Sashe 23
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ke ki dena jin tsoro, ina tare da ke fa." Hidaya ta faɗa tana riƙo hannun Sultanah, duk da ita kanta tana jin tsoron, amma don ta ba wa 'yar'uwarta ƙwarin gwuiwa ya sa ba ta nuna ba. Ganin alamar blue tick da suka yi ne ya sanya kusan a tare suka gyara zama. Sultanah ta haɗiye wani yawu da ƙyar tana jin yadda bugun zuciyarta ke ƙaruwa. Ba ta san yadda za ta yi da zuciyarta ba, ba ta san lokacin da ta faɗa ƙaunar Abdoul ba. Farga kawai ta yi dumu-dumu cikin wata matsananiyar ƙaunarsa irin mara adadi ɗin nan. Tun tana ganin za ta iya jurewa har ta kasa, don kuwa yanzu haka ita kaɗai ta san irin zafin da zuciyarta take yi, na rashin isar da saƙon zuciyarta gare shi, har zuwa wannan lokacin. Ta san halin yayansu, shi ɗin mai damuwa da damuwarsu ne, sai dai ba ta sani ba, ko a wannan karon ma ze bi bayanta ne bayan ta sanar da shi tana ƙaunar abokinsa. Ba ta sani ba ko ma hukunci ne ze biyo baya.
"Har yanzu fa be yi reply ba Hidaya." Sultanah ta faɗa ganin da ta yi bayan wajen minti 5 da ganin saƙon da Tareeq ya yi amma har yanzun be yi reply ba.
"Ze yi ne Sulty, mu ƙara lokaci." Hidaya ta faɗa a sanyaye, saboda yadda ta ji gaba ɗaya ɗan ƙwarin gwuiwar da ta yi nasarar haɗa shi yana ƙoƙarin zagwanyewa.
A ɓangaren Tareeq kuwa ya karanta saƙon nan ya fi sau uku. Daga ƙarshe dai sai ya sake dubawa don tabbatarwa da gasken Sultanah ɗin ce ta turo masa saƙon. 'Tabbas ita ce' Ya tabbatar wa da kansa hakan yana sake kallan saƙon. Shiru ya yi na tsawon lokaci, tabbas abin ya matuƙar ba shi mamaki, ya kuma ɗaure masa kai. Be taɓa tunanin ƙanwar tasa za ta iya yin hakan ba, har kuma ta sanar da shi. Sai dai kuma da ya nutsa tunaninsa sai ya ga abin da Sultanah ta yi kamar shi ne daidai. A matsayinsa na yayanta mai ƙoƙarin samar mata mafita a kowanne yanayi ne, shi ya kamata ta sanar wa da abin da ke faruwa. Abu na biyu kuma shi ɗin aminin Abdoul ne, wanda ze iya amfani da kasancewar hakan wajen samar wa 'yar'uwarsa mafita. Sauka ya yi daga Whatsapp ɗin kai tsaye ya nemo number Abdoul ya kira. Ringing 1_2 ya ɗauka, kafin Tareeq ɗin ya ce komai Abdoul ya ce
"Barka Aboki."
"Yawwah, kana lafiya?" Tareeq ya faÉ—a hannunsa na kan goshinsa yana É—an murzawa.
"Alhamdulillahi. Ya ake ciki?" In ji Abdoul.
"Kana gida ne?"
"A'ah, yanzu na ɗan fita ne karɓo saƙo." Sai da Tareeq ya ɗan gyara zaman sa sannan ya ce
"Ohk, gobe za ku shigo ai?" Murmushi Abdoul ya yi kana ya ce
"Eh mana, da wuri ma kuwa In Sha Allah."
"Allah Ya nuna mana, akwai wata muhimmiyar magana da nake so mu yi da kai."
"Ikon Allah! Wacce magana ce wannan?" Abdoul ya faɗa cike da mamaki. Ɗan murmushi ne ya wanzu a kan laɓɓan Tareeq kafin ya ce
"Kai dai za mu haÉ—u."
"Malam ka sanar da ni kawai please."
"Sai kuma ka yi ai." Tareeq ya faÉ—a cikin basarwa.
"Kai fa dama ɗan rainin hankali ne wallahi.." Abdoul ya dakata daga haka, kafin ya yi ƙwafa kana ya ɗora da faɗin
"Amma ya na iya.. Allah Ya kai mu." Murmushi mai sauti Tareeq ya yi kana ya amsa da "Ameen." a nutse. Daga haka suka yi sallama.
**
Washe gari sosai gidan ya tashi da karɓar 'yan'uwa na kusa. Waɗanda ke ta shirye-shiryen dawowar Alhaji Alhassan Dikko. Jawahir da ba su kwana a gidan ba, da sassafe suka diro gidan don tarbar Abeeyn. Tun safe duk suna sashen Dada ji, Maama, Hidaya, Sultanah, Jawahir da Mamanta. Maamin Sultanah ce kaɗai tun wayewar garin kwata-kwata ba ta shigo ba. Duk kuwa da cewa ayyukan da ake gabatarwa sun fi yawa a sashen Dada ji ɗin kamar yadda aka saba. Duk kuma da cewa ta san duk en gidan suna sashen nata, hakan be sanya ta zuwa ba. Tana can sashenta tana shirya wa mijinta abubuwa na musamman. Babu kuma daɗewa ƙawarta, aminiyarta Hajiya Zulaiha ta iso gidan. Mata ga Aminin Abeey, kuma mahaifiya ga Abdoul Aminin Tareeq. Su biyu suka iso gidan, Abdoul ya wuce sashen Tareeq, ya yin da Umma ta wuce kai tsaye sashen Maami.
Da sallama ya shiga palourn, idanunsa a kan Tareeq da ya kwantar da kansa a kan kujera idanunsa a lumshe. Ya ɗora hannunsa ɗaya a kan fuskarsa, wanda hakan ya yi nasarar kare idonsa guda ɗaya. Sai da Abdoul ya ƙarasa ya zauna a gefen sa ya ce cike da mamaki
"Tareeq." Da sauri Tareeq ya buɗe idanunsa, don kwata-kwata be ji shigowar Abdoul ba. Idanunsa da suka ɗan janye saboda daɗewar da suka yi a lumshe ya sauke a kan Abdoul. Ya ja wani nannauyan numfashi da ya fito daga ƙirjinsa a takure kafin ya ce
"Yaushe ka shigo?"
"Bayan ka yi nisa a tunanin." Tareeq ya faÉ—a yana karantar yanayinsa. Iska kaÉ—an Tareeq ya fesar daga bakinsa kafin ya gyara zamansa, ba tare da ya ce komai ba, har lokacin da Tareeq ya ce
"Anya kuwa lafiya Aboki?" Ya faÉ—a yana sake karantar yanayinsa. Cikin basarwa Tareeq ya ce
"Lafiya mana, wani abu?" Ya ƙare har lokacin dai cikin basarwa.
"Ko dai har yanzu maganar Diyana ne?" Be san lokacin da tsaki ya suɓuce masa ba.
"Me kake so na ce maka ka yadda na daÉ—e da cire Diyana a babin rayuwata? Allah É—aya ne koh? Toh ina rantse maka da shi, ko kaÉ—an babu damuwar Diyana a tattare da ni. Ina ga zuwa yanzu ya kamata ka amince da ni." Numfashi Abdoul ya sauke kana ya ce
"Shi kenan, amma tabbas idan babu wannan akwai wani abu da kake ɓoye mini." Da sauri Tareeq ya girgiza kai. Ba tare da ya kalli Abdoul ba ya ce
"Kar ka damu kanka, babu wani abu."
"Amm.." Abdoul ya buÉ—e baki ya fara magana Tareeq ya yi saurin katse shi da faÉ—in
"Maganarmu.." Girgiza kai Abdoul ya yi, jin yadda ya basar da zancen. A ransa yana saƙa tabbas ko ma mene ne, idan ta yi tsami ze ji. Idan dai har abin da ya kamata ya sani ne, toh ya san Tareeq ɗin ze sanar da shi ko ba yanzu ba. Hakan ne ya sanya shi faɗin
"Ina jin ka." Gyara zama Tareeq ya yi, sai dai kafin ya ce komai wayarsa ta soma ƙara. Ya janyo ta yana kallan mai kiran nasa.
"Yaya wai ka fito muna palourn Dada ji." Hidaya ta faÉ—a, bayan Tareeq ya amsa wayar.
"Ohk." Ya amsa da hakan, yana mayar da kallan sa kan Abdoul ya ce
"Tashi mu je, Abeey na dab da iso wa." Ya faɗa yana miƙewa. Be jira Abdoul ya ce komai ba ya shige bedroom ɗinsa. Bayan shuɗewar wasu mintuna ya fito, suka fice daga sashen gaba ɗaya.
... A ɓangaren Daneen kuwa, da mayafin da ke jikinta ta yi amfani wajen nannaɗe fiye da rabin jikinta. Ta kifa kanta a kan gwuiwarta tana lumshe idanunta. Kewar mahaifiyarta take matuƙa gaya, kewarta ce ke ratsa duk wata gaɓa ta jikinta. Yanzu ko tana ina?Tana can tana tunanin suna zaune a ƙauyensu suna jiran ta? Tana can ita ma duk inda take hankalinta yana kansu, kamar yadda nasu hankalin ke kanta? A nutse ta sake lumshe idanunta tana jin yadda wani bacci ke ƙoƙarin fizgarta. Haka ta yakice shi, don duk wani hankalinta yana kan Ameer. Ta kwashe fiye da awa ɗaya tana ta saka ran jin muryar Ameer ya yi mata magana, amma shiru. Tun tana cigaba da kwanciya har ta gaji ta tashi zaune, ta shiga rarraba manyan idanunta da suka ɗan faɗa, cikin rashin sanin abin yi. Wasa wasa, har bayan wajen awa uku, babu Ameer babu alamarsa. Har ba ta san lokacin da ta miƙe a kan ƙafafunta ba, duk da jikinta da babu ƙwari hakan be dame ta ba, burin ta kawai ta san yadda za ta yi ta je ta nemo inda Ameer ya yi, ya bar ta a nan tana ta jiransa. Har ta soma takawa don barin wajen, kamar wadda aka tsikara kuma sai ta dakata. Ta sake kallan inda take tsaye, sai ta mayar da ƙafarta baya. Gaba ɗaya tunaninta ya tafi kan Ameer, idan kuma har ta bar wajen nan, kai tsaye ba ta san inda za ta nufa ba. Bayan kuma ya faɗa ya sake jaddada mata da kar ta je ko'ina komai daɗewar da ze yi ta jira shi. Idan ta bar wajen kuma shi ya dawo be gan ta ba fa? Daga nan me zai faru? Cikin sauri ta shiga girgiza kanta kamar wadda ke magana da wani. Cikin matuƙar sanyin jiki ta koma da baya ta zauna inda ta tashi. Tana nan zaune har ta ji an soma kiraye-kirayen Sallahr Azahar, amma babu Ameer babu dalilinsa. Gaba ɗaya wani tunaninta ya tafi kan inda ya tsaya. Haka zalika tambayar da ke ta mata yawo a cikin kwanya ita ce 'Ina ya tsaya? Me ya sa har yanzu bai dawo ba?' Cikin sakannin da ba su wuce biyu ba, ta ji bugun zuciyarta ya ƙaru, nan take jikinta ya ɗauki rawa, fararen idanunta tuni suka soma sauya kala, cikin sakanni ƙalilan, hawaye suka taru. Kawai sai ta shiga juye-juye, cikin rashin sanin abin yi, sai ka ce wadda aka cewa idan ta juya ɗin za ta hango shi. Duk kuma lokacin da ta kalli mutanen da ke kaikawo a wajen, sai ta ga kamar za ta hango Ameer ɗin a cikinsu, babu kuma abin da take ji, sai ƙarin faɗuwar gaba, da bugun zuciya.
A yi manage da wannan, In Sha Allah gobe ma za ku samu Update.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 16