai ma yi tunanin za ta kuma cewa komai ba, sai zuwa can ya ji ta soma faɗin

"Shi ke nan Tareeq, ina addu'a a kan duk abin da ya zama alkairi a gare ka ya dawwamar da shi. Abin da ba shi da alkairi ya nesanta mini kai da shi. Duk da ban ji hakan ya kwanta mini ba, amma kuma kai ya kwanta maka, na kuma san ba za ka zauna haka ba tare da neman zaɓin Allah ba. Don haka na amince ɗari bisa ɗari, Allah Ya tabbatar da abin da ya fi alkairi." Lumshe idanunsa ya yi yana jin nauyin da ke ƙirjinsa ya ɗan ragu, ya kai wajen minti ɗaya a hakan, kafin ya buɗe idanunsa a kan Maama.

"Na gode sosai Maama, Allah Ya saka da alkairi." Ba ta iya amsawa ba, sai murmushi kawai da ta yi a hankali.

... Da mamaki take kallon Hidayar da ta shigo É—akin tana faÉ—in wai Maama na kiran ta. Ta tashi zaune daga kwancen da take, idanunta sun sauya kala kamar wadda ta yi kuka.

"Maama na kiran ki." Hidaya ta sake maimaitawa ganin da ta yi kamar ba ta fahimci abin da take faÉ—a ba. Jinjina kai ta yi tana faÉ—in

"Toh." Daga haka ta miƙe jiki a sanyaye ta bi bayan Hidayan.

"Ɗiyata, ki bi Hidaya, Yayanku na jiran ki za ku yi magana." Shi ne abin da Maama ta ce bayan sun je inda take. Da sauri ta ɗaga kai ta kalli Maama cike da mamaki. A kan laɓɓanta ta furta 'Yayanmu?' Har cikin zuciyarta tana jin wani banbarakwai, kuma da gaske wallahi ba ta gane abin da take nufi ba. Ita ma Hidaya da ba ta san dalilin kiran Maaman ba, ya sanya cike da mamaki ta ce

"Yah Tareeq?" Ta faÉ—a bayan ta buÉ—e manyan idanunta irin na Tareeq.

"Shi." Maama ta faɗa tana jinjina kai. Kiran sunansa da Hidaya ta yi, shi ne ya ƙara mata haske a kan maganar Maaman. Nan take duk wani ragowar annurin fuskarta ya ɗauke ɗiff, take ta ji wani irin bugun zuciya. Toh ke nan me ye dalilinsa na son ganin ta? Wace magana za su yi? Ita kwata-kwata ba ta da buƙatar ganin sa, ballantana kuma har wata magana ta haɗa su.

"Maza Hidaya ki raka ta." Shi ne abin da Maama ta faɗa da ɗan murmushi a kan fuskarta. Kamar wata saƙaguwa, haka ta soma tafiya, zuciyarta cunkushe da tunanunnuka kala-kala. Gaba ɗaya kuma fuskarta a cunkushe. Dab suke da ƙarasowa inda yake, daga nesa tana iya hangen sa daga kan kujerar da yake kai. Ba ka iya ganin komai na jikinsa sai baƙar kwantacciyar sumar kansa, da ke ta sheƙi. 'Babu yadda za a yi ma ka ƙare rayuwarka da ƙafa, mugu kawai. Allah ne Ya fara nuna maka iyakarka, sakayya ka fara gani tun kafin a je ko'ina. Ka kuma jira hukuncin da alƙali zai yanke maka daga zarar na gama abin da ya kawo ni cikin gidan nan' Abin da take raya wa a cikin zuciyarta ke nan, zuciyarta na mata wani irin zafi.

"Yah Tareeq ga ta in ji Maama, bari na koma." Hidaya ta faɗa tana murmushi. Ɗan gajeren murmushi ya maida mata, kana ya jinjina mata hannu, alamar girmamawa. Ta yi dariya kafin ta wuce daga wajen. Ci gaba da tsayawa ta yi a wajen kamar wata saƙaguwa. Ba tare da ta kalle shi ba, don ba ta so ƙoƙarin wanzar da murmushi a kan fuskarta da take ta yi ya gagara. Bayan wajen minti 2, don har ta gaji da tsayuwar, sannan ta jiyo muryarsa a nutse

"Ki zauna mana." Runtse idanunta ta yi tana ji kamar ta buɗe baki ta ce 'Ba zan zauna ba' Sai kuma ta cije, ta daure ta ɗaga ƙafafunta da ƙyar ta nemi waje ta zauna. Ajiyar zuciya Tareeq ya sauke yana tunanin ta inda zai fara. Idan ya ce zai fara ne ta gabatar da kansa kamar hakan ɓata lokaci ne, idan ya ce zai gabatar da kansa a matsayin masoyinta, nan ma tabbas ya yi ƙarya. Hakan ne ya sa bayan shuɗewar wasu mintuna sannan ya ce

"Daneen." Ya kira sunan da wani irin sauti, da duk da ya saba faɗin sunan ba ta jin ya taɓa faɗa da irin wannan sautin. Dalili ke nan da ya sa ta ɗan shiga ruɗani, kada dai ya gano ta? Kada dai ya gano wace ce ita? Kar dai ya gano dalilin zuwan ta gidan? Wannan ruɗewar da ta yi, ita ce dalilin da ya sanya ta ɗaga raunanan idanunta ta kalle shi, sai dai ko sakan 10 ba ta yi ba ta sauke tana jin yadda zuciyarta ke bugawa, so take kawai ta ji ya ambaci abin da ya sa aka kira ta. Sai da ya ɗan yi shiru, yana tunanin ta inda zai fara, don sai yake jin abin wani banbarakwai, kamar yana shirin aikata saɓo. Amma sai ya fesar da iska daga bakinsa kafin ya soma faɗin

"Na san za ki yi mamakin sakawa da na yi aka kira ki. Toh a zahirin gaskiya dai ina ganin babu amfanin kwane-kwane, duk da cewar ke yarinya ce, amma idan aka yi duba da nutsuwarki, hankalinki, hangen nesa da sauransu In Sha Allah hakan ba abin damuwa ne." Ban da bugawa babu abin da zuciyar Daneen ke yi, wannan zagaye-zagayen da yake ta yi babu abin da yake sake jefa zuciyarta sai tsoro. Kamar ya san me take tunani, sai ya ci gaba da faÉ—in

"A taƙaice dai, idan har kin amince na zo da ƙoƙon barar neman auren ki cikin ƙanƙanin lokaci." A razane Daneen ta ɗaga narkakkun idanunta ta zube a kansa, daidai lokacin da shi ma ya ɗaga nasa idanun ya kalle ta. Hakan ya ba wa idanunsu damar sarƙafewa cikin na juna. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka soma sauya kala, duk da yadda idanunta ke cikin nasa, hakan bai sanya ta janyewa ba. Duk kuwa da matuƙar tasiri da kuma kaifin su. Sosai ƙirjinta ke wani irin zafi, zuciyarta na ci gaba da bugawa tamkar za ta faso ƙirjinta. Maimakon ya janye idanunsa sai ya ji yana so ya ci gaba da kallon ƙwayar idanun nata, saboda ya karanci wasu abubuwan daga cikinsu.

"Allah Ya kiyaye ni auren mugu, fasiƙi, wanda ba ya tsoron Allah."

A zahiri abin da ya kamata ta furta ke nan, sai dai bugun da zuciyarta ke yi, ya tabbatar mata ba ta amince da hakan ba. A karan kanta ma sai take ji idan har muggan kalamai suka fito daga bakinta zuwa Tareeq É—in, shi ke nan ta kwafsa komai. Komai ya ruguje musu. Toh amma kuma idan ba ta ce hakan ba, me za ta ce? Za ta buÉ—e baki ne ta ce ta amince da aurensa ko kuwa? Kusan mintuna biyar a haka, kafin ta sauke idanunta bayan sun yi wani irin ja. Shiru Tareeq ya yi na tsawon mintuna yana sake faÉ—aÉ—a tunaninsa a kan irin kallon da ya ga Daneen É—in na yi masa. Sai dai kafin ya ida tunanin, ya tsinto muryarta tana faÉ—in
Chapter 47 · 0% Book details