← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 49

Sashe 3

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki tashi ana miki magana, kin zauna kin kafe mutane da idanu kamar za ki cinye mu. Kin tashi ne ko sai na tashi na kai ki da kaina." Dada ta faɗa a zafafe. Miƙewa ta yi a hankali tana jin yadda jiri ke ɗibar ta. Ba ta damu da hakan ba sai shiga ɗaki da ta yi, ta saɓa Daneen da har lokacin take bacci a baya. Ta ɗauki dogon hijabi ta saka. Abubuwan da ta san dole tana da buƙatar su ta tsaya ta ɗauka a gurguje sannan ta fito. Gaba ɗaya jikinta ya yi wani mugun sanyi haka ta fito, kamar ba za ta ce komai ba sai kuma ta lumshe idanunta ta ce

"Na tafi." Daga haka ba ta jira sun ce komai ba ta fice daga gidan. A cikin motar ta hango shi ya yi ƙwam a driver seat. Ƙarasawa ta yi ta ƙarasa buɗe murfin gaban motar da ya soma buɗe mata, ta shiga ta zauna. Kamar yadda be ce komai ba haka ita ma ba ta ce komai ba, ya tashi motar suka bar wajen. Sun yi nisa da fara tafiya ya kalle ta, ya saki murmushi kafin ya maida kansa kan titi kana ya ce

"Kin ƙara kyau abin ki 'yar fara tass tawa." A hankali ta ɗaga idanunta ta kalle shi, ta lumshe su tana jinjina kai, ta buɗe baki a sanyaye ta ce

"Na gode." Bai sake cewa komai ba har zuwa lokacin da suka ƙarasa ficewa daga rugar gaba ɗaya, suka miƙi hanya cikin gari. Ga mamakinta maimakon ta ga sun yi gida, sai ta ga ya yi parking motarsa cikin wani private hospital, ta juya ta kalle shi cikin son jin ƙarin bayani. Be kula ta ba sai fita daga motar da ya yi ya ce yana kallan ta.

"Fito." Ya yi maganar cikin bayar da umarni. Sake kallan cikin asibitin ta yi, ita dai ba za ta ce ga takamaimai abin da ya kawo su ba, tun da ya zo gidan kuma bai tambayi lafiyar É—iyarsa ba, ballantana ta ce ko ya kawo su ne domin a duba lafiyarta.

"Ki fito mana, a'ah.." Ya sake faɗa. Hannu ta saka ta buɗe motar ta fito, tana cigaba da kallan cikin asibitin. Be ce da ita komai ba sai gaba da ya yi, babu ɓata lokaci ta bi bayansa. Kai tsaye ɗakin likitan suka shiga, bayan doguwar gaisawar da suka yi da Alhaji Baita, wanda hakan ke nuna sabon da ke tsakaninsu.

"Matata ce wannan, kamar yadda aka saba nake so a yi mata. Idan da akwai maganin da za a ba ta kwata-kwata ta dena haihuwa a ba ta don Allah." Cikin wata irin ruɗewa Inna-wuro ta kalli Alhaji Baita, zuciyarta na wani irin bugu da ya wuce na ƙa'ida. Girgiza kanta ta soma yi tana jin yadda tarin ƙwalla ta cika idanunta. Ilahirin jikinta na rawa kamar mazari, cikin karyayyiyar muryarta da ke rawa saboda tsabagen ruɗewa ta ce

"A'ah don Allah kar ka mini haka, kar ka cuci rayuwata, kar ka zama sanadin katsewar farin cikina, ina son na haihu, ina son ganin 'ya'yana ko da guda nawa Allah zai ba ni ina son su. Don girman Allah kar ka yi mini haka." Ta ƙare lokacin da wasu kyawawan hawaye suka sauka a kan fuskarta.

"Ni kuma ba na so, ba na so kwata-kwata. Ke kan ki kuma kin san ba don ki haihu na aure ki ba. Kar kuma ki yi tunanin don kin ce in ƙyale ki hakan na nufin zan ƙyale ki ko na datse alaƙar da ke tsakaninmu. A'ah zama da ni yanzu kika fara, domin iyayenki sun riga sun ba ni ke halak malak, don haka dole ki zaɓi mafita ɗaya. Ko dai ki zaɓi a cire mahaifar gaba ɗaya, ko kuma ki yi planning na shekaru, wanda za ki din ga sake wa daga zarar lokacin lalacewarsa ya yi." Alhaji Baita ya faɗa yana kallon cikin idanun Inna-wuro. Shiru doctor ya yi yana saurarar duk abin da ke gudana. Lallai Alhaji Baita shege ne, kuɗi kuma kan su shegu ne, tun da ga shi mata kala-kala na yarda su zauna ƙarƙashin Alhaji Baitan duk da yadda yake yadda ya ga dama da su. Kanta ta ji yana wani irin juya mata, tana tsoro kar ta je ta amince da abin da ya faɗa a yi mata abin da ya buƙata tun da farko. Idanunta da ke a rufe ta buɗe a kan fuskar Alhaji Baitan. Ta riga ta san ba ta da wani 'yanci na neman saki a wajen Alhaji Baitan, tun da iyayenta suka riga suka mallaka masa ita, duk da ba ta son sa, kuɗin da ya din ga musu ɓarinsa ne ya sa suka ba shi ita. Ta buɗe bakinta da ya yi mata nauyi da ƙyar ta furta

"Na amince."

"Likita na shekara biyar nake so, kar a yi na ƙasa da haka. Shekarun na cika kuma za mu dawo" Alhaji Baita ya faɗa yana kallan Likitan. Hannunsa da ya haɗe waje ɗaya ya raba su kafin ya ce

"Kar ka damu Yallaɓai. Ka bar komai a hannuna, ba za ka yi dana sani ba."

"Godiya nake Doctor." Alhaji Baita ya faÉ—a yana murmushi.

.. Har dare ya yi bai nemi ya ga ɗiyar da aka haifa masa ba. Tana zaune cikin ɗakin ta fito daga wanka ya shigo ɗakin, ƙarasowa ya yi yana kallanta lokacin da take ɗaure da towel. Ya lumshe idanunsa kafin ya ce

"Ki ɗauki yarinyar ki miƙa ta sashen 'yan aiki su kula da ita zuwa safiya. Sai ki taho sashena ina jiran ki." Da matuƙar mamaki ta ɗaga kai ta kalle shi, bakinta har rawa yake lokacin da ta furta

"Watanta biyu ne fa..?"

"Ko yau kika haife ta.." Ya ba ta amsar cikin rashin kulawa. Kafin ta kai ga cewa komai ya ce

"Ina buƙatar ki, ki same ni a ɗakina. Ba na son ɓata lokaci." Daga haka ya juya yana shirin ficewa, jin ba ta ce komai ba ya sanya shi dakatawa, ya juya ya kalle ta kafin ya ce

"Kin ji koh?" Jinjina kai ta yi kafin ta lumshe Idanunta daidai lokacin da ya fice daga ɗakin. Ta kai wajen minti 10 a cikin ɗakin tana tunanin abin da ya kamata, kafin ta share hawayen fuskarta ta ja Daneen a jikinta ta rungume, kusan mintuna 2 kafin ta sauke ta, ta shayar da ita na tsawon mintuna masu yawa kana ta miƙe ta fice daga ɗakin. Kai tsaye sashen 'yan aikin ta nufa, zuciyarta cunkushe da tunane-tunane kala-kala. Shin idan ta yi hakan ta yi wa yarinyarta adalci kuwa? Da wannan tunanin haka ta ƙarasa, ta samu Atika da ta yarda da ita sosai ta miƙa mata yarinyar.

"Ki kula mini da ita don Allah. Idan ta farka ki ba ta ruwa ta sha In Sha Allah za ta koma bacci. Zuwa safiya zan zo na karɓe ta." Yadda take maganar a hankali kamar wadda ke shirin yin kuka ya sanya Atika faɗin

"Rankiyadaɗe lafiya kuwa?" Ta tambaya tana karɓar fidar da Inna-wuron ta miƙa mata. Murmushin yaƙe ta yi kafin tace

"Lafiya ƙalau. Ki kula mini da yarinya."

"In Sha Allah Hajjaju kar ki damu." Ba ta iya sake cewa komai ba ta fice daga sashen gaba ɗaya. Kai tsaye sashen Alhaji Baita ta nufa, gaba ɗaya zuciyarta a cunkushe, jikinta kuma a matuƙar sanyaye. Tana shigowa ya miƙe ya rungumo ta fuskarsa ɗauke da murmushin da rabon da ta ta gan shi a kan fuskarsa tun bayan da ya fahimci tana da cikin Daneen. Ƙarasawa ya yi da ita a jikinsa zuwa kan gadon. Kamar koyaushe cikin ƙanƙanin lokaci ya shiga fiddo da zilamarsa a kanta a fili. Duk wata kewar jikinta da ya yi na tsayin kwanaki sai da ya fanshe a daren.

"Shi ya sa kullum nake ƙara jin son ki a cikin zuciyata Fatima." Ya ƙare maganar yana shafa doguwar baƙar sumar kanta da ke kwance kamar wadda ke saka wa relaxer. Wasu hawaye masu ɗumi ne suka samu damar sakkowa zuwa kan fuskarta, waɗannan kalaman da ya faɗa babu abin da suka haifar mata sai raunin zuciya da sake kashe mata jiki. Shin kowacce mace haka take fuskanta a gidan aurenta? Shin da ma aure ana yin shi don wannan abun ne ko kuwa dai ita nata kalar auren ne daban da na mutane? Ba ta taɓa samun farin ciki, ba ta ganin murmushinsa idan ba a kan wani abu da ya shafi jikinta ba.

... Sam ta kasa zaune, ta kasa tsaye. Daga ta je can sai ta dawo nan. Ban da bugawa babu abin da zuciyarta ke yi. Kanta gaba ɗaya ya kulle, tsoro da fargaba take ji matuƙa. Idan dai har ba kuskure ta yi ba, tun da ta dawo daga gida haihuwar Daneen ba ta sake ganin baƙon watanta ba. Duk kuma wasu alamomi da ta ji farkon cikin Daneen shi take ji a yanzu. 'Kar dai abin da take tunani shi ne?' Ta tambayi kanta tana jin sabuwar faɗuwar gaba na ziyartar ta. A hankali ta kai idanunta kan Daneen da ke kwance kan gado tana ta wasa, don yanzu ta sake wayo sosai, ta yi ɓul-ɓul abin ta. Tausayinta ya kama ta, kawai sai ta ji ƙwalla ta taru a idanunta. Daidai lokacin da Alhaji Baita ya shigo ɗakin. Ta yi saurin ɗauke ƙwallar tana juyawa da sauri ta kalle shi.

"Me kike yi ne har yanzu ina jiran ki ba ki ƙaraso ba? Ko kin manta yau kwanan ki ne?" Ya tambaya ba tare da ya damu da yanayin da ya gan ta ba. Girgiza kai ta yi kafin ta ce

"A'ah, Daneen ke kuka na tsaya rarrashin ta." Ta yi maganar idanunta a kan Daneen.
Chapter 3 · 0% Book details