Sashe 45
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗaga idanunta Umma ta yi ta kalli Dada ji. Karo na farko da ta fara kallon Dada ji ɗin ba a matsayin mahaifiyarta ba, bayan tsawon shekaru masu yawa. Ba za ta iya bari a ce tana ji tana gani, duk yadda ta ci buri da 'yarta a ce ta ƙare a auren nakashashshshe, musaki, mara ƙafa ba. Wanda ko likitoci ba su da tabbacin zai warke ko kuwa nan gaba kaɗan za a yanke ƙafar ne idan ta daina aiki. Daga lokacin kenan sunan ɗiyarta zai tashi daga Jawahir ya koma 'Matar Gurgu' Abin da ba za ta iya jurewa ba ke nan. Tabbas ta matuƙar so haɗin Tareeq da Jawahir, ko don yadda Jawahir ɗin ke son shi. Ita kuma tana matuƙar ƙaunar abin da ɗiyarta ke so, shi ya sa ta yi ta fafutuka wajen ganin auren nan ya yiwu. Amma fa a lokacin ba ta taɓa tunanin Tareeq ɗin zai tashi daga cikakke kuma lafiyayyen mutum zuwa nakashashshshe ba. Don haka ba za ta iya jure ganin 'yarta ta ƙare rayuwarta wajen kula da miji ba, a banza a wofi ta lalace. Kullum babu hutu, sai dai kula da nakashashshshen miji. Ina za ta iya zuba ido ta din ga kallon shalelen 'yarta cikin wannan hali? Hakan ne ya sanya ta ɗan jan wani numfashi, tana ji ya zama dole ta buɗe baki ita ma ta magantu ko da hakan na nufin rugujewar zumuncinsu.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 29
"Ki yi haƙuri Dada ji, ban san me zan yi mata ba." Shi ne abin da ta faɗa, ba tare da ta bari sun haɗa ido da ita ba. Kallon ta kawai Dada ji take yi cike da tsananin mamakin da ya hana ta furta komai. Ji take kamar ba gaske ba ne, waɗannan maganganun ba daga bakin Maimunatun suke fitowa ba.
"Jawahir har cikin zuciyarki kike faÉ—ar wannan maganar?" Abeey ya faÉ—a bayan ya kalli Jawahir É—in. Kasa haÉ—a ido ta yi da shi, kawai ta ci gaba da kallon wani wajen kana ta buÉ—e baki da niyyar soma magana, Abeey ya katse ta da faÉ—in
"Ɗaga idanunki ki kalle ni sannan ki tabbatar mini da abin da kika faɗa." Kamar ba za ta ɗaga idanun nata ba, haka dai ta daure ta kalli Abeeyn a ɗan tsorace. Ba ta buƙatar ƙarin bayani, don ta san abin da yake buƙatar ta ce, don haka ta buɗe baki ta ce
"Eh Abeey a yi haƙu..." Ɗaga mata hannun da Abeey ya yi, shi ne ya sanya ta katse maganar da ta fara, ta yi saurin yin ƙasa da kanta. Tun da ta fara magana ya ɗaga lumsassun idanunsa ya kafe ta da su, ba ya buƙatar wani ƙarin bayani daga Jawahir. Domin kuwa, duk wani bayani da yake so ya sani ya fuskance shi daga cikin muryarta. Ya san Jawahir tana son shi, bai kuma taɓa tunanin tana son shi don ƙirar jikinsa ba, duk da yadda ya kamata ya fahimta, ko don yadda maganganunta da yawa ba sa wuce a kan kyawunsa ne da sauran su. Amma bai taɓa barin hakan ya yi tasiri a zuciyarsa ba. Sai ga shi yanzun ƙiri-ƙiri ta bayyana ba za ta iya aurensa ba, ba kuma don komai ba sai don nakasar da ya samu a ƙafarsa. A hankali ya lumshe idanunsa yana jinginar da kansa kan kujerar da yake kai ba tare da ya ce komai ba. Dubansa Abeey ya maida kan Umma ya ce
"Maimunatu kin amince da abin da yarinyar nan take faɗa?" Ya ƙare maganar har lokacin yana kallon ta. Shiru ta yi na tsawon sakanni kamar mai tunani, kafin ta gyara zama ta ce
"Toh ya zan yi da ita Yaya? Ita ta ce tana so tun farko, yanzu kuma ta ce ba ta so saboda wani dalili. Sai nake ganin kamar babu abin damuwa, tun da dai ra'ayi ne. A yi haƙuri kamar yadda ta faɗa ɗin." Tun da ta fara magana Abeey ke kallon ta har ta ƙarasa. Ya yi matuƙar mamaki, maganar Umma da ita kanta Jawahir ɗin sun ba shi mamaki. Ya kuma jefa shi cikin shakkun halayya da ɗabi'un mutane da ka iya sauyawa cikin ƙanƙanin lokaci. Bai taɓa tunanin haka daga Umman Jawahir ba. Bai taɓa tunanin akwai ranar da za ta zo, don Tareeq ya samu nakasa a ƙafarsa ta bi bayan ɗiyarta na ƙin aurensa ba. Ta ɓangaren Dada ji kuwa shiru ta yi tana kallon Maimunatun. Lallai duk inda aka ce ɗa ba naka ba ne, wani lokacin sai hakan ya bayyana. Tun da ta ɗauki Maimunatu take riƙe da ita tsakani da Allah ba tare da ta taɓa nuna mata wani bambanci tsakaninta da Alhassan ba. Duk wanda ma bai sani ba, ba zai taɓa cewa Umman ba 'yar Dada ji ce ba. Don kuwa tun da take ba ta taɓa buɗe baki ta ce ba 'yarta ba ce. Kullum burin ta ma kar wani ya gane ba ita ta haife ta ba. Duk wata kulawa da ya kamata uwa ta ba wa ɗiyarta ta ba wa Umma. Babu abin da ta rage ta da shi wanda uwa za ta yi wa ɗanta. Sai ga shi lokaci ɗaya ta guji jininta, don kawai Allah Ya jarabce shi da ciwo. Ciwon da suke fata da addu'ar Allah Ya yaye masa, Ya sa ya warke. Amma ita da ɗiyarta sun juya masa baya, sun nuna ba su yarda da ƙaddara ba, sun fito fili sun nuna dalilin da ya sa suke son Tareeq, ba tare da tunanin yadda hakan zai janyo tangarɗa wa zumuncinsu ba.
"Za ku iya tafiya. Allah Ya saka da alkhairi." Abeey ya faɗa yana jin yadda zuciyarsa ke zafi. Ya fi jin zafin ƙanwar tasa a kan ɗiyarta, domin bai taɓa zaton haka daga gare ta ba. Ba su ce komai ba dukkansu suka miƙe, ba tare da sun kalli kowa ba, suka fice daga ɗakin. Daidai lokacin da suka fito daga ɗakin, ita ma Maami ta fito daga nata sashen. Ta kalle su saboda yadda ta gan su kamar a birkice. Ba wani mutunci suke yi da Umman ba, amma yau ɗin sai ta ji ina ma a ce suna yi, ko don ta ji abin da ya faru, saboda yadda yanayin Umman ya nuna kamar ba lafiya ba. Kamar ba ita ba, ta ce bayan ta ɗan rage tazarar da ke tsakanin su
"Lafiya me ya faru?" Ta faɗa tana ƙare musu kallo, kallon da a idanunsu ya fi kama da na rainin hankali ko wulaƙanci. Wani banzan tsaki Umma ta sauke tana jan hannun Jawahir, kamar ba za ta ce komai ba, don kwata-kwata ba ta yin Maamin, amma sai ta ce
"Ban sani ba. Idan gulmar kike so, me ya hana ki zuwa taron da Yaya ya shirya? Ba fa na son iya-shege." Umma ta ƙare maganar tana jefa mata wani banzan kallo. Daga haka ba ta jira ta ce komai ba, ta ja hannun Jawahir suka wuce suka bar ta a wajen. Bin su ta yi da wani wulaƙantaccen kallo, tana ji yau ɗin gaba ɗaya ta gama muzanta. Me ya sa ma ta yi mata magana bayan dama tun can ba shiri suke yi ba? Ta ja tsaki tamkar za ta tsinka harshenta. Baƙin ciki ya bi ya cika mata zuciya. Kawai sai ta juya ta koma sashenta ranta a mugun ɓace.
A ɗaya ɓangaren kuwa tun bayan da suka fita shiru ne ya biyo baya na tsawon mintuna masu yawa. Babu wanda ke da niyyar cewa komai, saboda yadda dukkanninsu kowa da abin da yake saƙawa. Sosai zuciyarsa ke masa wani irin zafi. Wanda rabon da ya ji shi tun bayan rabuwarsa da Diyana. Me ya sa ba shi da sa'a ne shi kam? Sun yi soyayya da Diyana kamar babu gobe, sai dai ashe gaba ɗaya tana son shi ne don dukiyarsa, dukiyar da ta yi ƙoƙarin mallake ta tun kafin ta kai ga shigowa gidansa. Ba domin ikon Allah ba da tuni wani zancen ake ba wannan ba. Bai so Jawahir ba, amma kuma ya amince da aurenta, ita kuma ga abin da ya faru. Kenan shi ƙaddararsa a kan soyayya take? Ko kuwa ya kira ta a kan mace ne? Macen ma wadda sai yana dab da aurenta?
"Hidaya." Da kaushashshiyar muryarsa ya ambaci sunan, bayan ya buɗe idanunsa da suka rine daga fari fat, zuwa ja. Shi kaɗai ya san irin zafin da yake ji a ƙirjinsa. Ba ya tunanin zai iya ci gaba da zama cikin ɗakin, gwara ya samu ya keɓance kansa ko ya ji sukunin abin da yake ji.
"Na'am Yah Tareeq." Ta faɗa a matuƙar sanyaye tana kallon ɗan'uwan nata cike da tausayawa. Tun kafin ya yi magana ta fahimci abin da yake nufi, don haka ta miƙe, kai tsaye ta ƙarasa bayansa ta shiga tura shi. Daidai suna dab da gifta Maama ta yi ƙarfin halin faɗin
"Ba na son tunani Tareeq. Ka samu ka yi bacci, za mu yi magana zuwa safiya. In Sha Allah hakan ne mafi alkairi, kar ka saka wa kanka damuwa. Hakan ma taimakonmu Allah Ya yi, ta hanyar nuna mana masoyanmu na gaske da kuma waÉ—anda ba na gaske ba." Shiru ya yi yana saurarar abin da Maaman take faÉ—a, bai ce komai ba kawai ya jinjina kansa, suka wuce. Ita ma Dada ji bin su ta yi da kallo cike da tausayin jikan nata.
... "Wai me kike jira ne? Ko dai kin haƙura kin fasa ɗaukar fansar ɗan'uwan naki? Ko dai ba kya so a hukunta Tareeq ne?" Maganganun da Yohana ya faɗa mata ke nan, waɗanda suka saka ta yin shiru kamar mai nazari. Kafin ta kai ga cewa komai ya sake faɗin
"Anya kuwa kina lissafin ragowar kwanakin da muke da su? Cikin sati biyu kwana nawa muke da shi? Ki faɗa mini idan kin fasa ne in daina damun kaina." Sai a lokacin sannan ta sauke ajiyar zuciya, ta buɗe baki da ƙyar ta soma faɗin