← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 49

Sashe 16

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
Sosai dare ya sake tsalawa har lokacin suna tafiya, wani lokacin idan sun gaji su nemi waje su zauna. Wani lokacin kuma su cigaba tafiya. Sai dai har zuwa lokacin ba su san takamaimai inda za su je ba. Kuɗin da ya rage a hannunsu dududu bai fi na abincin da za su ci ba, ballantana su yi tunanin komawa ƙauyensu, tun da dai wannan gari Allah Ya masa faɗin da sanin inda Innarsu take kamar ba mai yiwuwa ba ne. I zuwa lokacin ban da kukan tsuntsaye, da motsin ƙalilan ɗin ababen hawa babu abin da kake iya ji. Tsoro da fargaba tuni sun cika zuciyoyin Daneen da Ameer. Musamman ma dai Daneen da ke cigaba da raba ido kamar munafuka.

"Adda wai tafiya za mu yi ta yi, ba za mu nemi inda za mu kwana ba." Ameer ya faÉ—a yana dakatawa.

"Toh Ameer a ina za mu kwana? Ni na rasa ma mai zance wallahi."

"Kawai mu nemi wani wajen wallahi, kin ga fa titin babu kowa yanzu. Idan ya so gobe sai mu nemi mafita." Cikin na'am da zancen Ameer ɗin Daneen ta gyara zaman jakarta, suka cigaba da tafiya suna kalle-kalle, ko za su samu inda za su yar da haƙarƙarinsu. Lumshe idanu kawai Daneen ke yi, saboda baccin da ke ta kawo mata hari, dalili kenan da ya sanya manyan idanunta suka ɗan taasa kamar waɗanda suke ciwo.

"Bacci kike ji ko Adda?" Ameer ya faÉ—a cike da kulawa. Jinjina kai ta yi tana kai hannunta saitin bakinta lokacin da ta yi hamma. Ta É—an runtse idanunta tana sake buÉ—e su, daidai lokacin da ta jiyo muryar Ameer na faÉ—in

"Laa Adda kin ga wani waje can wallahi ki zo mu je. Za mu iya kwana abin mu." Ya faɗa yana jin yadda farin ciki ke mamaye ilahirin jikinsa. Inda yake nuna wa ta bi da kallo. Trader ce irin ta mai shayi. Wadda da alama mai ita ba ya zama, ko kuma wani dalili ya hana shi zama yau ɗin. Saboda yadda masu shayi kan kai wa dare, bai ci a ce har ya tashi i yanzu ba. Juya wa Daneen ta yi ta kalli titin da motoci ke cigaba da wuce wa. Kafin ta dawo da dubanta kan trader. Kawai sai ta ji jikinta ya sake yin sanyi. Tabbas da ta san ba za su haɗu da Innarsu ba, ba za ta taɓa yarda su fito daga gida ba ko me Dada za ta musu. Ba ta taɓa tunanin akwai gari mai girman da za a ce kowacce unguwa akwai nasu mai unguwar ba sai yanzu. Ba ta taɓa tunanin ƙaddarar rayuwa kan iya jefo su har suna shirin kwana a kan titi ba. Shin me ya sa ta biye wa Ameer suka fito daga ƙauyensu zuwa wannan garin mai girman da da alama ya ninka ƙauyensu sau babu adadi. Shin me ya sa suka yi wannan gangancin na biyo Innarsu ba tare da sun san takamaimai inda take ba.

"Ki zo mu ƙarasa." Ameer ya faɗa yana jan hannun Daneen, ganin da ya yi da alama ta yi nisa a tunanin da ta tafi. Babu musu ta bi bayansa. Shi ya fara yin gaba, ya yin da ta bi bayansa. Har ciki suka shiga kasancewar babu ƙofa. Sai dai wajen irin keɓantaccen nan ne. Don haka ko da suna ciki babu wanda zai iya ganin su. Karɓar jakar hannunta Ameer ya yi, ya ajje ta gefe, ya sanya hannunsa ya ɗakko rigunansa guda biyu ya shimfiɗa, kana ya kalli Daneen ya ce

"Adda taho ki kwanta." Ya yi maganar lokacin da yake gyara zaman jakarta don ta ji daɗin yin pillow da ita. Kallan Ameer ɗin Daneen ta yi, ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. Ƙaunar Ameer a gare ta yawa gare ta, haka zalika ƙaunar ta gare shi tana da yawa. Don ji take tamkar ta fi ƙaunarsa ma a kan yadda take ƙaunar kanta.

"Kai fa?" Ta tambaya tana kallan sa.

"Ki fara kwanciya, ni ma zan kwanta." Ƙarasawa ta yi ta kwanta, zuciyarta cike fall da tunane-tunane. Sai dai abin da ya fi tsaya mata a rai, shi ne yadda za su samu kuɗin motar da za ta maida su ƙauyensu. Sai a lokacin sannan Ameer ya nemi waje shi ma ya yi shimfiɗa ya kwanta.

Sosai dare ya cigaba da tafiya, gari na sake yin shiru, ƙarar kukan tsuntsaye na daɗuwa. Sautin ababen hawa na raguwa. Har zuwa lokacin da motsin su ya ɗauke kwata-kwata.

"Baba yau fa so nake na afa aji garau ɗin nan da yawa, don wallahi so nake na haura hazo na yi ta shawagi ni ɗaya." Sautin da ke fita a daddaƙire, cikin irin muryar en shaye-shaye ta doki dodon kunnen Daneen da baccin nata kwata-kwata bai yi nisa ba.

"Kar ka damu. Ni kaina yau ɗin nan so nake na yi mugun cajin da na daɗe ban yi ba." Wanda suke tare ya faɗa. Lokacin da suke ƙara kusantar trader. Kai tsaye can suka nufa, suka nemi waje suka zauna. Cikin ƙanƙanin lokaci suka baje kayan harkarsu. A hankali Daneen ta tashi zaune, tana jin yadda zuciyarta ke buga wa tamkar za ta faso ƙirjinta. Ta lalubi fuskar Ameer ta taɓa, ta ji bacci yake. Sai ta ɗauke hannun nata tana koma wa ta zauna a kan shimfiɗarta, bugun zuciyarta har wani sauti yake bayar wa 'dif, dif, dif' saboda tsananin tsoron da take ji.

"Kai.. Ni fa kamar motsi nake ji a cikin abar nan." ÆŠaya daga cikin su ya faÉ—a yana É—an waigawa. BuÉ—e idanunta Daneen ta yi jin abin da ya faÉ—a, daidai lokacin da wasu hawaye suka samu damar zubo wa a kan kuncinta lokaci guda.

"Kai ni ma fa kamar na ji. Waye a nan?" Ya faɗa a ɗan tsawace yana kallan cikin trader. Runtse idanunta Daneen ta yi tana karanto duk wata addu'a da ta zo ranta, lokaci ɗaya tana haɗe jikinta waje ɗaya, kanta ɗore a kan cinyarta, zuciyarta na wani irin harbawa, tsoron da tun da uwarta ta haife ta ba ta taɓa jin sa ba na cigaba shigar ta.

"Ya kamata mu duba fa." Ɗayan ya faɗa yana miƙe wa. Shi ma miƙe wa ɗayan ya yi suka shiga takawa zuwa inda su Daneen suke. I zuwa lokacin zuciyar Daneen bugawa ne kaɗai ya rage ba ta yi ba. Kawai sai ta cigaba da addu'a tana miƙa wa Allah lamarinta kawai. Don ba ta san kuma abin da ya kamata ta yi ba bayan wannan.

"Kai! Wallahi kamar mace nake hange a ciki fa. Kar dai a ce yau rabon farka wata yarinya ne ya fito da mu." Wanda da alama ya fi ɗayan tantiranci ya faɗa yana dariya, lokaci ɗaya yana kallan Daneen, hannunsa a kan haɓarsa yana shafawa.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 11

"Ke don tantiranci ma kawo kanki kika yi? Lallai abin zai bayar da citta." Ya ƙare lokacin da ya ida ƙarasa tura kansa cikin wajen da su Daneen suke. Har kuma lokacin shu'uman idanunsa na kanta, yana bin ta da wani kallo kamar tsohon maye. Cikin saurin da ba ta san tana da shi ba, ta miƙe daidai lokacin da ta ida buɗe kumburarrun idanunta a kansa.

"Me ye haka kuma? Ina kike ƙoƙarin zuwa? Maada ƙaraso da gulafarka ciki mana." Shi dai wanda ya soma magana tun farko ya sake faɗa. Kamar cikin mafarki Ameer ya soma jiyo maganganu ƙasa-ƙasa. Babu shiri ya buɗe idanunsa da ke ɗauke da bacci. A kan Daneen ya sauke su lokacin da take zube a kan ƙafafunta, kyawawan idanunta sharkaf hawaye. Tun da Inna-wuro ta haife ta, ba ta taɓa tsintar kanta cikin tashin hankali irin wannan ba.

"Don girman Allah kar ku yi mana komai, ku bar mu mu tafi don Allah. Wallahi ba za mu sake zuwa wajen nan ba, don Allah." Ta ƙare hannayenta biyu a haɗe waje guda. Dariya Maada ya sheƙe da ita, yana kallan Dawa kafin ya ce

"Kaa ji me take cewa fa." Ya faɗa yana nuna Daneen da yatsan hannunsa. A tare suka sheƙe da wata sabuwar dariyar suna kallon Daneen da har lokacin take zaune a kan gwuiwoyinta.

"Bari ka gani." Dawa ya faÉ—a yana soma sassauta É—aurin tazugen wandon da ke jikinsa.

"Adda." Ameer ya faɗa yana miƙe wa lokacin da ya gama fahimtar maza har biyu sun shigo cikin trader yana bacci. Ga kuma abubuwan da ya ji suna faɗa. Abin da ya tayar masa da hankali kenan, ya kamo hannun Daneen ya riƙe gam cikin nasa, kafin ya maida dubansa kan su ya ce

"Don Allah ku yi haƙuri." Da mamaki Dawa ya ɗaga ido ya kalli Ameer, don kwata-kwata bai lura da wanzuwarsa cikin wajen ba sai da ya yi magana.

"Maada yi mini waje da wannan wawan, kai ma ka ɗan ba mu waje, idan na gama sai ka shigo ka ɗora." Tun kafin ya ida maganar, Maada ya ƙarasa ya cafki hannun Ameer da niyyar fidda shi daga cikin trader. Ganin da Ameer ya yi da gaske so suke su fitar shi, ya bar su kenan tare da Addarsa? Hakan ne ya sanya shi sake riƙe hannun Daneen gam-gam cikin nasa, ita ma hakan ce ta faru. Duk da yadda ilahirin jikinta ke ɓari, sai ka ce wadda zazzaɓi ke shirin rufe wa, ko kuma ya rufe ɗin ma. Gaba ɗaya ta rikirkice, ta ruɗe, ta rasa abin da ya kamata ta yi. Sai dai har lokacin ba ta dena ambatar sunan Allah cikin ranta ba. Ganin da Maada ya yi Ameer zai ɓata masa lokaci ne ya sanya shi saka hannunsa gaba ɗaya ya soma ƙoƙarin saɓa shi a kafaɗa.
Chapter 16 · 0% Book details