Sashe 5
Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ki yi kuÉ—in mota."
Ba ta yi niyyar tankawa ba, sai dai yadda zuciyarta ke bugawa, tana ƙara zafafa da wannan cin mutuncin da ya mata ya sa ta ji ba za ta iya ba. Shirun da za ta yi tamkar nuni ne da ta ji haushin fitar ta daga gidan, wanda ta san tabbas hakan ze yi masa daɗi, ba ma shi kaɗai ba har Hajiya Amina. Sai dai tana dakatawa da niyyar juyawa ta yi masa magana, zuciyarta ta ƙeƙashe, tarin takaici ya cika zuciyarta. Ba ta jin tun da take a rayuwarta akwai fuskar da ba ta ƙaunar sake gani kamar ta Alhaji Baita. Kamar yadda ya ce babu shi babu ita, babu kuma shi babu 'ya'yansa, toh har abada sun rabu ɗin kenan. Daga haka ta gewaye kuɗin ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake ko da waiwayowa ba ne.
... A ƙofar gidansu ta tsaya tana kallan ƙofar gidan kamar wadda ta fara ganinsa yau. Ta yi shiru tana cigaba da kalla zuciyarta na harbawa. Tunanin abin da ke cikin gidan take, tunanin da wane ido za ta kalle su ta sanar da su Alhaji Baita ya sake ta take. Sai dai ko ma mene ne zai biyo baya ta shirya karɓarsa. Tun da ba ta da inda ya wuce mata nan ɗin. Tuna hakan ya sanya ta ɗaga ƙafafunta ta jefa cikin gidan nasu, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga gidan.
"A'uzubillahi minash shaiɗanir rajim." Shi ne abin da Dada ta ambata ƙirjinta na bugawa tana kallan Inna-wuro. Dakatawa Inna-wuro ta yi, jin da ta yi tun a lokacin gaba ɗaya ƙwarin gwuiwar da ta ji kafin ta shigo gidan yana rugujewa yana yin nasa wajen. Tun kafin ta ƙara taku ɗaya Dada ta matso tana faɗin
"Me ya dawo da ke gida kuma? Me kika zo yi mana a gida?" Buɗe baki ta yi jiki a matuƙar sanyaye ta ce
"Dada.."
"Kar ki sake ki ƙara kiran sunana. Daga ganin idanunki akwai abin da kika shuka, faɗa mini me ya faru. Me ya dawo da ke gida?" Girgiza kanta ta soma yi, daidai lokacin da wasu sabbin hawayen suka sake cika idanunta taff, ta buɗe baki kamar me koyon magana ta ce
"Ya.. sake.. ni."
Salati da sallallamin da Dada ta soma yi shi ne ya fito da Baffa daga ɗaki, ya ƙaraso yana faɗin
"Lafiya kuwa Uwar gida?" Ya ƙarasa maganar daidai lokacin da idanunsa suka sauka a kan Inna-wuro, da zuwa lokacin hawaye har sun jiƙa fuskarta.
"Inna-wuro?" Ya ambata yana kafe ta da idanunsa. ÆŠaga jajayen idanunta ta yi ta kalli Baffan, daidai lokacin da Dada ta fashe da kuka.
"Subhanallahi me ya faru?" Baffa ya tambaya yana kallan Dada.
"Tambayi 'yarka, tambayi 'yarka kai kam. So take ta kashe ni wallahi" Shi ne abin da take maimaitawa cikin tsananin ƙunar zuciya. Juyawa ya yi ya kalli Inna-wuro, ya buɗe baki da niyyar tambayar ta, Dada ta ji ba za ta iya tsayawa har sai ta faɗa da bakinta ba. Don haka ta buɗe bakinta ta ce
"Alhaji Baita ya sake ta, ya sake ta. Mu kuma shi kenan mun shiga uku."
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Baffa ya ambata yana kallan Inna-wuro da ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne. Idanunta na kallan ƙasa cikin rashin sanin abin yi. Kamar wadda aka tsikara Dada ta miƙe ta dawo gaban Inna-wuro, ta goge hawayen fuskarta sannan ta ce
"Saki nawa ya miki?" Ta tambaya cikin tsananin tashin hankalin da ba ta ji makamancinsa lokacin da Inna-wuron ta ce an sake ta ba.
"ÆŠaya ya miki koh?" Dadan ta sake ambata kafin Inna-wuron ta kai ga cewa komai. Cike da tsoron jin abin da zai fito daga bakinta. Shiru Inna-wuro ta yi tana tunanin ta inda za ta fara, sai dai kuma tana tsoro kar Dadan ta kawo mata duka, saboda wani irin kallo da take bin ta da shi.
"Saki uku." Ta faɗa jikinta na ƙarasa mutuwa gaba ɗaya. Ta riga ta saddaƙar yau ɗin Allah ne kaɗai ze raba ta da Dadan. Sai dai Dada kasa cewa komai ta yi, ban da komawa da ta yi baya ta yi zaman ɗabaro ta yi shiru, ban da bugawa babu abin da zuciyarta take, ta kuma kasa furta komai.
"Inna-wuro ashe ba ki da hankali? Me kika yi wa mijinki ya sake ki?"
"Baffa babu abin da na masa.. Wallahi ban masa komai ba Baffa." Ta ƙare maganar tana kuka jajayen idanunta a kan Baffa. Cike da fatan yau ɗaya ya ji tausayin ta, ko da kafaɗarsa ne ya ba ta ta ɗora ta yi kuka ko da za ta ji sassaucin abin da take ji a cikin zuciyarta.
"Ƙarya kike munafuka, ƙarya kike yi. Yo ko yankar namanki yake ai kya zauna. Uban me bakinki yake lokacin da kika ji yana ƙoƙarin ambatar sakin, mai ya hana ki saurin katse shi ba tare da ya ƙarasa ba. Ashe mahaukaciya ce ke Inna-wuro ban sani ba? Ashe bayan kanki da kike yi wa baƙin ciki har mu kike yi wa? Wallahi ko ki faɗa mini dalilin da ya sa ya sako ki ko in miki shegen duka yanzun nan. Ki buɗe baki ki mini magana kafin na ci ubanki." Duk da zagin ta da ta yi hakan be sanya Baffa ko da kallan ta ne ba, ballantana ya nuna ya ji zafin hakan. Shi kansa kallan Inna-wuron kawai yake don jin amsar da za ta fito daga bakinta.
"Baffa ciki ne da ni, shi kuma ba ya so. Wallahi shi ne kawai dalilin, ya ce ya yanke duk wata alaƙa ta da shi, har 'ya'yana ma."
ÆŠauke wuta gaba É—aya kansu ya yi, musamman Baffa. Ya rasa me ze ce? Ya ma rasa ta ina ze fara. Sai kawai ya kama bakinsa ya yi shiru yana jira ya ji abin da Dada za ta faÉ—a. Wane hukunci za ta yanke a kan Inna-wuron wanda duk hukuncin da ta yanke ya riga ya zauna daram.
"Kin cuce mu wallahi, kin cuce mu." Dada ta yi maganar cikin ƙunar zuciya, tana fashewa da wani sabon kukan baƙin ciki. Ji take kamar ta rufe Inna-wuron da duka ko ta ji daɗi, sai dai yadda take jin zuciyarta idan ta fara dukan ta san za ta iya mata lahani. Tsabar takaici ma ta kasa ko da yunƙurin dukan Inna-wuron ne.
"Toh yanzu da kika ɗauko ƙafa kika dawo gida, ba ma ke kaɗai ba har waccan yarinyar da ke bayanki, da kuma abin da ke cikinki kina nufin mu za mu din ga ciyar da ku? Toh wallahi kin yaudari kanki. Shigo idan zaman gidan kike so ga ki ga shi, amma fa tabbas ki sani za ki yaba wa aya zaƙinta."
"Ki yi haƙuri Uwar gida." Baffa ya faɗa ƙasa-ƙasa ko hakan ze sa Dadan ta sakko daga fushin da take. Sai dai cikin ɗaga murya ta ce
"Da Allah ni ƙyale ni, ka rabu da ni in ji da abin da ke damu na. Idan ba haka ba daga kai har 'yar taka zan haɗa in ci wa mutunci wallahil azeem. Don na ga kai ma ka fara canja hali, za kuma mu haɗu da kai." Bin ta Baffa ya yi da sauri yana ba ta haƙuri, sai ka ce yaron da ya yi wa uwarsa laifi yake so ta haƙura. Ita kuma ko kallan inda yake ba ta yi ba ta wuce ɗaki, ya bi bayanta ba tare da ya sake bin inda Inna-wuro take da kallo ba. Runtse idanunta Inna-wuro ta yi, tana jin yadda tausayin kanta, da na mahaifinta na kama ta. Ta ɗaga ƙafafunta da suka sage, tana jin yadda Daneen ke mutsu-mutsu a gadon bayanta, wanda hakan ke alamta mata farkawar da ta yi. Ƙarasawa ta yi cikin ɗakinta da ya canja. Ta ɗan gyara a gurguje ta sauko da Daneen, kafin ta nemi waje ta zauna. Gaba ɗaya yinin ranar babu wanda ya sake kula ta, daga Dadar har Baffan. Sai ita ma ta kama kanta ta yi shiru cikin ɗakin tana tunanin yadda rayuwarta da ta 'ya'yanta za su kasance cikin gidan.
... Karɓe kwanon da ke hannun Baffa, Dada ta yi da sauri tana faɗin
"Wallahi ba za ta ci ba, ba ka isa ba. Ƙatuwa da ita da 'ya har da cikin wani a ce mu za mu din ga ciyar da ita? Toh wallahi ba a gidan nan ba. Waye ya hana ta zaman aure? Idan da ita wata ƙatuwar mai hankali ce komai yake mata ai zauna wa za ta yi. Amma da yake shashasha ce duk irin arziƙin da ke gidan Alhaji Baita sai da ta yi abin da ya sa ya sako ta. Toh wallahi ko dai ta fidda miji ta yi aure ko kuma takura da gallazawa yanzu ta fara ganin su cikin gidan nan." Shiru Baffa ya yi jikinsa a sanyaye don be yi tunanin Dadar za ta gan shi lokacin da ya kawo wa Inna-wuro abincinsa ba. Ya haɗiye shakkarta da yake ji ya ce a hankali
"Don Allah ko don shayarwar da take ki bar ta ta ci abincin nan don Allah."
"Na ce ba za ta ci ba." Ta faÉ—a tana shirin barin wajen, bayan ta makawa Inna-wuro wata uwar harara.
"Toh ko yaya ne a din ga ba ta. Tun da dai kin ga yanzu ba ta damar yin aure har sai ta haihu, daga nan duk abin da kike so sai a yi." Baffa ya faɗa yana kallanta cike da fatan ta amsa roƙonsa. Wani kallo ta ƙarasa juyowa ta watsa masa, mamakinsa na kama ta. Lallai dole ne ta tashi tsaye a kan mutumin nan.
"Malam..?" Ta ƙarasa ambatar sunan nasa da alamar tambaya.
"Ki yi haƙuri." Ya yi saurin faɗin hakan yana shirin juyawa jiki a sanyaye da irin kallan da ta masa. Kafin ya kai ga wuce wa Dada ta ce