← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 49

Sashe 18

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba sai mu ce aiki muke nema ba, idan za su ba mu kin ga ai sai mu yi mu samu kuɗi." Ya ƙare maganar yana murmushi. Shiru Daneen ta yi kamar me tunanin wani abu, kafin ta sake ɗaga kai ta kalli gidan. A sanyaye ta kalli Ameer ta jinjina kanta ta ce

"Toh mu gwada koh?" Ta sake tambayarsa. Sai ya jinjina kai yana murmushi.

"Kin ga idan ba su ɗauke mu ba ma ai dai mun ga gidan nasu mun yi musu wayo." Ya ƙare yana dariya. Ita ma er ƙaramar dariyar ta yi tana sake kallan gidan a karo na biyu.

Sai da gari ya sake yin nisa sannan Daneen ta amince Ameer ya je ya ƙwanƙwasa gidan nan. Shi ko tsoro ma ba ya ji, ita ya bar ta da faɗuwar gaba. Shiru babu alamar za a buɗe. Ya juya ya kalli Daneen, kafin ya ce komai ta ce a hankali

"Ko dai ba gida ba ne?"

"A'ah fa gida ne ke kam." Ya ba ta amsa cike da tabbatarwa kamar da gasken ya sani. Be jira ta sake cewa komai ba ya juya ya cigaba da ƙwanƙwasawa. Babu daɗe wa suka ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Kallan juna suka yi shi da ita, Ameer ya yi murmushi kawai, ba tare da sun ce komai ba suka maida duban su kan wadda ta zo ta buɗe ƙofar. Tun daga sama har ƙasa take kallan su, kamar wadda ta ga baƙin halittu. Tana sanye cikin wata doguwar rigar da ba ta kai ƙasa ba. Hannunta ɗore a kan gate ɗin tana cigaba da kallan su.

"Lafiya?" Ta faÉ—a kai tsaye tana jefa musu wani kallo. Kallan juna Daneen da Ameer suka sake yi kafin Daneen ta buÉ—e baki a nutse ta ce

"Aiki muka zo nema, ko kuna da buƙata." Har za ta buɗe baki ta ce ba sa buƙata, sai kuma ta yi shiru. Ta sake kallan Daneen a karo na barkatai kafin ta ce

"Ku shigo." Ta yi maganar tana ba su hanya. Babu musu suka sanya ƙafafunsu zuwa cikin , gaba ɗaya idanunsu a kan cikin gidan, suna kallan irin zubin da aka yi masa, tamkar ba a duniya mutum yake ba. Gaba matar ta yi, ya yin da suka cigaba da bin bayanta.

"Ka sanar wa da Auntyyy ta yi baƙi." Ta faɗa lokacin da suke dab da wuce wani da ke zaune a kan kujera yana danna waya.

"Auntyyy, kin yi baƙi." Wani gabjejen mutum da muryarsa ta fi kama da ta er budurwa ya faɗa yana kallan matar da ke zaune a kan kujera. Sanye cikin doguwar rigar wani material, a ƙalla a shekaru ta ba wa 50 baya. Fuskar nan ta yi ɗau ta yi jajir da farin bature. Sai dai wani sashe na fuskarta duk ya yi baƙi-baƙi, musamman ma daga gefen idanunta. Kanta ɗaure da ture kaga tsiya, ta baza uban ƙananun kitson da suka zuba har gadon bayanta. Kujerun da ke gefen ta kuwa wasu manyan alhazai ne su biyu, da ke sanye cikin shadda ɗinkin babbar riga. Kowanne da ka gan shi ka san kuɗi ya zauna masa babu wai.

"A shigar mini da su ɗaki, ka dai san ina tattauna wa ne mai muhimmanci. Zan ƙaraso daga zarar na gama." Ta ƙare maganar tana wani karairaya kamar wata yarinya er shekara 20.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 12

Kallan juna Daneen da Ameer suka yi, lokacin da suke ƙoƙarin zama a ƙasan kujerar ɗakin da aka shigar da su. Babu wanda ya ce da su ko uffan, haka aka fice aka bar su ciki su kaɗai. A karo na barkatai suka sake kallan junansu kafin Ameer ya ce

"Adda kar fa mu je en yankan kai ne." Ya faɗa yana sakin jakar hannunsa idanunsa sun yi tsilli-tsilli. Wani yawu da ya tsaya wa Daneen a maƙogwaro ta haɗiye tana sake bin ɗakin da kallo ta ce a sanyaye

"Toh mu jira dai mu gani." Ta faÉ—a tana gyara zaman ta. Cikin ranta tana fatan Allah Ya sa ba gidan en yankan kai suka kawo kansu ba.

Bayan wajen minti 30 suna zaune cikin ɗakin amma shiru babu wanda ya leƙo. Zuwa lokacin sun fara ruɗewa.

"Ni dai wallahi ki tashi mu tafi, hmm uhmm." Ameer ya faɗa yana girgiza kai. Ita ma a ɓangaren ta hakan take saƙa wa a ranta, su tashi su fice daga gidan, don da alama ma waɗanda suka kawo su sun manta da rayuwarsu. Tun da ga shi tun da suka tafi ba su sake bi ta kansu ba. Kafin wani a cikin su ya sake cewa komai, sai ga motsi an shigo cikin ɗakin. A tare suka ɗaga ido suka kalli matar da ta shigo. Wannan matar ce ta ɗazun da ke zaune da wasu maza. Cikin shigar ɗazun dai take, da alama ta gama da waɗancan ɗin shi ne tayo nan. Tun da ta shigo idanunta ke kansu, har ta ƙarasa ta nemi waje ta zauna tana cigaba da bin su da kallo.

"Ina wuni?" Suka haÉ—a baki wajen faÉ—ar hakan. Sai da ta É—an yi jimm kafin ta ce

"Lafiya, ku ne baƙin nawa?" Ta faɗa tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta sake ganin gaba ɗaya yanayin Daneen, zubin halittarta da komai na jikinta. Jinjina kai suka yi kafin Daneen ta ce cikin siririyar muryarta

"Eh."

"Kuka ce aiki kuke nema?" Ta ƙare tana jin wani murmushi na taho mata.

"Eh." Daneen ta sake amsa wa a wannan karon ma. Jinjina kai Auntyy ta shiga yi kana ta ce

"Toh, kun samu." Cikin wani irin farin ciki suka É—aga kai suka kalle ta. Ta sake jinjina kai sannan ta ce

"Ƙwarai kuwa. Abin da nake buƙata kawai sirri, da kuma haɗin kai. Ba na son taurin kai ko kaɗan. Yin sa kan sa na kori mutum na har abada. Idan dai har kun amince shi kenan, maganar kuɗi kuma za ku iya samun sa duk ranar da kuka yi aiki. Ke aikin ki ya fi yawa, saboda haka da ke zan fara." Ba tare da kawo komai a kan zancen ta ba Daneen ta ce

"In Sha Allah ba za ki yi kuka da mu ba."

"Haka nake so." Aunty ta faÉ—a, kafin ta É—an É—aga murya ta ce

"Shanawa zo ka shigar mini da yarinyar nan ciki." Shiru ne ya wanzu a wajen, zuwa can wannan mutumin na É—azu ya shigo cikin É—akin. Cikin muryarsa ta mata ya ce

"Aunty ga ni. Ina yarinyar?" Ya faÉ—a yana jefa idanunsa da yake ta wani fari da su cikin É—akin.

"Tashi ki bi shi, zai kai ki inda za ki yi wanka ki shirya." Kallan Ameer da shi ma ita yake kalla Daneen ta yi, kafin ta maida duban ta kan Aunty a sukwane ta ce

"Wannan ƙanina ne." Ta faɗa tana nuna shi.

"Kar ki damu, zai zauna a ɓangaren maza ne. Ki je ki yi wanka ki shirya ke dai, shi ma zai je ya gyara jikinsa." Jin abin da ta faɗa ya sanya ta ji daɗi. Ta miƙe tana ɗaukar jakarta. Da sauri Aunty ta ce

"A'ah ajiye ta, akwai komai na buƙata a ciki." Babu musu ta ajiye ta, ta kalli Ameer ta ce

"Bari na je, ka je ka shirya kai ma ka ji? Sai mu fara aikin da wuri ka ga gidan na da girma." Ta faɗa ƙasa-ƙasa. Jinjina kai Ameer ya yi. Daneen ta bi bayan mutumin nan. Tafiya suka soma yi, suna tafiya yana karairaye karairayensa, shi a lallai dole mace. Ita dai sai taɓe ɗan mitsitsin bakinta take saboda haushi da ya ba ta. A haka har suka ƙarasa wani ɗaki. Tsaya wa ya yi a wajen, ya dakata ya yi knocking na ƙofar, zuwa can aka zo aka buɗe. Wata dattijuwar mata ce da a ƙalla za ta yi shekaru 40 ko da wani abun. Tana sanye cikin riga da zani da ɗan'kwali irin na da ɗin nan.

"Toh ke ga baƙuwa nan kin samu. Na san Aunty ta gama miki bayani." Jinjina kai matar ta yi kafin ta kalli Daneen ta ce

"Shigo." Haka nan kawai ta ji ƙirjinta ya buga, har sai da ta kira sunan Allah, kafin ta soma taka wa. Ta saka ƙafarta cikin ɗakin. Daga haka shanawa ya juya, ya yin da matar ta rufe ƙofar bayan Daneen ta shige cikin ɗakin. Kallan ta matar ta shiga yi kamar wadda ta ga sabuwar halitta, sosai ya yaba da kyawun Daneen matuƙa. Don kuwa idan ban da kayan da suke jikinta, a kallan farko idan ka yi wa fuskarta za ka iya kiran ta da er'india, saboda tsananin kyan da Allah Ya ba ta irin mai ɗaukar hankalin nan. Babu abin da ma ya fi tashin kai a kan fuskarta irin cat eyes ɗinta, masu wani irin shape na musamman.

"Mu je ciki banÉ—akin na ciki." Ta faÉ—a tana nuna wa Daneen ciki. Kallan inda ta nuna É—in ta yi, kafin ta ce

"Toh." Ta yi maganar a sanyaye. Sai da matar ta ƙarasa ta haɗa wa Daneen komai da ta san za ta buƙata na wanka kafin ta fito. Daneen ta ƙarasa ciki tana kallan irin tsarin da aka yi wa banɗakin kamar ba banɗaki ba. Don sau dubu ya fi ɗakin da suke kwana a ƙauyen su. Jinjina kai ta yi tana ƙarasawa ciki. Ta fi minti nawa tana tunanin ta inda za ta fara, kafin zuwa can ta yi ƙarfin halin soma wankan a sanyaye. Ta ɗauki wajen minti 30 kafin ta soma ƙoƙarin fito wa, ta mugun jin daɗin jikinta. Har wani sassanyan murmushi ke tashi daga kyakkyawar fuskarta ta fito.
Chapter 18 · 0% Book details