← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 49

Sashe 28

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"In Sha Allah zai samu sauƙi. A je a kawo gwajin nan yanzun nan, za mu san abin yi ne bayan an yi su." Cikin sauri ta jinjina kai, ba ta sake cewa komai ba ta fice daga office ɗin. Sai kuma da ta fito ɗin sannan ta dakata tana kallan takardar tamkar idanunta za su faɗo. Sai a lokacin ƙwaƙwalwarta ta tuna mata babu ko sisin kwabo a jikinta, ba kuma ta da wanda za ta tunkara ya ba ta kuɗin yin gwajin. Ta lumshe idanunta tana ambatar sunan Allah daidai lokacin da ƙirjinta ya wani irin bugawa. Buɗe idanunta ta yi, ta shiga jefa su cikin asibitin kamar mai neman wani abu. Cikin rashin sanin abin yi ta shiga taka ƙafafunta, tunani birjik cikin ƙwaƙwalwarta, mafita kawai take nema, mafita kawai take so. Ameer take so ya sami lafiya, toh amma ta ya ya? Tana ci gaba da waɗannan tunanukan sai tsintar kanta ta yi cikin harabar asibitin. Ta sake wuwwulga idanunta tana kallon mutanen da ke zaune, wasu na tsaye, wasu kuma na hira. Kai tsaye ta soma takawa, ba ta jira komai ba, ta tsuguna har ƙasa lokacin da ta isa dab da wata mota, wadda wani babban mutum ke tsaye, gefensa kuma wata mata ce, ya yin da wani saurayi da a ƙalla zai yi shekaru 30, ke kusa da mutumin.

"Don girman Allah ku taimaka mini da kuɗin gwajin waɗannan, ƙanina ne ba shi da lafiya, kuma ba ni da komai, don Allah ku taimaka mini." Ta yi maganar idanunta a kan mutumin.

"Ka ga halin mutanen koh? Har sun fara." Matar ta faɗa tana jan tsaki a ƙarshen maganar tata. Kallon Daneen mutumin ya yi, kafin ya maida dubansa kan matarsa ya ce

"Idan ma ba su fara ba ba ni da nutsuwar saurarar kowa a yanzu.. Kai Yohanah ina jiran ka, kar ka ƙara ko da minti 10 ne a kan lokacin da na ba ka. Na dai faɗa maka, ka kuma kiyaye." Ya ƙare maganar yana kallon saurayin da ke gefensa, wanda ke sanye cikin wata riga da wando crazy. Kansa da wani banzan aski, ya yi cibiri-cibiri a tsakiyar kan.

"Toh sai na ƙaraso." Ya faɗa da gurɓatacciyar hausarsa, da tun daga fara maganarsa za ka fahimci ba bahaushe ba ne. Ko da yake fuskarsa ma kaɗai ka kalla za ka iya fahimtar hakan, daga zarar kuma ya yi magana shi ne za ka tabbatar. Bai jira wani ya sake cewa komai ba ya faɗa cikin motar, matarsa na gefensa ya ja ya fice daga asibitin. Daneen ta bi su da kallo tana jin wata faɗuwar gaba na kama ta. A hankali ta ɗan sake runtse idanunta tana miƙewa a kan ƙafafunta, har lokacin idanunta na bin ƙurar da mutumin nan ya bari.

"Nawa kike buƙata?" Ta ji an ambata daga bayanta. Da sauri ta juyo har tana ƙoƙarin yin tuntuɓe ta kalli matashin saurayin da a kira da 'Yohana'. Kawai sai ta miƙa masa takardar. Maimakon ya kalli takardar, sai ya ci gaba da bin ta da kallo, tun daga sama yake kallon ta har ƙasa, wanda har hakan ya ɗan so ya sa ta tsargu, har ta kai ga ta soma janyo addu'a cikin zuciyarta. Sai ya maida dubansa kan takardar ya shiga karantawa.

"Mu je." Ya ambata yana yin gaba. Babu musu Daneen ta soma binsa. Hausarsa kwata-kwata ba ta da daɗin saurara, saboda yadda bai iya ta ba, kawai dai yana kwaɓawa ne. Dukkan kuma wasu alamu sun nuna yarinyar nan da ke gabansa ba lallai ta iya turanci ba. Don haka suna ci gaba da tafiya ya ce

"Kina son taimako a kan duk abin da kike so na yi miki?" Duk da ya yi maganar a juye, amma tabbas ta fahimce shi, dalili kenan da ya sanya ta jinjina kai tana faÉ—in

"Ehh don Allah." Ajiyar zuciya ya sauke, kafin ya ce

"Alright, I will help you, but ke ma za ki taimaka mini a kan wani abu. Get it?"

"Zan taimaka maka idan dai har ka taimake ni, ni dai burina kawai É—an'uwana ya samu lafiya."

"Ohk don't worry, he will be fine soon." Duk da ba wani turanci ake yi musu a makarantarsu ba, amma tabbas ta fahimci abin da yake nufi, don haka ta jinjina kai kawai.

Har bayan shuɗewar wasu awanni Daneen na tare da Yohana, bayan an yi wa Ameer gwaje-gwajen da likita ya buƙata. Kuma da taimakon Ubangiji, taimakon gaggawar da aka ba shi ya taimaka masa matuƙa, wanda har bayan dawowarsu daga gwajin ya samu wani wahalallen bacci ya ɗauke shi. Sosai Daneen ke ci gaba da jajanta kirkin Yohanah, don duk wasu alamu sun nuna ba musulmi ne ba. Abin da ya sa kuma ta ƙara tabbatarwa, shi ne da lokacin Sallah ya yi ba ta ga ya tashi ya yi ba. Sai dai taimaka matan da ya yi, ya matuƙar yi mata daɗi, ta kuma gode wa Allah da ya kawo mata shi a irin wannan lokacin da ta ke buƙatar taimako.

.."Zuciyarsa ta yi raunin da ana buƙatar a yi masa aiki, idan ba haka ba a kowanne irin lokaci za a iya rasa shi." Likitan ya faɗa yana kallan Yohanah. Dama ya san da wuya idan ba haka ne zai faru ba, saboda yadda shi kansa da ba likita ba ya ga yanayin Ameer ɗin, da kuma gwajin da aka masa. Hannu ya miƙa wa likitan suka gaisa kafin ya fita daga office ɗin. Kamar yadda ya tsammata kuwa, Daneen na ƙofar tana jiran sa. Kallon sa kawai take yi, tana jira ta ji abin da zai ce. Fahimtar hakan ya sanya shi faɗin

"Ana buƙatar a yi masa aiki a zuciya." Wani irin jiri ne ya kwashi Daneen, lokaci guda wani duhu ya zo ya mamaye ganinta. Ta yi gefe za ta faɗi, duk da yadda take ƙoƙarin ganin ba ta zube ba. Dalili kenan da ya sanya Yohana kai hannunsa ba tare da wani tunani ba ya riƙo ta. Wani irin runtse idanunta ta yi, tana komawa kan ƙafafunta, ta yi maza ta buɗe a kan hannunsa da ke kan nata hannun, sai kuma ya yi saurin janyewa yana furta

"Sorry girl, Sorry please." Ya faɗa saboda yadda ya ga tana bin sa da wani irin kallo. Ba tare da ta bi ta kan abin da yake faɗa ba, ta zube a kan ƙafafunta tana jin yadda bugun zuciyarta ya ƙaru. 'Aiki a zuciya?' Shi ne abin da take ta maimaitawa, hawaye tuni sun cika mata idanunta.

"Stop crying Cutie. Ki tashi mu samu mafita." Ya faɗa yana kallan yadda take kuka kamar Baby. Duk wasu alamu sun nuna yadda take matuƙar ƙaunar ɗan'uwanta. Gaba ɗaya aikinta da kuma maganganunta sun nuna shaƙuwa da kuma tsananin ƙaunarta da ɗan'uwanta. 'Me hakan ke nufi?' Ya tambayi kansa. Sai kuma ya yi gefe, ya fito da wayarsa daga cikin aljihu ya danna wa wata number kira.

"What's going on?" Ya faɗa bayan an ɗaga wayar. Shiru ya yi na ɗan wasu sakanni, yana saurarar abin da ake faɗa masa daga can ɓangaren, kafin ya ce

"Ya yi, send me the address now! I will call you later."

"Ohk." Ya sake faÉ—a bayan wasu sakanni. Jefa wayar ya yi cikin aljihu kafin ya koma inda ya bar Daneen, da ke zube a wajen tamkar wadda aka dasa.

"Tashi mu tafi." Da sauri ta É—aga idanunta ta kalle shi. Ya jinjina mata kai kana ya ce

"Ehh, asibiti za mu sauya.. Za ki iya sadaukar da wani abin da kika mallaka saboda É—an'uwanki."

"Matuƙar dai zai samu lafiya." Ta faɗa tana jinjina kai.

"Ohk let's go. But let me go and meet the doctor, I will explain everything to him. Wait for me here." Daga haka bai jira ta ce komai ba ya faɗa cikin office ɗin. Wajen minti 20, sai ga shi ya fito, tana tsaye kamar yadda ya bar ta. Ya miƙa mata takardun hannunsa kafin ya wuce ɗakin da Ameer yake.

Runtse idanunta Daneen ta yi tana sake gode wa Allah. Ba don Allah Ya kawo mata Yohanah ba, da ba ta san yadda za ta yi ba. A bayan motar Yohanah ɗin aka kwantar da Ameer, da na'ura ke taimaka masa wajen numfashi. A gaban motar Daneen ta zauna, ya yin da shi kuma ya zauna wajen mai tuƙi. Babu ɓata lokaci ya ja motar suka fice daga cikin asibitin. Suna tafiya Daneen na juya wa baya ta kalli Ameer, sai kuma ta dawo ta ci gaba da kallon titi. Ganin abun take tamkar a mafarki, tamkar ba Ameer ɗinta ba. Har suka yi tafiya mai nisa ba ta daina tunane-tunane ba. Tun daga bakin asibitin za ka fahimci lallai babban asibiti ne, babban ma irin babban da ya amsa sunansa babba. Hamshaƙi, haɗaɗɗe wanda kallo ɗaya za ka masa, ka san ya lamushe kuɗaɗe da yawa wajen gina shi. Idan kuwa aka shiga ciki ba za ka taɓa zata a cikin Nigeria kake ba, saboda matuƙar haɗuwa da ya yi. Kai tsaye a inda aka tanada don ajje motoci Yohanah ya yi parking na motarsa, Daneen kuwa ban da ci gaba da kallon cikin asibitin babu abin da ta yi, mamaki take toh me ya kawo su nan ɗin? Saboda yadda duk wasu alamu suka nuna nan ɗin bai yi kama da inda za a taimaka wa talaka ba. Ita tun da take ma, ko kuma ta ce tun da suka shigo garin Kano ba ta taɓa ganin waje mai kyau da tsaruwa irin wannan ba. Sai dai da yake gaba ɗaya hankalinta yana kan Ameer ya sa yana ida yin parking ta sauka daga motar ta koma inda Ameer yake. Shi ma saukar ya yi. Cikin ƙanƙanin lokaci aka shigar da Ameer cikin asibitin, da cikinsa ya fi harabarsa tsaruwa nesa ba kusa ba.
Chapter 28 · 0% Book details