Sashe 46
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina nan ina iya ƙoƙarina. Na matuƙar gode da kulawa, kuma in Allah Ya yarda za ka ji ni zuwa gobe. Na gaji da zaman gidan nan kwata-kwata, ba na son ci gaba da kasancewa gida ɗaya da mutumin nan. Ba na son ganinsa ko kaɗan, duk lokacin da na gan shi kewar ɗan'uwana dawo mini take. Ina jin zuciyata na mini zafi, wani irin abu ke tokare mini a ƙirji ya din ga tokare mini numfashi. Ba na son ganin sa ko kaɗan. Zan yi ƙoƙari in Allah Ya yarda a cikin kwana biyu in san yadda zan yi in shiga ɗakinsa." Jinjina kai Yohana ya yi kafin ya ce
"Yawwah, ki ƙoƙarta. Kar ki manta har yanzu ruhin ɗan'uwanki na can cikin rashin salama. Gwara a yi maza a hukunta shi ko ruhinsa ya samu salama." Jinjina kai kawai Daneen ta yi kamar yana gabanta. Soma fahimtar halinta da ya yi ne ya sanya shi fahimtar ta ji abin da ya faɗa. Don haka bai sake cewa komai ba, kawai ya katse wayar. Daidai lokacin da aka turo ƙofar ɗakin aka shigo. Ita ma kuma daidai lokacin ta fito daga cikin toilet. Hidaya da Sultanah ne, suka sakar mata murmushi kusan lokaci guda. Maida musu da martanin murmushin ta yi, kana ta ƙaraso cikin ɗakin.
"Ohh, kwata-kwata ba na jin daÉ—in jikina yau É—in nan wallahi." Sultanah ta faÉ—a tana É—an dafe kanta bayan ta zube a kan luntsumemen gadonsu.
"Ke dai malama kawai ki ce Yah Abdoul bai kira ki ba." Hidaya ta faÉ—a tana dariya. Harara Sultanah ta jefa mata kana ta ce
"Lallai ma Sisi, wallahi ba ki da dama. Toh ko damuwar Yah Tareeq ai ta isa ta hana mu walwala daga ni har ke É—in." Cikin na'am da zancen Sultanah Hidaya ta kwantar da kanta kan pillow kana ta ce
"Wallahi ke kam ki bari kawai. Duk jikina a sanyaye yake tun jiya wallahi."
"Daneen." Hidaya ta faÉ—a tana kallon Daneen da ta yi shiru tana kallon wani wajen kamar mai tunani. Da sauri ta kalli Hidayan ba tare da ta ce komai ba. Cikin mamaki ta ce
"Lafiya kuwa?" Ɗan murmushin yaƙe ta aro ta yafa a kan fuskarta kafin ta ce
"Babu komai."
"Kin tabbatar 'yar'uwa?" Hidaya ta sake tambaya cikin kulawa. Jinjina kanta ta yi tana miƙewa. Ta ce bayan ta kalli Hidaya
"Bari na É—an fita." Jinjina kai Hidaya ta yi tana faÉ—in
"Tohm." Daga haka Daneen ta fice daga É—akin, ya yin da Hidaya da Sultanah suka bi ta da kallo har ta fice.
"Ba ta da walwala gaba ɗaya, kamar akwai wani abu da ke damun ta." Sultanah ta faɗa har lokacin ba ta daina kallon inda Daneen ta ɓace wa ganinsu ba. Cike da amincewa da zancen nata Hidaya ta jinjina kai kana ta ce
"Na gani fa.. Ga shi ba ta saurin sabo. Ta ƙi sakin jikinta kwata-kwata ballantana mu shiga jikinta."
"Wallahi, abin na ba ni mamaki." In ji Sultanah.
A hankali take taka wa cikin palourn, sanye take cikin doguwar rigar atamfa, da kuma dogon hijabin da ya wuce har ƙasan gwuiwarta.
"Ohk." Shi ne kawai abin da ta ji, wanda hakan ya matuƙar tsorata ta, don ba ta yi tsammanin akwai wata halitta cikin ɗakin ba. Domin dai kuwa ita ba ta gani ba.
"Wayyo Allah na." Ta faɗa bayan ta dafe ƙirjinta, maganar tata ke nan da ta ɗauki hankalinsa. Ya ɗaga kai ya kalle ta, daidai lokacin da ita ma ta sauke nata a kansa. Sam ba ta yi tsammanin ganinsa a wannan lokacin ba. Kafin haɗuwar idanunsu waje ɗaya ta yi saurin janye nata tana sakin ajiyar zuciya, lokaci guda rashin annurin fuskarta na sake bayyana. Wani irin ɓacin rai tuni ya mamaye ta.
'Kar ki kwafsa' Ta ji wani ɓangare na zuciyarta ya gargaɗe ta. Ji take kamar ba za ta iya ba, amma haka ta daure, ta cije, ta kuma yi iya bakin ƙoƙarinta wajen haɗa kalmomi ta ce
"Barka da wannan lokacin." Shiru ya yi yana nazarinta na tsawon sakanni. Kamar kuma ba shi ba, sai ya janye idanunsa kafin ya ce
"Barka dai. Ina za ki je?" Ya ji tambayar da yake tsarawa cikin ransa ta yi masa katsalandan wajen fitowa. Har ta ware idanunta da niyyar kallon sa, sai kuma ta fasa, don ba ta so kallon fuskarsa ya tuna mata da waye shi. Dalili ke nan da ya sanya ta faÉ—in
"Na ga su Hidaya suna hutawa, shi ne na ce bari na tambaye ka ko za a gyara maka ɗaki ne." Ta ƙare maganar ita a karan kanta tana jin wani banbarakwai. Shiru ya yi na tsawon sakanni ba tare da ya ce komai ba. Har ta cire ran zai amsa, ta kuma ji haushin kanta sannan ta jiyo muryarsa can ƙasa ya ce
"Yanzu dai ba na buƙata kam." Ya dakata a nan. Bai yi niyyar sake cewa wani abu ba, sai dai ko babu komai ita ɗin mace ce mai muhimmanci a rayuwarsa, bayan haka kulawa ce ta nuna a gare shi, yana da kyau ko ya ya ya nuna ya yaba. Don haka ya ce
"Amma idan ina buƙata zan yi miki magana. Kira mini Sultanah ko Hidaya." Ya yi maganar lokaci guda. Cike da takaici da haushi ta juya ba tare da ta ce komai ba. Ya ɗan lumshe idanunsa na tsawon lokaci yana saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa. Har bai san lokacin da Sultanah ta ƙaraso cikin ɗakin ba. Sai da ya ji hannunta saman kujerar da yake kai sannan ya ankara.
"Yah Tareeq." Ta faÉ—a tana kallon yadda duk wasu alamomi suka nuna ya dawo daga tunani ne. Ba tare da ya amsa kiran sunansa da ta yi ba ya ce
"Kai ni É—akin Maama." Ya faÉ—a kai tsaye. Babu musu ta tura shi har zuwa bedroom É—in Maaman. Daga haka ta juya. Maama ta kalle shi tana faÉ—in
"A'ah, ƙarasowa ka yi kenan." Jinjina kai ya yi kana ya ce
"Ehh Maama, wata muhimmiyar magana nake so mu yi."
"Toh! Ikon Allah! Me ya faru kai kam? Sanar da ni." Maama ta ƙare tana gyara zamanta. Ya yi shiru yana nazarin ta inda zai fara maganar, duk da yadda duka jikinsa ya yi na'am da abin da ya yanke. Bai san ya daɗe cikin ɗakin ba tare da ya ce komai ba, sai da Maama ta ce
"Tareeq!" Ta kira sunansa cike da mamakin yadda ta ga ya faÉ—a duniyar tunani. Duk da ta ga tarin damuwa a kan fuskarsa, sai dai hakan ba abin mamaki ba ne, duba da abin da ya sake faruwa tsananinsa da Jawahir. A hankali ya É—an lumshe idanunsa a nutse kana ya buÉ—e su a kan Maama. Cikin nutsuwa ya soma magana, kamar wanda ba ya so a ji abin da yake faÉ—a.
"Maama.."
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 30
"Ina ganin idan har kin amince da abin da zan faɗa, toh na samu mata." Ya ƙare maganar yana kallon ta. Cike da mamaki wanda ya bayyana a kan fuskarta, Maama ke kallon sa. Jin abin take kamar a mafarki. Ya samu mata fa yake faɗi? Ta yaya? A ina? Yaushe hakan ta faru? Anya kuwa ma Tareeq ɗin ne? Duka waɗannan tambayoyin ita kaɗai take yi wa kanta cikin zuciyarta, sai dai har lokacin idanunta na kansa. Bayan wajen shuɗewar sakanni talatin sannan ta ce
"Mata kuma Tareeq? A ina? Wace ce ita? Yaushe kuma kuka haɗu har ka ji ta kwanta maka a rai, har za ka iya auren ta? Faɗa mini Tareeq." Ta yi maganar cike da zaƙuwa da jin amsar da za ta fito daga bakinsa. Hannunsa ya kai a hankali ya ɗan murza goshinsa, kafin ya lumshe idanunsa a nutse yana jin wani irin nauyi cikin ƙirjinsa. Ta ɗauka hakan da ya yi yana nuni ne da ya haƙura da yin maganar saboda yadda ya ga tsananin mamaki a kan fuskarta. Sai dai ga mamakinta sai ji ta yi ya ce
"Maama idan dai har kin amince, zan auri Daneen, idan ita ma ta amince." Wani irin kallo Maama take bin Tareeq da shi, kallon da lokaci guda ya fassara shi da 'Anya kana da hankali?' Bin sa da kallo Maama ta ci gaba da yi ba tare ta ce komai ba. Cikin zuciyarta addu'a take yi, Allah Ya sa ba ƙwaƙwalwar yaronta ce ta taɓu ba. Daneen fa? Cike da fargabar da ta zo ta yi mata dirar mikiya lokaci guda ta ce
"Tareeq." Ta faɗa bayan ta sake kafe shi da idanunta. Saukar da kansa ƙasa ya yi, jikinsa a matuƙar sanyaye. Bai yi tunanin samun cikas tun a wajen Maama ba, shi ya sa ma ya fara yi mata maganar.
"Ka san me kake cewa kuwa? Daneen ce matar da kake nufi ka samu? Da gaske kake yi?" Ta faÉ—a cike da tashin hankali. A nutse ya É—an sauke ajiyar zuciya, yana jin har cikin ransa daÉ—in tambayar da Maaman ta yi masa. Ko babu komai zai fayyace mata komai, dalilansa na son auren Daneen É—in. Ya É—an ja numfashi kaÉ—an yana ajiyewa, kafin ya buÉ—e baki a nutse ya soma faÉ—in
"Maama na yi tunani, na yi tunani har na gaji. A zamanin nan ban san kuma wace mace ce za ta so ni tsakani da Allah ba. Na gwada ta waje, ta ba ni kunya. Kun gwada 'yar'uwa, ita ma ta ba mu kunya. Toh a duk tunanin da na yi, na ga babu wadda ta dace in aura da ta wuce Daneen." Daga haka ya ɗan dakata bayan ya sauke gajeren numfashi a hankali. Ba ya buƙatar jin wani abu daga bakin Maama a kan maganar da ya yi, don haka ya ci gaba da faɗin
"Yarinyar nan ta ɗauki ƙodarta ta ba ni, ba tare da sanin waye ni ba. Ba tare da buƙatar komai ba Maama. Ba kya tunanin ta cancanta na aure ta?"
"Idan kuma da wata manufar ta bayar fa?" Maama ta yi saurin katse shi da faÉ—in hakan, tun kafin ya ida sauke maganar. Lumshe idanunsa ya yi a hankali, yana buÉ—ewa lokaci guda.