Sashe 17
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ka sake ni, ka sake ni malam. Ka sake ni." Shi ne abin da Ameer ke ta faɗa yana ciccije wa, yana kuma sake riƙe hannun Daneen da ke cigaba da riƙe na shi. Duk inda Maada ya ja shi sai Daneen ta bi shi, don haka kawai ya saɓe shi gaba ɗaya. Daidai lokacin da hannun Ameer da na Daneen ya rabu, ta buɗe duk wata murya da take da ita ta yi wata ƙara, da tunani tare da fatan wani ya ji ya zo ya taimaka musu.
"Ka sake ni, kar ku cutar mini da Addatah. Kar cutar mini da Addatah, kar ku taɓa mini ita. Ka sake ni." Ameer ya cigaba da faɗa lokacin da yake kafaɗar mutumin, yana dukansa da duk wani ƙarfi da ya san yana da shi. Amma ko bi ta kansa bai yi ba, sai cigaba da tafiya da ya yi da shi.
"Toh ke sai ki haƙura ai mu sarara." Dawa ya faɗa yana kallan Daneen da ke kuka kamar ranta zai fita. Tana kuma ƙoƙarin bin inda su Maada suka yi don fice wa daga wajen, amma Dawa ya ƙi ba ta dama. Ganin da ya yi idan ya cigaba da biye mata za ta ɓata masa lokaci ya sanya shi yin kanta gadan-gadan yana ƙarasa zame tazugen wandonsa gaba ɗaya. Wata ƙarar Daneen ta saki cikin dashashshiyar muryarta. I zuwa lokacin ji take zuciyarta na dab da fito wa daga ƙirjinta.
"Wallahi kika sake yi mini wannan ihun za ki ga yadda zan wulaƙantaki cikin daren nan." Dawa ya faɗa a fusace, don tsoro yake ji kar garin ihun nan nata ta tona musu asiri tun kafin su shana. Kwalar rigarsa da ya ji an kama babu zato babu tsammani, ita ce ta sanya shi dakatawa cike da mamaki. Ya san babu yadda za a yi Maada ya yi masa haka, shi ya sa ya yi mamaki, sai ya ɗaga kai ya kalli wanda ke riƙe da kwalar rigar tasa har lokacin. A cikin idanunsa ya sauke nasa idanun. Cike da mamaki ya gyara tsayuwarsa
"Waye kai?" Ya faɗa cikin ƙarfin hali. Murmushin takaici Tareeq ya yi kafin bai ce komai ba ya ja Dawa ta hanyar jan kwalar rigarsa zuwa waje.
"Malam me ye haka ne?" Ya faɗa cikin muryar nan tasa da ta jiƙu da shaye-shaye. Karo na farko da ya buɗe baki, bayan ya kalli Abdoul da ke tsaye a wajen ya ce
"Ba shi ɗaya ba ne, ina iya jin sautin murya daga baya. Taimaka ka taso ƙeyar kowaye mu miƙa su." Iya abin da ya faɗa kenan, har lokacin bai saki Dawa da ke cigaba da kallan sa ba. Amsa wa Abdoul ya yi yana yin gaba. Daidai lokacin da Dawa ya soma faɗin
"Ka san wani abu Boss? Ka yi haƙuri ka rufa mana asiri kar ka miƙa mu wajen kwalawa. Wallahi tallahi babu abin da na yi wa yarinyar mutane. Dama razanarwa ce kawai ehh ka gane ai. Ban da haka babu wani abu. Ba na son haɗuwa ta da kwalawa ko kaɗan, muna da case da su dama. Ka yi haƙuri ka mini afuwa ka bar ni na je, ba ma za ka sake gani na a arear nan ba." Ya ƙarasa maganar daidai lokacin da Abdoul suka ƙaraso da su Maada da Ameer. A guje Ameer ya ƙarasa ya rungume Daneen, a ruɗe yana faɗin
"Babu abin da ya same ki ko Adda? Babu abin da ya same ki?" Ya faɗa shi kansa jikinsa ko'ina rawa yake. Rungume shi ta yi, ko ta ji sauƙin abin da take ji cikin zuciyarta. Ta shiga jinjina kai har lokacin hawaye ba su dena sintiri a kan fuskarta ba.
"Taso mu tafi Adda, ba za mu sake kwana a wajen nan ba. Taso mu tafi." Ameer ya faɗa bayan ya miƙe, yana riƙo hannunta. Ita ma miƙewar ta yi, tana saka hannunta ta goge gefen fuskarta.
"Ki dena kukan toh kin ji?" Ameer ya faÉ—a cike da kulawa. Jinjina kai ta yi tana jin zuciyarta na sake karye wa. Sai dai ba ta bari hawayen sun zubo ba. Ta saka hannu ta É—auki jakarta, shi ma tasa ya É—auka bayan ya tura kayansa ciki kafin suka fito. Suna tsaye su biyu, Tareeq na daga baya, ya yin da Abdoul ke gaba. Da alama dama inda suke ya nufo. ÆŠaga ido suka yi suka kalle su kafin suka É—auke.
"Ina za ku je?" Abdoul ya tambaya yana kallan su sosai don fahimtar su. Shiru suka yi kamar masu tunani. Kafin Daneen ta gama tsara abin da za ta faÉ—a Ameer ya ce
"Gida."
"Kuna da gida mai ya kawo ku nan?" A wannan karon Tareeq ne ya yi maganar yana kallan su sosai, duk da ba ya iya ganin takamaimai ya fuskarsu take, saboda ƙarancin hasken da aka samu a wajen yanzu ba kamar ɗazu ba.
"Wuce wa muka zo yi. Mun je unguwa shi ne muka yi dare." Ameer ya sake faÉ—a. Cigaba da kallan sa Tareeq kawai ya yi, sai dai bai ce komai ba.
"Ko ma ina ne kuka je ku dena kai wa dare haka, kuna ganin gari ya yi shiru haka, babu kowa. Ga ɓata gari sun yi yawa. Yanzu ga shi kuna gani ba don Allah Ya taƙaita ba, da sai dai Allah Ya tsare. Ku din ga kula, kai wa dare a waje ba na 'ya mace ba ne." Abdoul ya faɗa. Jinjina kai kawai suke yi kamar wasu ƙadangaru, ita dai Daneen ko ɗaga ido ta kasa yi ballantana ta kalle su. Sai a lokacin Tareeq ya gyara tsayuwarsa, ya kalli Abdoul ya ce
"Ka ɗauke su ka kai su gida please, na kira Nuhu yana jira na." Ya ƙare yana kallan Abdoul, kafin a karo na barkatai ya sake kallan Ameer. Sai dai har lokacin bai sake ce masa komai ba, suka yi sallama da Abdoul ya wuce.
"Ku wuce in kai ku gida." Abdoul ya faɗa yana kallan su. Babu musu suka yi gaba, kamar da gasken suna da gida. Har inda motarsa take suka ƙarasa, ya buɗe musu suka shiga, kafin ya tayar da motar. Shiru kawai Daneen da Ameer suka yi jin yadda motar ke tafiya tamkar ba a kan titi ba. Ameer ya kalli gefen su, don sake tabbatar da da gaske a kan titi suke tafiya ba wani wajen ba.
"Mai ya sa ba ka bari mun ce masa ba mu da gida ba, ka sani ko ya samar mana aikin da za mu yi mu samu kuɗin da za mu koma ƙauyenmu." Daneen ta faɗa ƙasa-ƙasa tana kallan Ameer.
"A'ah.."
"Wacce unguwar ce?" Abdoul ya katse wa Ameer maganar da ya fara. Sai kuma idanunsu ya yi tsilli-tsilli, suka kalli juna cikin rashin sanin abin yi.
"A kan titin nan ne ai." Daneen ta yi ƙundunbalar faɗin hakan jikinta a matuƙar sanyaye. Cigaba da driving ɗin ya yi har zuwa lokacin da Daneen ta sake yin ƙarfin halin faɗin
"Ya isa haka, nan ne." Ta faɗa ƙirjinta na wani irin bugawa. Sauka ya yi daga kan titin, kafin ya ce
"Bari na ƙarasar da ku." Ya faɗa yana shiga cikin layin da ta nuna masa. Daga ita har Ameer sai da cikinsu ya ɗuri ruwa. Amma haka suka yi shiru, suka cigaba da rarraba ido kamar shege a rabon gado.
"Ya isa haka, mun gode." Daneen ta faɗa cikin sanyin muryar nan tata da ta sake yin sanyi matuƙa. Jinjina kai ya yi yana tsaida motar, suka sauka bayan sun yi masa godiya sosai.
"Babu komai." Ya faÉ—a yana murmushi.
"Allah Ya saka da alkhairi." Daneen ta sake faɗa a karo na barkatai. A wannan karon murmushi kawai ya yi, ba tare da ya ce komai ba. Ya bi su da kallo lokacin da suka shige wani waje da ke nuni da gidan da suka nufa nan suke ƙoƙarin shiga. Sai a lokacin ya tayar da motarsa ya bar wajen.
Ajiyar zuciya Ameer ya sauke kafin ya ce
"Addaneen."
"Na'am." Ta faÉ—a tana kallan sa.
"Allah Ya taimake mu, amma yanzu ya za mu yi?" Ya tambaya a dame. Kallan inda suke ta yi na tsawon sakanni, kafin ta ce
"Kawai mu zauna a nan zuwa gobe mu nemi aikin da za mu samu kuɗin koma wa gida. Ni ba na son garin nan, kwata-kwata bai yi mini ba. Ba na son shi." Daneen ta ƙarasa maganar tana lumshe kyawawan idanunta. Kallan jar fuskarta da ko'ina na jikinta ya yi jajir Ameer ya yi kana ya ce
"Ni ma haka, ba na so. Ina so mu koma ƙauyenmu kafin Inna ta dawo. Na yi kewar ta, ina so in gan ta." Ba ta san lokacin da murmushi ya ƙwace mata ba. Ta nemi waje ta tsuguna, tana tunanin ta inda za su fara.
Cikin ikon Allah tun da suka zauna a wajen, babu wanda ya fito daga cikin gidan da suke zaune a ƙofarsa, ko kuma wani ya zo wuce wa. Musamman da yake gidan ba a waje yake sosai ba, an yi wasu en dabaru wajen kare shi. Hakan ne ya sa suka zauna a nutse, sai dai fa bacci babu shi babu alamar sa. Suna nan zaune har aka kira sallahr Asuba. Ameer ne ya samo musu famfo suka je suka yi alwala, suka dawo suka yi sallah a wajen, kafin suka cigaba da zama. Lokacin da gari ya ida buɗe wa, sosai Daneen ta shiga buɗe idanunta tana kallan irin gidajen da ke zagaye da su. Gidaje ne waɗanda ba ta taɓa tunanin akwai su a gaske ba. Gidaje ne maka-maka, haɗaɗɗu na gani na faɗa, waɗanda ba ta taɓa ganin irin su ba.
"Kin ga wancan Adda." Ameer ya faÉ—a yana nuna mata wani gidan da shi ma ya gaji da haÉ—u wa.
"Kuma gidan ne fa da gaske koh?" Ta tambayi Ameer a sakarce. Sai da juya ya kalli bayansu kafin ya ce
"Toh mu gwada buga wannan mana sai mu tabbatar." Riƙo hannunsa ta yi da sauri tana girgiza kai
"A'ah babu ruwa na wallahi."